NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 218 of 223

na shekara dubu bana tare da ke". mun ɗau tsawon lokaci muna waya da ita kafin muyi sallama. daga nan kuma na kira Ummi, ita kuma ta maida ni kaman wata ƙawarta sai tsiya ta ke min, har nake ce mata aini na daina kulata, tace ai dama tuni tasan da cewan na daina yinta, itama mun daɗe muna waya daga ƙarshe take ce min,"Maryam nasha gaya miki Kabir na matuƙar sonki, dan haka yau sai kinyi haƙuri da yanda zai zo miki, ta salon da za ki sameshi...kiyi dauriya da juriya, dan wannan ruɓaɓɓan son da ya ɗauki tsawon shekaru masu yawa yana yi miki yau zai nuna miki shi, kema ki zage ki zama mace ta gari Maryam, a wannn daren ki faranta masa rai, dan Allah a daren yau ba sai an kai da nisa ba ina so ki ɗauko min jika, tunda ni dai ba zan yarda ƴata na haihuwa nima ina haihuwa ba, zan dai ta rainon jikokina...yauwa sannan idan kin shirya wannan humrar da na bashi ya kawo miki, ki tabbata kin shafe duk ilahirin jikinki da ita, dan so nake kiyi zarra a zuciyar Kabiruna, ya zamana babu mace mai iya kamoki a zuciyarsa da idanuwansa". Maganartata ta saka naji kunya, mu kai sallama da ita cike da kewarta ina daɗa jin ƙaunarta acikin raina. na kira Alhassan ma muka sha hira da shi, yana ce min wai idan zai zo nayi masa girki sama da kala goma dan so yake ya tabbatar da ingancin girkina, nayi dariya nace da shi aikuwa sai dai kar yaci. Shamsiyya Sani ma mu kai waya da ita, tana ta tsokanata da wannan iskancin nata, ƙarshe dai ba dan mun gama hiran ba na kashe wayan, dan idan na biye mata sai ta lalata min kunnena. na kira Yagana na sanar mata mun sauka, sai da za muyi sallama nake tsokanarta yace ko ta fara lissafin, tayi dariya sosai tana ce min shaƙiya tare da cewar za tayi kewarmu. bayan sallar isha'i nayi shirina cikin wasu riga da skirt na english wears da Yaya ya lodasu akwatu huɗu, kaman me shirin buɗe kanti. kayan sun min kyau sosai dan har sai da na bawa Nawwara tayi min hotuna, na duƙa ina rufe drowern da na maida humra sai jin mutum nayi ya kwantar da kansa a bayana ya kuma zuro hannayensa saman cikina, cikin wata iriyar muryar da ban taɓa jinsa da ita ba yace,"i love you Maryam". sai naji ƙafafuna sun shiga ruwa, na ɗago ina juyowa gare shi tare da dafa kafaɗunsa gudun karna faɗi, sai ya rungumeni tsam irin rungumar da ta banbanta da sauran da yake min, dan har ƙashin bayana sai da yay ƙara. a hankali naji yana shinshinar wuyana kafin muryarsa ta fito can ƙasa yayin da yake murza hannuna cikin nasa,"Maryam wannan ƙamshin fa?...wane irin turare ne kika saka haka?, wayyooo Maryam kinji yanda yake motsa min jikina kuwa". kaɗan ya rage yawun da ke zarcewa zuwa maƙogorona ya haɗo tare da zuciyata su fito, na motsa jikina ina so na zame daga jikinsa sai ya kuma ƙanƙameni, fuskarsa kwance kan kafaɗata yay shiru kaman wanda yay bacci, sai numfashinsa da ke fita a hankali a hankali...shirun da naji yay yawa yasa nace,"Yaya". har ga Allah a irin yanda yay shirun nan da yanayin yanda yake sauke nunfashi zaka rantse kace ko bacci yake, amma da mamakina sai naji ya amsa da,"ummm". sai nayi shiru ban ƙara cewa komai, kafin na ƙara jinsa ya kira sunana."Maryam". a hankali na amsa da,"na'am". "ina sonki, ina sonki da yawa, dan Allah kinji...". kamar wani ƙaramin yaro me neman wani abu a yanda yay roƙon, naga kaman yana neman faɗuwa sai na ruƙo shi ina tambayansa,"dan Allah me?". bai ce komai ba har tsawon sakanni uku, kafin nan ya ɗago da kansa ya haɗani da jikin bango, sannan ya duƙo da kansa saitin bakina a ƙoƙarinsa na ya haɗe bakinmu wuri ɗaya, haɗuwar leɓensa da nawa yay daidai da bugawar wayarsa, sai kawai yaja wani dogon tsaki na ƙorafi ya saki ƙuguna da yake riƙe da shi sannan ya ɗaga wayan yana magana murya a ɗage. "Abdurrahim kana da matsala". ban san me Abdurrahim ɗin yace da shi ba naji ya ƙara jan dogon tsaki kamin yace,"su jirani ina zuwa". ya kashe wayan yana zurawa a aljihu, ya tsareni da idanuwansa da suka fara ƙanƙacewa tare da ce min kiyi alwala ki jirani yanzu zan dawo, just some minutes kinji. gyaɗa masa kai kawai nayi, kuma sai da na ɗauki tsawon wasu sakanni tsaye a wurin kamin na iya jan ƙafafuna cikin mutuwar jiki na shiga toilet nayi alwala na dawo bakin gado ina zaman jiran dawowarsa. inata jera hamma ya dawo ɗakin yana aje leda a bakin drower, tukunna ya shiga yayo alwala ya dawo yace na tashi muyi sallah, munyi sallah raka'a biyu kaman yanda sunnah ta koyar, sai kuma naji ya shiga koro adu'oi wanda zan iya cewa adu'ace da ke cikin kansa gaba ɗaya yake yinta, yayinda ni kuma nake binsa da amin har lokacin da shima yace amin muka shafa tare. ya juyo ya fuskanceni ya dafa kaina yay min adu'ar da sunnah ta koyar sannan ya matso kusa da ni, yasa duka hannayensa ya tallafo gefen fuskata yace. "doll". da wannan muryar tasa mai zurfi ya kirani da sunan da shi yasani saurin ɗago ido na dube shi, ƙwayar idonmu ta sarƙe wuri guda. "kina jin yunwa?". na girgiza kaina acikin tafukan hannunsa alamar a'a, bai janye hannunsa ba ya ƙara cewa. "amma
🏠