NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 212 of 223

mu akai min ke ɗakina, za ki sha mamaki, za ki sha mamakin sonki da ya shekara goma sha daskare a zuciyar Kabir". Allah ma ya sa ni a lokacin ba zan iya cewa komai ba, kuma ba zan iya aiwatar da komai ba, illa bige hannunsa da nayi dake neman shiga cikin rigata. murmushinsa mai sauti ya fito haɗe da cewar,"wai duk wannan dogon bayanin da na maki ba ki yarda da ni ba?". cikin sauri na ɗaga masa kai. sai ya lakuce min kumatu da faɗin,"to kar ki yarda ɗin, ni dai ai nasan haka ne, kuma tunda Ummi ma shaida ce kar ki taɓa yarda ɗin...ni ai ba yaronki ba ne da zan tsaya kina min yanda kika so, da ki yarda da ni ma har saina miki kalar tausayi, to sannu Yagana". nace da shi,"in ka iya tsara Ummina ni dai ba zaka tsarani ba...dama ai nasan duk ƙarya ne kake gillawa...". sai ya ɗalle min baki yana cewa,"wai ni sa'anki ne da kike faɗin ina miki ƙarya? ko kin manta wane ni, ni ne fa wannan Ya Kabir ɗin naki". sai naja hancina a lokacin da nake jin wani mixed feeling nace,"kai ɗin, ina ruwana da kai". "zanyi maganinki ne soon, ranar da aka kai min ke ba za ki samu damar faɗa min haka ba". sai kawai nasa kukan shagwaɓar da ban san lokacin da ya zo ba ina faɗin. "ai dama nasan kasheni za kai shi yasa ka aureni, kuma ni ka sakeni ko kuma duk abinda nayi maka a gidan kai ka siya da kuɗinka, ai na faɗa maka bana sonka, dan haka ka rabu da ni tunda kaima ba sona kake ba". na lura wannan kalmar tawa na saka shi a wani yanayin, a jikina kawai na tsinci ɓacin ransa, a irin matse hannuna da yay na tsinci irin ɗacin da yake ji idan nace baya so na, so kawai sai na shiga raira kukana a hankali, shi kuma ya miƙe ƙafafunsa yana jingina da gadon, sannan ya sakani tsakiyar ƙafafunsa ya lafar da ni a ƙirjinsa, lokaci kaɗan naji bacci ya fara fizgata, kafin baccin ya ɗaukeni gaba ɗaya ina jin time ɗin da yake waya da wanda ya kira da su na Abdurrahim yana faɗa masa shi dama ai ba ma'abocin yin abunda mutane suka raja'a akai bane, in dai dinner ce zai yi gagarumar dinner amma a gidansa, cikin ɗakinsa, kan gadonsa, a cikin wannan daren. kuma baccin da nayi ban san lokacin da ya tafi ba, na farka naga babu shi, sai naji na farka da mararin son ganinsa a lokacin, har nake tambayar Shamsiyya wama ya maidani kan gado, ta harareni tace sai na kira shi wanda nayi baccin ajikinsa na tambaye shi. tana ƙara ce min wai wallah wannan Ya Kabir ɗin ba shi da kunya, in banyi hankali da shi ba sai ya dinga bada ni a gaban mutane, nace me yayi tace wai na tambayi Ummi ta ban labarin a yanda tazo ta samemu, kuma ganin nata baisa ya daina abunda yake ba, tayi magana kuma yace wai ai Maryam ɗinsa ce. tsaki kawai nayi a lokacin na sakko daga kan gadon na shiga banɗaki da tunani kala kala acikin ƙoƙon kaina. Anty Iftihal da ta shigo yanzu bayan ta gaida su Abi da Daddy tace,"zamu iya tafiya?". Bella tace,"babu damuwa". Daddy ya miƙe yana faɗin,"da wa zamu tafi?". Ummi ta miƙe tana cewa,"ai ƙafata ƙafar ƴata". Ummi ta duƙo ta ɗagoni na tsaya akan dugadugaina, sandararriyar ƙafata na neman ta watsar da ni na zube. na hangi Mamina na goge ƙwalla sai kawai na ƙwace daga hannu Ummi na faɗa jikinta ina fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taɓa zuciyar duk mai saurare. Mami ta rungumeni tsam ajikinta itama tana kukan. muryarta na fita da amon kuka tana faɗin. "Allah ya sani bana son rabuwa da ke, amma babu yanda zanyi aure ibada ne kuma sunnar ma'aiki wadda ta zamar mana dole mu rayata...Auta Allah yayi miki albarka kinji, Allah ya albarkaci dukkan rayuwarki, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah ya tsare gaba da bayanki, Allah ya rabaki da sharrin maƙiya mahassada, Allah ya ɗoraki akansu, yasa ki zama mai rinjaye akansu...Ya Rahmanu yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Ya Maliku yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Ya Hayyu ya qayyum yasa masa tausayinki a zuciyar mijinki, ya ƙara ninka soyayyarki a zuciyarsa, Allah kuma ya ba shi ikon sauke nauyin duk wani hakki naki, ubangiji yasa ku zamewa junanku inuwar salama har ranar alƙiyama, Allah ya baku zuri'a ɗayyiba, Allah yasawa zuri'ar da zaku samar albarka, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi...Dan Allah Auta ina roƙonki kiyi riƙo da dukkan tarin nasihohin da aka miki, karki watsi da su dan bana so ki koka ko kaɗan, yin watsi da su dai-dai yake da yin bankwanan farin ciki a rayuwar aurenki...ina sonki, ina sonki sosai ƴata...duk wani abu da kike so ki kirani ki sanar da ni kinji ɗiyar albarka, zanyi kewarki sosai". tayi maganar ƙarshe tana sa hannu ta goge min hawayena alhalin nata ba su tsaya daga zuba ba. cikin kuka nace,"Mamina na fasa auren kinji". sai kawai ta kauda kai gefe dan kar naga sabon hawayenta da zai zuba. da ƙyar da siɗin goshi aka rabani da jikinta. Daddy ya kama hannuna na dama, Ummi ta riƙe na hagu suka fita da ni daga ɗakin, kuma muna isowa haraba busar algaitu ta fara tashi, ana kwararo adu'a da kirari wa ni da su Dad
🏠