sauka a daren jiya, sai Ammi da Bella da Ummina da Mamina, da Hajjah Nashwa da Shamsiyya duk su na zaune, kuka nake amma mara sauti, hawaye wani na bin wani saman fuskata, yana ɓata ƙwalliyar da aka ɗauki tsawon lokaci a safiyar yau ana min ita, kwalliyar da Ummina ta kasa rufe baki tana ta aukin yabawa, faɗa ta ke wai ai Kwalliyar Kabirunta ce, Kabirunta za'a yiwa dan haka Mai Kwalliyar ta baje duka basirarta yau, tayi kwalliyar irin yanda nake sheƙi kaman dafaffan ƙwan da aka ɓare, ni dai ko a lokacin murmushi ma ban iya ba, saboda a cikin fargaba nake, faɗuwar gaban da ta riskeni tun a jiya da na fito daga wannan jikin da ya rungumeni, na buɗe ido nayi tozali da mutumin da tun a ƙamshinsa na gama shaida ko waye.
a yanzu da Mai Martaba sarkin bichi yay shiru, Bella ta kada baki ita ma ta kira sunana, nayi shiru na kasa amsawa saboda ƙullutun da ke maƙale a throat ɗina, cikin wannan muryartata da ke fita da zallar izza da ƙasaita ta ƙara kiran sunana. "Maryam amsa min za kiyi". na buɗe baki na amsa kiran da muryata da ta gama disashewa da kuka. "Maryam Haƙuri, Haƙuri, zaman aure gaba ɗayansa haƙuri ne, Maryam haƙuri shi ne jigon zaman aure, sai da haƙuri aurenki zai yi lasting Maryam. dan haka Maryam idan ba ki san shi ba to ki nemo shi duk inda yake ki kamo shi, ki ƙanƙame shi, irin ƙanƙamar da ba zai taɓa suɓuce miki ba...haƙuri ba wani abu ne mai wahala ba, mutanene kawai ke ɗaukansa a matsayin kaya, amma muddin mutum ya riƙe haƙuri to tabbas darajarsa hauhawa za ta dinga yi, domin shi haƙuri arziƙi ne babba Allah ya nufe ka da samunsa, dan ba kowa Allah ke bawa ba sai kaɗan daga cikin bayinsa, da haƙuri da tawakkali haka suke". Hajjah Nashwa ta shiga maganar Bella da cewa,"to ai rayuwarma ita kanta haƙuri ce". Bella ta gyaɗa kai,"to dai...dan haka ni iyaka abinda zan daɗa jaddada maki kenan, dan tun jiya kike shan nasihohi a gidan nan". Ammi da naji shigowarta babu jima tace,"Maryam tun jiya nake ce miki ki zama mace ta gari, kuma ko kullu yaumin zanke zuwa gidanki ba zan daina faɗa miki wannan kalmar ba...Mace ta gari Maryam bata fallasa sirrin rayuwar aurenta ga kowa, ki zama mai riƙe sirrin gidanki, ina kuma tunasar da ke akan yin biyayya ga mijinki dan samun rahamar Allah acikin rayuwar duniya da Lahira, ki zama mai gaggawa wajen cika umarnin mijinki, ki zama mai kiyaye dukkan abin da zai ɓatawa mijinki, ki zama mace ta garin da idan mijinki ya kalleki zai ji farinciki ya lulluɓe shi...tun jiya na gama faɗa miki macen da ake kira da mace ta gari, Allah ya baku zaman lapia". Ummina ma ta fara magana da irin muryar da ke shaida rauni na zuciya tana cewa da ni,"Daughter nah dan Allah kar ki zama mace mai halin maza a gidanki kinji, namiji ba ya son wannan, abun da nake nufi kar ya zamana ba ki iya kisisina ba, ya zamana kin iya dabara, girki da kuma shagwaɓa ba, da kwalliya, da soyayya mai rikita kwanya, Daughter da iyaka waɗannan ma za ki mallake zuciyar mijinki...Allah yay miki albarka kinji". sauraronsu na ke tare da saƙa abubuwa da yawa araina, tun jiya zuwa yau komai sai dai ace Maryam ki zamarwa mijinki kaza ko kiyi masa kaza, to shin ni bani da hakki akansa ne da ba za ace yay min duk abubuwan da nake so ba? ko kuma ni banda abubuwan da nake so? ko kuma shi ma za'a faɗa masa nasa kamar yanda ake faɗa min?...nayi shiru ina ci gaba da sauraron faɗan Dad da ya amshe shima, faɗa yake min sosai tare da wasu nasihohin da suka sanya ƙafafuna wani irin sanyi, ni dai wannan aure ji nake kaman nace na fasa, dan har yanzu ma ni ban gama sanin me zuciyata ke ciki ba ga me da Kabirun da aka laliƙa min. nayi mamakin kaina ajiya, nayi mamakin kaina sose dana kasa fesar masa da kalaman rashin kunya da masifar da na tattaro zanyi masa a lokacin da na buɗi ido na gansa...abun da ya faru a lokacin na iya ƙarfin halin saka ƙwayar idona a tasa tarr babu ko ƙifce, sai dai abubuwa biyu da na hasko a cikin idanun nasa suka hanani aiwatar da abunda nayi niyya, wannan kwarjinin nasa, da kuma ƙyallin wani abu da na kasa tantance menene, kawai dai nasan ya zama silar mutuwar jikina gaba ɗaya. da ƙyar na iya kai hannuna da na dunƙule na kai masa duka a kafaɗa, sai kuma na fashe da wani irin kuka da ban taɓa yin irinsa ba, sai ya saki murmushi yana riƙe ɗaya hannun da na kuma kai masa duka dalilin ganin yana wani munafikin murmushi...yasa hannunsa a haɓata yana tambayata menene, sai na ture shi ina ƙara sautin kukana, ina ƙara kumbura sai aukin huci nake, na buɗi baki zan amayar masa da abunda ke dunƙule a ƙirjina cikin ƙarajin bala'i, amma sai naji muryata na fitowa cikin sanyi kuma a hankali nace. "da wacce manufar ka aureni Kabir, wanne irin shiri kai na ganin ka ƙuntatawa rayuwata da har kasan yanda kayi ka rabani da masoyina na gaskiya...to wallah bari ma kaji ta kowacce tsiya da bala'i sai ka rabu da ni, sai ka sakeni yanzu bada jimawa ba dan ba zan taɓa zama da kai ba, bana sonka kuma ba zan taɓa sonka ba, dan Allah ka faɗa musu ka sakeni n