san da me zance masa ba.
"wancan card ɗin fa?". tambayar Ya Kabir ta katse min gajeran tunanin da nake, ƙirjina ya fara yin fat-fat, ban san me aka rubuta ajikin card ɗin ba, dan tunda na ɗauko aje shi kawai nayi da zummar idan zan kwanta zan karanta, abu ɗaya kawai da nake tunani nasan ba zai wuce marriage wish ba. ban san me zance masa dan haka nayi tsilli tsilli da idanuwa bakina a gimtse. hannunsa na zagayowa kan cikina ya ƙara tambayata, da irin sautin da ayanzu na gagara yin shiru na amsa masa da. "Card ne". "ehh ai nasan card ɗin ne...na mene shi ne abunda na ke tambaya". na haɗiye wani guntun yawu sannan nace. "nima ban sa ni ba". na amsa mishi a ɗarɗarce saboda yanda yake tambayar cike da tuhuma, cikin kausashshiyar muryarsa yace,"tashi ki ɗauko min". nayi ƙumm na kasa tashi, a tsawace ya ƙara cewa,"nace ki tashi ki ɗauko min ko". muryana a ƙasa nace,"to ai ka matse ƙafan nawa". sai a yanzu ma ya tuna da cewar ƙafafuna na tsakanin cinyarsa ne da ya maƙalesu, ya ware ƙafar na miƙe kamar munafuka naje na ɗauko, abunda ya ban mamaki ina miƙa masa kallo ɗaya yaywa card ɗin sannan ya ɗago ya dubeni fuska babu annuri yace,"me ya kawo Ahmad wurinki?". sai nayi kaman ban gane me yake nufi ba. "wai ba za ki bar min shiru ba idan ina tambayarki". "to ai kai ne da wata negative tambaya, me zai kawo Ya Ahmad ɗakin nan bayan yasan ni matar wani ce". a harzuƙe cikin tsananin ɓacin rai yace,"zan ɗaukeki da mari wallah, ni za ki rainawa hankali...ƙamshin turarensa da naji shigowata naki ne? ko kuma wannan hand writing ɗin naki ne?...kin faɗa uban me ya kawo shi wurinki ko sai na miƙe kinga ainihin tsayina tukunna". jikina na shaking nace,"wallah ni ban san me yazo yi ba, kawai ya shigo ya aje min wannan ya fita amma Allah ka yarda da ni ko kallonsa ban ba". ya galla min wani banzan kallo kamin yasa hannu ya keta card ɗin, sai da yayi gutsi gutsi da shi tukunna yay watsi da su gefe sai wani irin huci yake. sannan ya miƙe tsaye ya tsaya a tsakiyar kaina yana cewa,"daga yau ko wuta Ahmad ya aje kikai gigin ɗauketa gudun karta ƙona ki Maryam abin da zan miki sai kin ƙwammaci mutuwa ki kai...stupid kawai". yay maganar kamar zai rufeni da duka sannan ya bar ɗakin fuuuu kawa guguwa. ya fita ina jiyo Yagana na cewa da shi,"Ta faru ta ƙare, da gasken dai lissafin daga ɗakina zai soma...ai shikenan Kabiru kanka ka yiwa". abinda yasa ta faɗa masa haka ganin yana gyara zaman belt ɗin da ke jikinsa ne, dan da kamar zai cire belt ɗin ne ya dukeni sai kuma yay saurin ficewa.
na miƙe ƙafafuna a sanyaye na shiga toilet ɗin Yagana na wanko fuskata na dawo na kwanta ko cire kayan jikina banyi ba, bacci yay ƙaura daga idona tunda na kwanta, tunaninsa da tunanin abunda yay min kawai na ke, sai ƙwafa nake saki a raina. haka har Yagana ta shigo ɗakin, ina jinta sanda ta kunna fitila ta kashe tana faɗin,"ni Rakiya Allah yasa bai jiwa ƴar mutane ciwo ba...dan yanda naga ya fito fuskar nan kamar hadarin da ya haɗe a gabas nasan bata daɗin rai akai ba, ni dai Kabiru bai kyautan ba, dan da ya san amana na karɓa ba zai aikata hakan ba". ta hayo gadon tana taɓa jikina, cikin fushi na bige hannun nata. ta hau surutanta har taga ji kuma ta dawo tana yabona da yabon Ya Kabir, har da kukanta na zata rabu da shi gobe, wai tasan yanda yay auren nan in ya tafi sai ranar da ta ganshi...ina kallonta tana haɗa wasu kayansa da ta ke faɗin ta wanke masa tasa an goge, tana haɗawa kuma tana goge hawaye, duk sai naji ta bani tausayi, na sauko na ɗora kaina saman cinyarta, nan ta shiga yi min kalar nata nasihar da faɗan duk akan zamantakewar aure.
****ɓangaren Kabir kuwa yana fita direct ya zagaya ta ƙofar baya, inda ɗakinsu Nawwara yake, dama ƙofa biyu ce, ko ka shiga ta kitchen ɗin Yagana ko kabi ta baya wajen flowers ɗin gidan. da farko da ya shiga ɗakin bai lura da kowa ba dan ko sallama bai yi ba bare a amsa yasan da wani a ɗakin, sai Iya ce da ta kula da shi ta yunƙura ta miƙe daga kwancen da ta ke tana gaishe shi. ya shafi bayan wuyansa ya amsa sannan ya tambayeta ina Nawwara. tace da shi ta shiga wanka ne da yake yau ta wuni da zazzaɓi sai yanzu taji daɗin jikinta. sai ya juya ya fice bayan yace da ita,"iya idan ta fito kice ta sameni a ɗakina". ta amsa mishi da "to" tana ƙara yi masa Allah sanya alkhairi dan jiya gaba ɗaya ma bata ganshi a gidan ba.
bai yi minti goma sha biyar da shiga ɗakinsa ba yaji knocking ƙofa. ya ƙarasa saka button na rigarsa sannan ya bata izinin shigowa ɗakin. ta sanyo siraran ƙafafunta ciki bakinta ɗauke da sallama kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta. "Ya Kabir gani". ba tare da ya dubeta ba yace,"na ganki, idan kin gaji da tsayuwar kya iya hawa kaina ki tsaya". daga yanda yay maganar tasan ransa babu daɗi, dan da sauri ta ɗago ta dube shi, kamin nan ta durƙushe a wurin tana fuskantarsa. "ɗauki wannan abincin ki cinye". ta buɗi baki zata yi magana ya dakatar da ita da cewa,"bana son musu". saboda haka ba dan taso ba ta shiga cin abi