i ƙwaƙwalwata ga fara tunanin laifin dana aikata naji wani ƙullutun abu ya faɗo ta gabana, na daɗa rumtse ido sosai saboda zafi da ya ratsani.
Da gudu-gudu kuma naji abu kamar ruwa naci gaba da fita daga gabana me ɗumi, na mayar da kaina kwance idanuwana a rufe ina cije leɓe, tsawon wasu daƙiƙu dana ɗauka ƙasan cikina na min azabar ciwo sannan na fara dawowa cikin hayyacina dana bari, numfashin wahala nake saukewa da sauri da sauri, daga can na jiwo muryar Gwaggo na fita acikin faɗa.
"rashin hankali ne kawai irin nata, Amarya zuwa yanzu ya kamata ki daina goyon bayan Mairo akan duk wasu abubuwa da take wanda ba dai-dai ba, haba wacce iriyar rayuwa ce wannan da za'ace mutum zai yi ba dai-dai ba a zuba masa ido baza'a nuna masa kuskurensa ba, ni wallahi kuna ɓata min rai idan kuna cewa yarinya ce".
Inna Amarya ta fitar da murmushi me sauti sannan tace,"to ai sai yanzu girman ya risketa ko, daga yanzu ne ita ma zata fara sanin kanta da kuma inda ke mata ciwo, wanda da kanta zata gane kuskuren abunda bai dace ba". Shiru na tsawon daƙiƙa biyu Gwaggo bata ce komai ba, sai can naji ta ambaci sunan Kulu tare da cewa mata, "ki duba magungunan muji yanda suke kamin ta farka, allurar kuma za ki yi mata ne ko ya?". Abunda na sani Kulu bata magana dan haka ko a yanzu da idanuwana ke rufe banji fitar muryarta ba da amsar maganar Gwaggo, haka kuma maganar da Gwaggo tayi bana da tabbacin da ita tayi, dan magana ce da aka alaƙanta ta da masu hankali bata mahaukata irinsu Kulu ba, to amma sai dai kuma me? a ɗazu dana farka bayan Gwaggo da Inna da Kulu babu wani bayan ni, ko kuma wani ya shigo bayan rufuwar idanuwana ne?, lokaci ɗaya nasa shakku akan maganar Gwaggo, duk ta yanda naso nayi wani tunani akan lamarin sai na kasa, saboda yanda kaina ke sarawa.
Har yanzu zuciyata na cikin fargabar laifin da nayi wanda ban sani ba, da kuma taraddadin hukuncin da zan karɓa daga wurin Gwaggona, saboda haka ne na kasa buɗe idona nayi kamar ina bacci, duk maganganun da suke yi inaji, har lokacin kuma da naji ana batun yi min allura, ai lokaci ɗaya tashin hankalin da nake ciki ya ninku, na ƙara rumtse ido gam ina jin kamar kar na buɗesu, alokacin da naji an ɗaure min hannu da igiyar roba na ƙwallara wata ƙara na miƙe zaune babu shiri ina neman hanyar guduwa, Gwaggo ta buga min wata uwar tsawa da ta saisaita hankalina, hawayen da ke maƙale cikin idona suka shiga zuba kafin na ɓare baki na fashe da kuka. Duk da idona rufe suke amma yanda naji an jawoni zuwa ƙirji an rungumeni ya bani tabbacin Inna Amarya ce, bayana ta-ke shafawa tana min magana cikin sigar lallashi, daga can inda Gwaggo kuma ke zaune naji ta kuma ɗaga murya acikin faɗa tana cewa,"wai ba za ki yi ki mata bane kin wani yi tsaye kanta kina kallonta, ke ni nafa gama ganeki, babu wani abu da kike so a yanzu fa-ce baƙin cikin da ke daskare a zuciyata ya ƙarasani, idan kuma na ƙarasa wallahi kece sila, hakkina kuma ba zai barki ba". Ban san dawa Gwaggona ke wannan masifar ba, dan a ƙanƙame nake da Innata, ta kauda kaina ɗaya gefen ta yanda ba zan kalla allurar da za'a min ba, sai dai naji tausayin koma wanene Gwaggo kema wannan masifar cikin hargowa da ƙaraji.
Ban aune ba naji shigar tsinin allura a hannuna, na kurma uban ihun da saida Innata tasa hannu ta rufe min baki, kuka nake wiwi ina kiran sunan Baba da Ya Kabiru da Ya Amadu, acan ƙasan maƙoshina kuma ina jera Allah ya isa ga wanda yay min allurar, a hankali nake sauke ajiyar zuciya Innata na aikin ban haƙuri da lallashi, har sanda bacci ya ɗaukeni ba tare dana sani ba.
Dawowar Malam daga wurin aiki ya wuce ɗakinsa, inda Inna Zulai wadda girki ke hannunta ta tarbeshi da kyakykyawan abincin da ta dafa na dambun acca kasaancewar Malam ma'abocinsa ne, zaune suke su na taɓa hira shi da ita, tana sanar masa da zancen maganar auren saurayin Sadiya da yake so a bashi izinin turowa.
Gwaggo ta shigo bakinta ɗauke da sallama, cikin ladabi ta duƙa tana miƙawa Malam baƙar leda me ɗauke da takardu aciki. "gashi ɗazu Liman ya aiko Muntari ya kawo yace a baka". Malam ya buɗe ledar, takardu ne guda uku kowanne da rubutu ajiki, ya dudduba ba dan ya san meke rubuce aciki ba.
Ya mayar cikin ledar ya ɗaure sannan yace,"to Madallah bari na ajiye idan yaran nan sun dawo sa duba muji mene ƙunshe a ciki".
"yayi kyau". Gwaggo ta faɗa tana yunƙurawa zata miƙe ta fita Malam ya maida ita.
Yay ɗan jim yana daɗa nazari akan maganar da Zulai tazo masa da ita, kamin yay gyaran murya ya fara magana da dukansu.
"to ke Zulai a maganar da kika zo min da ita nayi duba wanda magana ce mai kyau, sai dai ina so ya ƙara bamu ɗan lokaci...sannan a yanda nafi so na kuma gama tsarina tuni, so nake na haɗa yaran nan duk su uku na miƙasu ɗakinsu a lokaci ɗaya, duk da nasan da cewar hakan hidima ce babba amma babu komai Allah zai yassare yanda za'ai".
Sai a yanzu ya ɗago kai ya dubi Gwaggo wadda ke fuskantarsa tana sauraronsa yace,"Suwaiba ita Mairo bata taɓa zuwa miki da zancen kowa bane?