NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 223

ƙunci. Mairo kar ki sake sharrin zuciya ko soyayyar ɗa namiji su yaudareki ki aikata Zina, dan wallahi wallahi sai kinji dama mutuwa kika yi akan rayuwarki, yanzu ke ba yarinya bace, kinyi girman da zaki san komai ki kuma san inda ke miki ciwo...wannan jini da kika ganki acikinsa ɗazu bana haihuwa bane jinin girmanki ne, ada idan namiji ya taɓaki za ki zauna lafiya amma banda yanzu, karki bari hawayen dana daɗe da tsaidasu na tsawon shekaru goma sha huɗu suci gaba da zuba a saman fuskata, ki taimaka ki barsu su tsaya iyaka zuciyar, dan duk ranar da kika kuskura kika ɗauko min abun kunya Mairo saina kasheki kamin baƙin cikinki ya kashe ni". Maganarta ta ƙarshe ita tasa na haɗiye wani dunƙulallan yawu a maƙoshina wanda ya wuce da ƙyar, tsoro ya shigeni, Zina! Zina! Zina, kalmar da nake daɗa nanatawa acikin kaina kenan tun bayan da naji Gwaggo tayi shiru, _"kar ki sake sharrin zuciya ko soyayyar ɗa namiji su yaudareki ki aikata Zina."_ wannan kalaman na Gwaggo suka daɗa haskawa acikin kaina, mene sharrin zuciyar da har zaija na aikata zina?, wacce iriyar soyayya namiji zai nuna min har na aikata zina?, shin da ma ita zinar waɗannan abubuwa biyun ke janyota?, ya ya zinar take ne? Mecece ma ita zinar?, wanne irin hawaye Gwaggo tayi wanda take gudun sake zubarsu a yanzu?. Na rufe idanuwana na mirgina kwanciyata ina fuskantar rufin kwanon ɗakin, ayau dai na tabbata ba zan iya bacci ba cikin wannan daren, saboda maganganun dake tushe acikin kwanyata waɗanda ke neman tarwatsa min kai, ban warware zantukan Baba ba, ga Gwaggo ta kuma ɗura min wasu, na damƙe kaina da nake jin kamar zai rabe gida biyu. Nafi awa biyu ina juyi bacci yaƙi ɗaukata, da na rumtse ido sai naji gabana na faɗuwa, na tuna da wani wa'azi da muka taɓa saurara a radio da azumi, hakan yasa na miƙe na zuro ƙafafuna domin na fita na ɗoro alwala nazo nayi nafilfili, sai naji maganar Gwaggo na tambayar ina zani?, na waigo muka haɗa ido da ita nace zanyi sallar dare ne. Ta kuma jefe min tambaya,"salloli nawa kika yi ayau?". "duka nayi ɗazu dana farka". "to kar ki ƙara yin sallah har sai kinga wannan jinin ya ɗauke miki, ba'a yin sallah idan ana yinsa". Murya na rawa nace,"to Gwaggo yaushe zai ɗauke?". "idan ya ɗauke za ki kalla ya daina zuba. Ki kwanta haka". Na miƙa hannu na ƙaro hasken fitila na dubi fuskarta, muryata sanyi ƙalau nace,"Gwaggo kuka kika yi?". Ta gyara kwanciya inda ta juya min baya sannan tace,"waya mutu da zanyi kuka, hammar bacci ce, ki koma ki kwanta dare yayi sosai". "zanje fitsari". Bata kuma amsani ba, na sakko na nemi ledar ɗazu na zari abar da Kulu ta saka min a wando, dan a karatun bebayen da tayi min a ɗazu har da nuni da sauyata akai akai, na raɓa ta gefen shimfiɗar kulu na fita, da ƙyar na shiga bayi saboda duk a tsorace nake, aikuwa na tsorata sosai da yanda naga jini ya wanke farar audugar, na zareta daga jikin wandona na buɗe murfin masai na jefa aciki sannan na manna sabuwa tukunna na mayar da wandona. Fitowata daga bayi ina ƙoƙarin ɗauraye hannu, nayi saurin tarar butar dake neman faɗuwa daga hannuna ina cije fuska gudun kar aji motsi, ba ƙaramin razana nayi ba ganin Kulu ta shiga ɗakin Baba a wannan silasainin daren, na koma da baya na ɓuya, ina kallo ta fito ta shiga madafa ta ɗauki kwano ta tuttuli ruwa aciki sannan ta koma ɗakin, tana shiga kuwa nayi saurin fitowa na dawo na laɓe a ƙofar ɗakin Baba ta inda babu me iya ganina. Maɗaukakin mamaki da al'ajabi suka lulluɓeni a sanda na jiyo maganar Kulu tana cewa da Baba, "daga ina Allon ya ke?". Muryar Baba ta fita daga can nesa yana amsa mata da, "ɗaga wannan buhun yana wajen". Shiru ya ɗan gimla kamin ya ƙara da ce mata, "kin tabbata ruwan saman kika tsiyayo?". acikin hausarta da naji bata fita sosai tace,"ehh ina da tabbacin shi ne, dan jarkar naga Yaya ta tara daren jiya". nayi wata daskarewa a wajen, ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa da tarin tambayoyin dake cikinta, kenan Kulu ma matar Baba ce? Dama kuma tana magana? Kuma dama lafiyarta ƙalau?, to amma me yasa...?, cak na sume a tsaye ina bin Gwaggo da kallo wadda ta nufo hanyar ɗakin Baba, dai-dai fitowar kuma Kulu, ban mutu a tsaye ba sai da naji Kulu ta kira Gwaggo da,"Yaya". Ta faɗi hakan muryarta na rawa. Gwaggo ta kama hannunta suka koma ɗakin tana cewa,"bana son kuka ki haɗiye shi". ba zan iya faɗar irin ruɗanin dana shiga ba, naja ƙafafuna da ƙyar na wuce ɗaki, sai dai ina shiga ɗakin na zube a ƙasa na zama mutun mutumi, lamuran daketa faruwa da ganina da jina a yau sunfi ƙarfin kaina. *#Comment & Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *6)* Ta-ke idona ya firfito waje, gumi ya jiƙe min jiki, tashin hankalin da ban taɓa shigarsa ba ya dirar min, tsorona Allah tsorona irin wawan kallon da Gwaggo ke jifana da shi, na haɗiyi wani wahaltaccen yawu a maƙoshina, na runtse ido ƙirjina na dukan tara-tara, kafin na ka
🏠