NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 216 of 223

ncin, bata wani ci da yawa ba tace da shi ta ƙoshi. sannan ya ƙara cewa da ita,"ɓalli wannan maganin kisha". ta kalli inda wani ƙaramin box yake ta ɗauki maganin da ya mata nuni da shi ta ɓalla tasha, ya taso yace ta miƙe yay mata allura, lokaci guda ta shiga matse hawayen da ke shirin sakko mata, tana cewa da shi. "Ya Kabir na warke wallah". bai bi ta kanta ba ya janyota jikinsa ya tsira ma ta allurar a sanda ta ke ruƙunƙume shi tana sakin ɗan ƙaramin kuka. sanin cewar ba iya lailayawa zatayi ba ya lailaya mata sosai kan muryarsa ta fito a sanyaye yana cewa. "kin gama haɗa kayan naki?". ta ɗaga masa kai alamar ehhh. ya sauke numfashi sannan yace,"ɗazu naje wurin Baba". sai tayi saurin zamewa daga jikinsa tana ɗago kai da ido ta kalle shi. shima ya kalli ƙwayar idonta da ta ciko da hawaye tukunna yace,"ba na son kuka". ya faɗa yana saka hannu ya goge ma ta su da suka sami damar sakkowa. "munyi magamar Kabirun da kika ce an ba ki, yace sun neme shi tunda jimawa kuma an tabbatar musu da ya rasu, basu faɗa miki ba ne kawai...ashe almajirin Ummanki ne da yay musu halacci, kuma shi ya nuna yana biɗar aurenki tun kina tsumma...na faɗawa Baba cewar zan tafi da ke can ƙasar da nake zaune za ki ci gaba da karatunki acan...na basu haƙuri na ƙurewar lokaci da aka samu wurin sanar da su, amma nayi musu alƙawarin ko shekara ba za kiyi ba zan kawo ki kona sa akawoki ki gaida su...hakan yayi miki?". ta ɗaga kai tana cewa,"na gode da kulawanka gareni". sai taji yasa yatsunsa ya ɗago haɓarta yana cewa. "idan waɗan nan ƙafafun ba su daina rawa ba idan suka ganni next time ɓallasu zanyi, kin san dai ba zasu yi wuyar ɓallewa ba yanda suke kamar sillan karan nan". bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. "kin dai gama shirya komai ko?". "ehh na gama". "kar ki haɗa da tsaffin kayanki, na saya maki wasu su na wurin tailor sai zamu wuce zamu tsaya a karɓa". "tom na gode, Allah ya ƙara arziƙi". "amin amin..kije ki kwanta Allah ya ƙara sauƙi...amma ki tabbata ban fito ina cewa Nawwara fito ba, ko kuma ki fito kina ce min kinyi mantuwa". "insha'Allahu". daga haka tayi masa sallama ta fita yana bin bayan da kallo, zuciyarsa na lissafa masa wani abu da yake ganin da wuya ya yiwu...amma yana roƙon Allah yasa hakan ta kasance. *Plsss Comment and vote*. *SIRRIN ƁOYE* *_Abbas Haruna, Muhammad Kareem, Hussain ATK, Sdeen, Mukhtar, Muhammad Kamji, Surajo Salman, Hassan Basiru, Abubakar Saraki, Mariam Jumare, Amina Musa Galadima, Kherdeejer, Amina Kabir Caps, Maryam kd, Mum Syyid and Noor, Ummu Ashfat, Hajara Usman Aboki, Ummee Imam .Ina maku fatan nasara a rayuwaku tare da adu'an alkhairin Allah da kariyarsa su isa gareku a duk inda kuke._* *(53)* 6:00am. akan dining muke, ina fuskantar Ya Kabir shima yana fuskantata, sai Nawwara da ke daga ɗayan kujeran ta gefensa. na cika nayi fam da abunda ban san menene ba, wannan ƙullutun abun da ya tsaya min a wuya na rasa na menene, dan ta ƙarfi da yaji nake kora shi da abincin da nake ci amma yaƙi wucewa. "wai ke ba ki gama ci ba ne?". bakina ya furta maganar da ban shirya mata ba ga Nawwaran da idona ke kanta tun ɗazu ina banka mata wata uwar harara, ban san dalilin da ya sa nake jin mugun haushinta ba haka kawai babu gaira babu dalili, kuma jin haushin daga jiya ne zuwa yau amma lokacin da nake gidan kaman Basma na ɗauketa. sai naga ta tsorata da maganar da nayi mata har cokalin hannunta yana neman ya faɗi. "dilla Malama da ke fa nake kina wani muzurai kaman baƙar munafuka". na ƙara yin maganar a tsawace, sai kawai Ya Kabir ya tsaya yana kallona kafin ya maida kallonsa gareta. sannan saboda wani rainin wayo nasa da ya kusa sawa na kaiwa bakinsa duka yake tambayana wai dawa nake. naja dogon tsaki na miƙe ina tura kujera baya zan wuce ɗaki ya riƙo hannuna. "wai ke meke damunki ne...na faɗa miki fa ba zamu tafi haka ba ki ci abinci ba...kin san tafiyan awa nawa zamuyi? ko bana ce miki mun fasa zuwa abujan ba ne direct Ethiopia zamu wuce". na warce hannuna a nasa ina binsa da harara kafin nace,"idan damuwa kayi da cina ka biyoni da abincin ɗaki...amma ba zan zauna da mijina muna cin abinci tare da ƴar aiki ba, for what reason?...kuma ma indai da gaske da ita zamu tafi sai dai ku tafi tare amma ba zan bika ba, ai na faɗa maka bana son ƴar aiki". "to dama waya ce miki aiki zata je miki? ita ma nata personal zaman ne zai kaita". ban tanka masa ba nayi wucewata ɗakin Yagana ina sakin kuka mara dalili, kawai dai nasan idan nayi zan huce takaicin wani abu da ke ƙasan raina. bayan kusan minti ashirin sai gashi ya shigo ɗakin Yagana, ya zauna bakin gadon kusa da ni, na juyar da kaina daga kusa da shi na koma fuskantar Yagana da ke juye min wani rubutu a jarka da Baba ya bayar ɗazu da asuba. "to gashi nan Babanku yace kar ta yi wasa da sha...har kaima zaku ke sha tare kaji ko". ya amsata da cewan,"tom Yagana an gode Allah bada lada". bayan ta kamalla komai ta taso ta kamo hannunsa da nawa ta haɗe wuri guda tana cewa da ni,"Mai
🏠