NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 217 of 223

ro kike ko Maryam, ni dai dan girman Allah ki kula da marayan nan, ba shi da uwa dan haka na roƙeki ki zama uwa a gare shi, tun yana ƙarami ya rasa mahaifiyarsa dan haka dan Allah ki zame masa farinciki uwa ga ɗanta...tun bayan mutuwar mahaifiyarsa ni na zame masa uwa, ban taɓa bari yayi wani nisa da ni ba sai da karatunsa ya riske shi, yanzu gashi yayi aure kuma ba lallai wannan tafiyar me nisan zamani da zai yi ba mu ƙara samun damar ganawa ido da ido". sai kawai naji wani mugu mugun tausayinsa ya kamani, na kalle shi ta gefen ido naga yana goge ƙwallar idonsa. sannan na kalla Yagana da itama ke goge hawaye, sai naji nima hawayen na sakko min, muryana a hankali nace da ita. "insha'Allahu Yagana". sai tayi murmushi tana ƙara damƙe hannunwanmu anata tana cewa,"kin min alƙawari?". na ɗaga mata kai da cewan,"ehh Yagana nayi miki, haƙiƙa babu abin da za ki nema daga gareni na kasa yi miki shi, dan kinyi min komai a rayuwata... kuma insha'Allahu duk tsayin lokacin da zamu ɗauka acan zamu dawo mu sameki da rai da lafiyarki, da yardar Allah sai kin ɗauki ɗan jikanki da hannunki". a tare suka kalle ni, tana shafo fuskata da cewan,"Allah ya amsa min Mairo...au ashe fa Baba Kabiru ya hanani faɗin wannan sunan". sai na ɗan cukule fuska da muka haɗa ido da shi nace mata."to amma Yagana shima kiyi masa faɗa kar yake min ƙiriniyansa, dan ba ya jin maganata". nayi maganar a kumbure. tace da shi,"Baba Kabiru kaji dai...ka rage ƙiriniyanka tunda Mama Mairo tace bata so, in ba haka ba kuma duk hukuncin da tayi maka babu ruwana ko ƙara kar ka kawo min". yana murmushi yace,"za'ai yanda kika ce Hajiya Yagana". ta gyaɗa kai sau biyu sannan tace,"Maryam amanar Allah ce tsakaninmu Kabir, na ba ka amanarta, dan darajan Allah ka kula da ita, Kabiru idan ka cutar da ita kai da Allah". "insha'Allahu Yagana ba zan ba ki kunya ba". ta saki hannunmu tana miƙewa da cewar,"bari naga Iya ko ta gama dakan waccen daddawar da kace a haɗa maku da ita...sai daren jiya Zannira ta aiko da ita". ta ƙarasa ficewa a sanda ta ke ƙara cewa,"ita Nawwaran ta gama shiryawa to?". shi kuma yana bata amsa da ehh. ya jinginar da gefen fuskarsa atawa yana cewa da ni,"Ya ya dai?". ban ce masa komai ba sai ɗan murguɗa baki da nayi. sannan ya miƙar da ni tsaye, ya ɗauko vail ɗin abayata ya min rolling, sannan ya kama hannuna muka fice daga ɗakin, ina ta cewa ya cikani amma yaƙi har sanda muka ƙarasa bakin mota, kunya duk ta dabaibayeni ganin Baba a tsaye a wurin, amma shi ko a jikinsa, ganin Ya Ahmad ma yasa sai ƙara wani janyoni jikinsa yake yi. munsha adu'a daga ƴan gidanmu, har sai da suka sakani kuka sosai, musamman Inna Zulai da duk ta kashe min jiki a da ta ke ƙara roƙata yafiyar abunda tayi min. babu kowa a gidan sai Ya Ahmad, kuma shi ya kaimu airpot, muna tafe su na hirarsu da Ya Kabir ni dai da Nawwara munyi tsit. sai da muka hau jirgi tukunna shima ya bar airpot ɗin, da zamu hau jirgi kuwa raina ya washe da dariyar Nawwara dana ci, wadda ta kasa hawa jirgin sai da Yaya ya riƙeta tukunna. kuma tunda muka hau jirgin haka kawai sai nake jin wani mixed feeling da duk ya ɗauke wani ɓacin rai nawa, naji na wanzu a wani sabon yanayi da jin daɗi, dan haka kawai naji zuciyata na washewa, Ya Kabir na min hira wadda duk akan company ɗin da yake son buɗewa ne, wata maganar na tsoma baki wata kuma nabi zanen ginin company ɗin da kallo ba tare da nace komai ba...tashinmu da awa biyu naji idona ya fara rufewa, dan jiya ban wani samu nai bacci sosai ba saboda miskilanci, na zura hannuna ana Yaya na kwantar da kaina a kafaɗarsa daga nan kuma bacci ya ɗaukeni, ban farka ba sai buɗe ido nayi na ganni akan gado, wai ashe time ɗin da muka sauka ba ya so ya tasheni sai kawai ya ɗaukoni a hannu. time ɗin da na tashi baya gidan, sai Nawwara ce ke faɗa min wai sun fita shi da wani abokinsa, ina ji kuma nasan Abdurrahim ne...da yamma muna zaune ni da Nawwara a living room muna kallo muka ji ƙaran bell, Nawwara ta tashi taje ta karɓi abincin da Yaya yay taking mana order...kallo nake amma gaba ɗaya hankalina na kan Mamina, tun jiya rabona da jin muryarta, gashi wayana na hannun Ummi ina ga mantawa tayi bata bani ba. na shiga bedroom ɗin da yake mallakinsa ne wanda na tashi a bacci ɗazu. akan dressing mirrow na kalla ƙaraman wayansa a ijje, nasan kuma ba ya aje dan ya manta bane sai dan saboda yasan zan buƙata. fuskata ta washe da murmushin jin daɗi a lokaci ɗaya, na ɗauko wayan na zauna bakin gado tare da danna kiran wayan Mamina. "Autana". na amsa a sanda ta kira sunan nawa, ina jin kaman na shiga ta cikin wayan na rungumeta. "ya akai? kun sauka?". kaman ina gabanta na ɗaga kaina alaman ehh tare da cewan,"ehh Mamina tun ɗazu ma". "to masha'Allahu...babu dai wata matsala ko?". "ehh Mami babu...sai dai Mamina ina kewanki". tai murmushi mai sautin da ya motsa min zuciya sannan tace,"tun yanzu Autana, jiya ne fa kawai". na turo baki a shagwaɓe ina cewa,"Mami kawai fa kike cewa, to Allah Mami jina nake kaman
🏠