NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 208 of 223

annan zafin wutar marin. dalilin sassauta kukana kenan, dalilin fara natsuwata kenan har nake iya danne gunjin kuka na, dalilin fara lallamar zuciyata kenan akan tayi haƙuri, dama ita bai zama lallai ta zama mai farin ciki yanda taso ba, kuma dama ai na faɗa tun kwanaki, sai tayi haƙuri da duk wani ƙalubale da zata fuskanta, wannan ƙalubalen da Asalina ne zai ta jefata acikinsa. na ɗaga ƙwayar idona ina kallon Mami da ke hakimce akan one seater tana amsa kiran wayar da aketa ma ta a ɗazu na Allah sanya alkhairi, hankalinta kwance, sai farin ciki take abinta, kamar ba ita ce mai ɗiyar da zuciyarta ke ƙoƙarin bugawa ba nan kusa. hawaye masu zafin gaske suka shiga zubo min babu ƙaƙƙautawa, Shamsiyya na goge min da tafin hannunta, amma da zarar ta goge da wani ya kuma biyo baya. tsoronta Allah tsoronta Mami ta ɗago ta ganni ina wannan kukan, tun ɗazu tayi ƙasa da murya tana roƙona da Allah nayi haƙuri nayi shiru kar Mami ta ganni, dan Mami ce tayi ruwana ne nayi shiru ruwana ne naci gaba da kukan, dai-dai take da iskokan da suke kaina. har a lokacin ta buɗe min tafukan hannunta ta nuna min yatsunta tace min,"Maryam tun da har ba hannun da za'a kashe ki muka miƙaki ba, to billahil azim rabon wannan yatsun nawa su tsufa ne akan fuskarki yau". sannan ta ƙara nuna min doguwar ƙafarta tace,"sannan rabon wannan ƙafar ta dirje fasonta ne a jikinki...kar ki sami damar shiga hankalinki". ni ba ma sai ta kai ga nan ba, abunda bata sani ba ƙwayar idonta ma kaɗai sawa suke na shiga hankalina. sam taƙi bani damar da zan tambayeta dalilinsu nayi min hakan, taƙi bani fuskar tambayarta sam, ga Ummi ma tun ɗazu ban ganta ba, so nake naji me yasa za su rabani da zaɓin raina?, me yasa za su haɗani da Jawad bayan sun san cewar bana sonsa?...zuciyata ta tsayar dani cak a san da take cewa,"me yasa ba za ki tambayi kanki cewar ko shi Ahmad ɗinne yace ya fasa aurenki ba, ko kin manta ke wace? ko har wata ƴar guntuwar soyayya tasa kin manta ta yanda aka samar da ke ne?". sai naji wani dunƙulallan abu a maƙoshina, na rumtse ido na kora shi da yawun bakina da ƙyar, sannan na ɗago na kalla Shamsiyya cikin rawar murya nace da ita,"Yaya ya kira ni?". "taya za'ai ya kiraki, kema kin jiki da wani zance". sai kawai na maida kaina jikin gadon, wasu sabbin hawayen suka shiga sunturi, dama na faɗawa Yaya tun farko, nace masa ni shegiya ce ba zai iya aurena ba, me yasa ma na sakankance da yawa har haka?. "Keee". Mami ta kirani a tsawace, nayi saurin ɗagowa ina dubanta a diririce. kallona take tana cewa,"kar ki ƙullaci ɗan mutane a ranki, Ahmad ba shi yace ba ya sonki ba, result ɗin genotype ɗinku shi ya rusa komai". jikina na shaking muryana na breaking nace,"how comes Mami?, result ɗinmu fa ɗaya ne, kawai dan kuna so lallai sai na auri Jawad shi ne zaku fa-ke da wani result". ban ƙarasa rufe bakina ba naji saukar wayarta da ta jefo min a bakina ba tare da gudun wayar ta fashe ba, jifan wayar ya fashe min baki dan ba wulli mai sauƙi tayi ba. zafi yasa nayi saurin saka hannu a wajen ina rumtse idona zafin na daɗa ratsa jikina. na kalleta sau ɗaya nayi saurin ɗauke idona saboda irin kallon da take jifana da shi, tantanma nake anya kuwa Mami na sona. "miƙon wayata". maganartata ta kutsa cikin kaina da wani amo mai firgitarwa, na zuro ƙafafuna ƙasa na shiga takawa jiri na neman ɗibata ya zubar, sarai tana kallo da ƙyar nake tafiya amma ce min take faɗuwata ba damuwarta bace, na faɗi wayarta ta sami matsala shi ne damuwarta, kuma babu abinda zai hanata sauke wannan takaicin akaina. wannan furucin nata shi yasani isa gabanta cikin taku uku ba tare da na shirya ba, na zube gwiwoyina gabanta na miƙa mata wayar, maimakon ta karɓa sai ta kamo kunnena ta murɗe da iyakar ƙarfinta tana ce min,"mu ke da iko da ke bake ke da iko damu ba...kinyi kaɗan ki tsaremu da tarin tamboyinki Maryam, muke da ikon zaɓa miki miji, dan haka maganar ma mu biki ta maslaha da lalama ko na fahimtar da ke bai taso ba, ubanki zanci wallah idan ba ki daina min wannan kukan ba, zanci ubanki major ne idan ba ki hankalta ba...zai fiye miki ma ki fara koyawa zuciyarki sonsa tun yanzu, tun kamin gobe na miƙa ki ɗakinki...in yaso idan na kai ki ki haƙa rami ki binne kanki aciki shi ne ƙarshen da za ki nuna min cewar ko waye yayi kaɗan ki zauna da shi". sai da tayi kamar zata tsinke kunnuwana kafin ta cika su, sannan a hankali na jiyo muryar Ummi da ke bin iska tana shiga kunnena da cewa. "ba haka kawai muka hanaki Ahmad ba Maryam, sanin kanki mu ba mutanen banza bane, ba ƙanan mutane bane da zasu aiwatar da hakan babu wani ƙwaƙwƙwaran dalili...kawai abin da nake so ki fara fahimta shi ne ki yarda da cewar dama tuni Allah ya ƙadarta cewar ke da shi ba zaku zauna a inuwa guda ba...Almustapha ya faɗawa Daddynki result ɗin wani Ahmad ɗin daban ba tare da shi kansa ya san da hakan ba, kasancewar time ɗin da Daddynki ya kira shi yana cikin aikin da yaywa kansa yawa, kuma sai a safiyar yau da Daddynki na duba ta
🏠