NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 213 of 223

dy. gidansu Ya Kabir aka kaini, sai da aka kaini wurin Baba Daddy ya damƙa masa amanata, shima yay min kalar nasa nasihohin da faɗan sannan aka tafi dani ɓangaren Yagana, suka ƙara damƙa ni a hannunta, Yagana tana ƙwallar nuna farinciki take cewa ta amsa, fatanta Allah ya tayasu ruƙo...daga nan kuma su Daddy suka mana sallama suka wuce gida inda suka barni da sharɓar kuka. bayan tafiyarsu babu jimawa Mama Siddiqa wacce ta ke ƙanwa wurin Mamansu Ya Kabir ta shigo ɗakin, ta umarceni da na tashi nayi sallar la'asar, na miƙe jiki a sanyaye da tarin kunya na shiga bayi nayi alwala sannan na fito na gabatar da sallah. da su Adawiyya muka zauna a ɗakin muna ta hira, duk da na kasa sakewa jina nake kamar ban taɓa rayuwar cikin gidan ba, kamar baƙuwa na ke, Sadiya ma sai tsokanata take wai duk gulma ce ni dai bancewa kowa acikinsu ƙala ba. so nake ma duk su tashi su fita na samu sakewa da Basma tah. har magriba muna tare da su, kuma kowa da kalar tsiyarsa da yake min, Yagana ta kawo min wayarta da Shamsiyya ta kira. na amsa ina sallama, ban san lokacin da kukan da nake ta riƙewa tun ɗazu ba ya sauko min. tace dani,"ke dilla ni ba kuka na kira ki min ba". nace da ita,"Shamsiyya dan Allah kizo mu zauna tare kamin gobe mu tafi". sai ta saki wata munafukar dariya tana tambayata wai aina zan kwana yau ɗin da nake cewa tazo. kamar ina gabanta na saki harara nace,"ban sa ni ba, banza ƴar iska kawai". ta kuma ƙyalƙyalewa da dariya tana cewa,"naji dai...ke dama Ummi ce tace na faɗa miki ɗazu tayi mantuwa da humrarki a jakarta, amma Ya Kabir ɗin yazo ɗazu ta ba shi ya taho maki da ita, idan yazo sai ki karɓa". na turo baki nace,"amma dai ba cewa zanyi ya ban ba ko?". tace,"oho ke kika sa ni". duk sai naji ta ɗebe min kewar da ke damuna, mun jima muna hira tana ta zuba min iskancinta da ke cinta, wanda na rasa aina Shamsiyya ta san irin waɗannan abubuwan, da nayi magana sai tace,"oho ni dai faɗa miki nake in ba ki iya abu kaza da kaza ba kina ji kina gani wata can za tayi miki wuff da shi kuma babu yanda kika iya". **** anyi sallar isha'i ina zaune kan sallayan ban miƙe ba ina ta tunanin Mamina, sai ga Nawwara ta shigo hannunta riƙe da tray na kayan abinci, na amsa sallamarta ta nemi kan ƙaramin table ɗin da ke ɗakin ta ɗora akai, sannan ta dawo tace da ni. "Yaya abinci ne Yagana tace na kawo nan, wai ki shirya yanzun Ya Kabir ɗin zai shigo". nayi saurin ɗagowa nayi mata wani duba tare da cewa,"zai shigo yayi me?". sai tayi shiru kafin tace,"ance dai za'a kai muku abincin ɗakinsa yace a kawo nan". ban ƙara mata magana ba ta miƙe ta fita ina bin bayanta da harara kamar wadda tayi min laifi. na miƙe ina ninke hijab ɗin Yagana da nayi sallah sai ga shi ya shigo, ni dai banji sallamarsa ba ƙamshin tararansa ne kawai ya sanar da ni shi ɗin. ya shigo cikin wannan takun nasa da bana iya ɗauke idona akai amma ta yanda ba zai lura ba, ya ƙaraso har gabana sannan ya miƙo min baƙar leda yana faɗin. "ƴar gidan Ummi gashi inji Umminki". nasa hannu na karɓa ina turɓune fuska, na taka zan ƙarasa ga wadrobe ɗin Yagana naji yana tambayata wai menene a ledan, dan tunda aka ba shi yake jin ƙamshi, motarsa ma duk ta cika da ƙamshinsa, nayi kaman ba zance komai ba sai can nace. "me yasa ita da ta baka baka tambayeta ba tun acan". "ke naga damar tambaya ai". na juyo ina masa kallon ƙasan ido sannan nace,"to nima ban sa ni ba". sai kawai ya saki murmushi tare da cewan. "bari naje nayi wanka, yanzu zan dawo muci abincin...visa ɗinmu ya kammala amma goben a abuja zamu kwana sai washegari zamu wuce". ni dai bance masa komai ba har ya juya ya fice. yana fita Yagana ta shigo tana ta maganganunta, ita ma bance mata ƙala ba sai da ta gama abinda za tai zata fita sannan nace,"Yagana kice da wancan jikan naki ya dawo ya ɗauki abincinsa, zan rufe ƙofa ina jin bacci". sai ta dakata ta juyo ta dube ni da kyau sannan tace,"sannu sara mai baƙar takashi, ai mai hali ba zai taɓa fasa halinsa ba. to da za ki rufe ɗaki naki ne zaƙwaƙura?...ai sai ki bari ni da nake da iko da ɗakin in gama abunda nake idan na shigo kya rufe...". ban jira ta kai ƙarshen zancenta ba nace,"to ai dai naga da aka kawoni ke kika kawo ni ɗakin naki ko...to kije kiyi abinda za ki da sauri ki dawo zan kwanta". ta saki baki galala sannan tace,"to Uwar Yagana naji". ta juya ta fita tana faɗin,"ni dama da Amadun aka barki ya sai ta miki hali ba da wannan sanyi ƙalau ɗin mutum ɗin ba...da sonki zai hana shi hukunta ki". na zauna bakin gado ina jiran Nawwara da na kira a waya tazo ta ɗauke abincin da ba cinsa zan ba ta fita da shi. sai kawai ganinsa nayi ya shigo sanye cikin ƙananun kayan da idan nace bai yi kyau acikinsu ba ma nayi ƙarya, muna haɗa ido na ɓata rai. ya ƙarasa bakin table ɗin ya zubo abinci a plate sannan ya ijje akan carpet ya umarceni da na sakko muci. nayi masa shiru na kauda kai. ya ƙara cewa,"yanzu fa Ummi ta kirani tana tambayan kinci abinci". nace,"to ni ba zanci ba na ƙoshi...kuma ka
🏠