gama ka bani takardata na tafi gidanmu yanzu, dan naga da gaske ne kai ɗin aka aura min kuma ni ba zan zauna da wanda baya so na ba". sai ya sa ki wani killer smiling mai ƙarfin sauti da cewan. "ahh tunda ma dai ke kina sona ai da sauƙi, a hankali kya koya min son naki". da sauri nace,"ni nace maka ina sonka, Allah sauƙa na so wanda ba ya so na, yake ƙaurace min saboda ƙaddarar da ta samar da ni". yay shiru bai ce min komai ba, sai na ɗago ido ina dubansa da yanda ya tsareni da ido, na tsuke baki na murguɗa shi gefe sannan nace masa. "ko baka ji ba, nace bana sonka, idan kaji haushi ka ɗauka mataki". ai rufe bakina ke da wuya sai jin hannunsa nayi saman bakina ya matse da ƙarfi, kafn nan yasa haƙori ya gantsara min cizo a leɓe, na kuwa daddage na kurma uban ihu, ihun da ya ja Yagana zambaɗa salatin da bata shirya ba.
a lokacin kaman na fita parlon na sameta na bibbigeta dan takaici, salati ta ke zabgawa tana faɗin wai. "shikenan Abunda nake gudu ya faru...yanzu Kabiru haƙurin da nace maka shi ne ka gaza yinsa, yanzu shikenan akan gadon nawa...ni Rakiya Manniru naga ta kaina, haihuwar ƴaƴa da jikoki iya shegen da ba'a taɓa min ba sai akanku". ihun da na kuma saki ya ƙara sakata zabga salati tana cewa,"Kabiru kana jina ina salati da salallami shi ne ba zaka barta haka ba, dole dai sai an fara lissafin kwanakin ciki daga ɗakina...Kabiru nace ka ƙyaleta haka kuzo ku wuce Habujan a yanzu ku ƙarasa acan, ko kuma ga ɗakinka can ku ƙarata amma ni wannan ihu ƙara yinsa ba a ɗakina ba".
[7/18, 16:14] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*(52)*
Yagana na tsaye na sababi Zulai ta faɗo parlon da sauri, tambayarta ta ke lapia amma ko sauraronta bata yi ba, salati kawai ta ke zabgawa tana kambaba zancen da ba shikenan ba. Zulai ta juya ga su Basma da ke zaune kan kujera hankulansu na kan tv su na kallo, ta kira sunan Sadiya, ta juyo a sanda ta ke kai mango baki tana sha. "wannan ai shashashanci ne Sadiya, kuna jin Yagana na salati ba ku tashi kuga meke faruwa da ita ba". kamar Sadiya ba zata ce komai ba can ta nisa sannan tace. "Inna ki yiwa Allah ki ƙyale wannan rikitacciyar tsohuwar". lokacin Yagana ta juyo tace da Sadiyan. "wannan kuma da wadda ke tsaye kusa da ni kike ba ni ba". Sadiya ta ƙara kaiwa wuya amma bata ce mata komai ba. Zulai ta maida hankalinta ga Yagana da ke faɗin,"ki kalle min nan fa Uwar Amadu, wai yaron nan Kabiru daga yi masa halacci nace ya shiga su ci abinci da matarsa shikenan sai ya tafi aikata abunda ba haka mu kai da shi ba". Zulai tace,"me ya faru Yagana?". Yagana tayi guntun tsaki sannan tace,"kema Zulai wataran dai akwai ki da duhun kai...matsa ki ban wuri nan kiga na shiga na fito da shi". sai a yanzu Zulai ta fuskaci inda maganar Yagana ta dosa, dan haka ta dakatar da ita daga shiga ɗakin tana cewa,"yi haƙuri Yagana". "nayi haƙuri kamar ya Uwar Amadu...ba ki lura da ta'asa ake aikawa ba akan gadona ba ne". "bai zama lallai hakan ba Yagana". "ke kinji uban ihun da yarinyar nan ta kurma kuwa da kike faɗar wai ba farketa yay ba...ta ina za ki sa ni, haka fa yaron can Lamiɗo yay mana da bikinsa, daga shiga ɗaki a barsa ya keɓe da matarsa sai fito mana yay kayan jikinsa duk sun ɓaci da dilkar da ake shafa mata, to yanzu tsakani da Allah ki faɗa min a wanne irin yanayi Kabiru zai fito, kai kai ni Rakiya Manniru ina ganin abinda ya isheni bai ishi Allah na ba....akan gadona, kan gadona fa akai kwanciyar aure, wannan ɗiban alhaki da me yay kama". tayi zancen tana neman kujera ta zauna haɗe da rafka tagumi. Sadiya taja dogon tsaki tace,"wallah Yagana kayan haushinki da yawa yake...ta ya mutumin da baifi minti biyar da shiga ɗaki ba za ki ce ya farke matarsa?, sai kace wanda zai yi fyaɗe ko kuma wanda aka aura masa wacce ba ya so...dan Allah ki rage zuzuta abu". Yagana dai bata ce ma ta kanzil ba tayi kunnen uwar shegu da ita.
ni kuwa tunda Ya Kabir ya sakar min baki daga matsar da yay masa nake aikin matsar hawaye, naja hancina da ya cika da majina ina ƙara kumbura da irin tunanin sharrin da zan ƙala masa wurin Daddy a raba wannan auren. yasa hannu ya gyarani akan cinyarsa da nake a zaune, zaman da yay min ta dole dan kawai zai yi forcing ɗina naci abinci. ya kawo spoon bakina wanda ya ɗebo eba da ya sha miyan egusi busashshen kifi. "oya haa". na kasa yi masa garda saboda yanda naga ya ɓata rai, irin ɓacin ran da tun tasowarmu tare ban taɓa gani a fuskarsa ba, haka ya dinƙa feeding nawa har sai da ya tabbatar da cikina ya cika kafin ya ƙyaleni.
kuma abunda nake ta tsoro tun shigowarsa shi ya faru, idonsa ya ƙyalla kan wedding card gift ɗin da ke aje gefen pillow ɗin da na ɓoye. a ɗazu da ina sallar isha'i Ya Ahmad ya shigo, lokacin tayarwata kenan dan haka bai iya zaman jiran na idar ba ya sunkuya har ƙasa ya aje min card ɗin sannan ya juya ya fita, ya fita ya barni da bugun zuciyar da har yanzu bai tsaya ba, kuma harga Allah a lokacin ko da ace nayi sallama ne ba zan iya ɗaga kai na dube shi ba balle na iya yi masa magana, dan ban