kardu a motarsa, ananne yaci karo da ainihin takardar da ke ɗauke da result ɗin Ahmad na SS, ke kin san wane mahaifinki ba sai na ɓata lokaci wajen yi miki dogon jawabi ba, dan haka nasan yanzu kin gane dalilin da ya sa aka fasa aurenki da shi. ni na faɗa miki ma hope ɗina ba akansa yake ba, sai a yau nake farin ciki da aurenki Maryam, wallahi sai a yau nake murna". naja majinar hancina muryana a dashe nace,"to amma auren dole ne ba sai a ƙyaleni ba...". kuma ban kai aya ba, bayan yatsun Mami suka sauka akan laɓɓana, kan ciwon da taji min a ɗazu, sai na kuma fashewa da wani sabon kukan ina cewa,"ni dama Mami na san ba kya sona, shikenan, indai wannan ɗan'uwan naku Jawad ne naji zan zauna da shi amma ba dan ina sonsa ba, kuma ba dan zanyi tolerating duk wani yayinsa da zai zuba akaina ba...". "balle ma ba Jawad ɗinne mijinki ba, barrantana ki sami damar walaƙanta mana ɗan'uwa son ranki". na juyo ina duban Ummi cike da ruɗani, kafin na buɗi baki da ƙyar nace da ita,"Ummi to to wane mijin?". nayi tambayar ina mai ƙara fashewa da kuka, murya a rarrabe.
"wannan mutumin da ya ɗauki tsawon shekaru goma sha ɗaya yana sonki, wannan mutumin da ya fara sonki tun a lokacin da ya san wace ke, ba wai wace ke a wannan matsayin da kike kai ayanzu ba, wace ke a wancan lokacin da ya san ke shegiya ce, wannan mutumin da zuciyarsa ta cika da sonki da kuma tausayinki, wannan mutumin da yake kwana yana tashi da fargabar ki san asalinki, wannan mutumin da ya fara zubar miki da hawaye tun kafin naki su fara zubarwa...". ni dai ban bari Ummi ta ƙarasa zancenta ba na katseta da cewar,"na shiga uku Ummi, Ummi kar ki fasa min kai, kar ki sa ƙwaƙwalwata ta tarwatse...wai shi wannan mutumin da kike ta faɗa tsawon lokaci ba shi da su na ne?, ko kuma ba mutum bane da idanuwana ba zasu iya ganinsa ba ne?...". maganar na ke idanuwana a kulle, ina jujjuya kaina, kuma ban ƙarasa abin da nake son cewa ba maganar da naji Ummi na faɗi tasa nayi shiru. "ka shigo kaji da rigimammiyar matarka, ba zan iya da tambayoyinta ba". ban kai ga buɗe idanuwan nawa ba naji cikar girma da haiba na mutumin da Ummi ke magana sun cika ɗakin baki ɗaya, take naji wani sanyayyan ƙamshi na bin hancina, ƙamshin da ya shiga jikina ya wanzar min da ko wanene tun kamin na kai ga buɗe idona, a jikina nake jin takunsa, a rufaffun idanuwana nake hasko yanda doguwar ƙafarsa me ɗauke da zara-zaran yatsu ke takowa suna isowa inda nake, san da ya tsunguna gabana ya kamo hannuna da sanyayyan hannunsa mai taushi ya tabbatar min da mutumin da nake zargi, amma duk da haka ban buɗe idona ba, illama ƙara runtsesu da nayi sosai, sannan na kai hannunawana duka biyu na ɗora a kunnena dan toshe su daga jin dukkan wanzuwar wani abu da ban shiryawa jinsa ba a tare da ni.
tukunna na buɗe ƙaramin bakina duka zan kurma ihu, amma sai duk wani shirina ya tsaya cak, san da ya tarairayoni jikinsa gaba ɗaya, yay min matashi da ƙirjinsa, yay min rumfa da faffaɗan kafaɗunsa, ya kuma ɗora hannunsa kan sumar kaina da babu ɗan kwali yana shafawa a hankali, a hankalin da yake haɗewa da sabon kukan da nake son fashewa da shi, a yanzu da nake lafe a jikinsa ƙamshinsa ya ƙara samun damar shiga hancina yana motsani da kyau, wannan ƙamshin dai guda ɗaya da jinsa ke saka zuciyata ta motsa. kakkausar muryarsa ta fito a hankali, sam bana son jin wannan kakkaurar muryar tasa da ko cikin bacci na jita zan shaidata, wannan muryar da ko mutuwa nayi na dawo ba zan taɓa manta mamallakinta ba, tana da tsiri a gareni sosai, irin tasirin da nake ji a gangar jikina da ƙwaƙwalwata gaba ɗaya.
a tausashe muryar tasa ta fito ta ratsa cikin kunnuwana da ambaton sunana, furucin sunan nawa da ya fito cikin wani irin amon sauti, cikin wani irin salo da ya nemi kassara ɗan kuzarina. "Maryam Don Allah". sai kuma ya ƙara tsamkeni yana ci gaba da faɗin,"dan Allah ki daina bana so, bana sonsa Maryam, wannan kukan babu abinda yake haifarwa sai illata zuciyar da babu komai acikinta face sonki da ƙaunarki...".
Ya Rabb! a wannan lokacin, babu abin da nake so illa na fito daga hannuwan da nake kewaye a cikinsu, sannan na buɗe idanuna da dukkan fatana na duniya naga akasin abun da nake ji.
_____________________________________
*_the only way you people will show your love and appreciation towards me is by voting and commenting on this story. please don't exit any page without dropping a comment, it encourages me to do more._*
[7/18, 15:55] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*(51)*
*washegari*
*02:00pm.*
akan ƙafafuna nake acikin turakar mai martaba, kaina a ƙasa cikin hular alkyabbar da aka saka min white colour, tunda aka wayi garin yau naji cewar za'a kaini gidana, zanje inda zan fara wata sabuwar rayuwar da ta ke daban da irin wacce nayi a baya, gidana, gidan aurena, shikenan jikina ya mutu gaba ɗaya, wani irin yanayi nake ji da bazan iya kimanta shi ba. a yanzu da nake a tsakiyar turakar mai martaba ina fuskantarsa shi da mahaifina, da Kakana na wajen Uwa da ya