NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 220 of 223

an idona ya sauka akan fuskar Yaya da ke kwance akan ƙirjina, hannayensa na kewaye dani. murmushi ya ɓalle min, na kai hannu na ƙara rufemu da bargon ina mai tusa hancina acikin sumar kansa da wani sanyayyan ƙamshi ke tashi. *AFTER 1 YEAR...MK* "Hellowww Daddyn Urnborn". nayi whispering softly acikin kunnensa. "It looks like someone will be late for work today". na ƙara faɗa ina ba shi kiss a kowanne eyes nasa, that made him open his eyes lazily yana kallona da murmushin da ke talewa a leɓensa. "Morning to you Baby Doll". ya faɗa yana janyoni jikinsa. "morning sarkin bacci". na faɗa ina kama tsinin hancinsa. "Doll wannan ɗumin jikinne bana gajiya da shi shi yasa kullum nake kusan yin late a work". sai na ƙara sakin wani murmushin na kwanta lamo ajikinsa ina jin yanda zuciyarsa ke bugawa. ya kai hannu kan ƙaton cikina yana faɗin,"1 week remaining ko?". na gyaɗa masa kai kawai ina tura hannuna cikin singlet nasa na shiga wasa da nimple ɗinsa. "i have to be at the office by now shi ne za ki tsokanoni ko". shiru nayi masa, dole ce take sawa nake barinsa fita office, amma ba dan son raina ba, ina son mijina, ina matuƙar sonsa, kuma ina godiya ga Allah da ya mallaka mani shi, haka ina godiya ga wannan ƙaddarar da ta sauya komai. duk sanda nake tare da shi, sai naji inama akwai wata hanya da zan sanya lokaci ya tsaya cak, so i could cherished our moment together forever, or if my life was a dream zan yi fatan naita baccin ba tare da na farka ba. ya bani kiss a saman kumatuna da forehead ena, duk da cikin jikina ya tokareshi amma haka ya san yanda yay ya haɗe hancinmu wuri guda yana gogawa, shaƙar numfashin juna kawai muke, kuma tuni na gama kashe masa jiki da shafa hannuna da nake a saman mararsa, sai ya ƙanƙameni yana lumshe idanu, sai na saki murmushin da ya haɗe da dariya ina janyewa daga jikinsa. sai yay saurin buɗe shanyayyun idanuwansa yana ƙara janyoni yace,"Allah ba ki isa ba". kuma ba tare da ɓata wani lokaci ba muka fara nunawa junanmu soyayya har zuwa lokacin da muka gama samun natsuwa sannan mu kai wanka...na shirya shi muka fita mu kai break fast tukunna ya wuce office ina cewa da shi,"Jay plss be at home in time for dinner". ko da na dawo ɗakin Nawwara na wuce, na sameta tana shafa icing a jikin cake ɗin munafurcin da ta gama haɗawa. yawuna ya tsinke na zauna kusa da ita, tsabar walaƙanci tana jina amma saboda abinda ta ke ya fini bata kula da ni ba. bata ankara ba kuwa na kaiwa cake ɗin damƙa nayi ƙatuwar gutsira na kai baki, tsananin baƙin ciki da takaici ya hanata cewa da ni komai sai sakin baki da tayi tana kallona, kaman ta kurma ihu ta rufeni da duka. haka na janyo cake ɗin gabana naci iya cina bata ce da ni ƙala ba, sai da nayi hani'an tukunna na dubeta ina dariya nace. "sorry ba laifina ba ne". "dama ai haka za ki ce". ta faɗa kaman tasa kuka. na shafe ma ta icing ɗin a fuska har lokacin ban bar dariya ba saboda yanda ta cukule. "dilla can Allah na tuba dan dai cake, me akai akayi shi...sai a tura driver ya sayo masa wani". tace,"ai nasan da na sayarwa naƙi saya na zauna nayi da kaina saboda bana so hubbina yake cin kayan waje". na taɓe baki nace,"oho dai, tun jiya nake cewa ki rakani kawai ai min operation a ciro waɗannan yaran kika ƙi, da yanzu ai cake ɗinki na nan lafiya". ta buɗi baki za tayi magana wayarta tayi ƙara da ringtone ɗin i love you my baby boy. tana ɗagawa sai cewa tayi da Abdurrahim "Habibi kaga Yaya ko?". ta faɗa masa da kukan shagwaɓa, ina jiyo shi ta cikin speakern wayan yana tambayanta me nayi mata, tace da shi. "na gama haɗa maka birthday cake ɗinka tazo ta cinye tana wani ƙalawa unborn". ina jinsa ya saki ƙwafa yana faɗin,"yanzu duk wahalan da kika shiga bata tausaya maki ba ta zauna ta cinye, ina ce ma ko sannu bata maki ba ko?". tace da shi,"ina tace min sannu kuwa tana can ɗaki liƙe da miji bata ma san nayi aikin ba, sai iya zuwa ta cinye". "rabu da ita, zan rama ne akan mijinta...kuma zan zo na ɗaukeki ai sai naga yanda zata yi da zaman wannan ƙaton gidan". na ƙyalƙyale da dariya na warci wayar ina cewa da shi,"ka ɗauketa ka kai ta ina ƙaton gwauro?". "ina ruwanki, ke da mijinki ya ɗaukoki daga gidanku ina ya kai ki, Allah kina shigar mana hanci da ƙundundune...sa'arki ɗaya ma ɗanmu ne yaci da sai dai kiji sammaci yanzun nan". "oho dai cake ne na cinye kuma ko yanzu akai wani naji ina so sai naci ehe...kuma wallah Abdurrahim kar na sake naji kaima Jay wani abun in ba haka ba sai na shiga na fita na lalata wannan auren naku". sai ya bushe da dariya yana cewa,"yasin munfi ƙarfinki, munsha li'ilafi da tabbatyada, dan haka munfi ƙarfin muguntar mutum". kashe wayar nayi na jefa mata kayarta ajiki, na dafata na miƙe ina roƙonta akan ta yiwa Allah ta zo muje asibiti ai min operation ai yanzu ya isa acire twins ɗin da ke cikina duk da Edd ɗina sai nan da 7days, danni nace ban haihuwa da kaina sai dai a yankani. dan walaƙancin Nawwara sai ce min tayi bata ƙi ganin ma na fara naƙuda yanzu ba ta
🏠