NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 207 of 223

ban ango. ango kuwa a wannan lokacin farin cikin da ke tare da shi Allah yayi yawa da shi, jin abin yake kamar a mafarki, haƙurinsa da Akila take cewa ya cuce shi yau gashi ya zame masa rana, shi ba zai iya misalta irin tarin abun da yake ji a tare da shi ba, abu ɗaya kawai yasan yanayi tun shigowarsa masallacin lokacin da ya tabbatar da maganar Baba Mujibu shi ne godiya ga sarki Allah. ya cire Maryam a ransa tuni, ya gama cire Maryam a lissafin zai sameta, ashe Allah ya rubuta a lauhul mahfuz Maryam mallakinsa ce. sam-sam ya kasa hana kansa nuna abin da yake ji, duk wanda ya kalle shi zai shaidi yana murna da faruwar abun. shi a yanzu ma an hana shi sukuni dan Major da Mai Martaba sun riƙe shi sai faman gaisawa ake da shi ana ɗaukar hoto, ga Alhassan da Suhail ma basu barshi ba, daga wannan yaja shi can ai hoto da mutanensa sai wannan ma ya kuma jansa. yayin da shi hankalinsa ma kwata-kwata ba anan yake ba, yana can duniyar Maryam, so yake kawai taron ya watse, in ace ya san idan ya biyo Baba Mujibu masallacin fada zasu yo to da bai biyo shi sun zo tare ba, duk da yasan ba lallai ne Maryam ta bada hankalinta ta fahimci komai ba a ƙarancin lokaci, amma atleast sai yayi duk yanda zaiyi ya hana hawaye fitowa daga idonta. an ɗau tsawon lokaci kafin jama'a su fara watsewa lokacin tafiya reception yayi, kuma a wannan lokacin da aka fito za'a tafi ɗinne Baba ya girgiza kansa yace da Mujibu. "Kaga yaron nan Ahmad har yanzu bai iso ba." "Yaya kaima kasan ba lallai yazo ba, saboda an riga an kar ya masa zuciya". sai kawai Baban ya juyo da kansa yana hango inda Kabir ke tsaye shi da Suhail a wani sabon cuncurundon ana masu hoto, ya umarci Aminu da ya kira shi, kuma a san da ya iso kansa na ƙasa yace da Baban. "Baba da baku yi saurin yanke wannan hukuncin ba." Baba yay murmushin manyace tare da dafa kafaɗar Kabir ɗin yace,"a lokacin da ake ƙoƙarin Jawad ya maye wannan gurbin Akila ta faɗa mana komai, komai ɗin tun daga mafari har zuwa yau...haƙiƙa na jinjina maka ɗana, sai dai ban san ko shi ɗan'uwan naka zai iya yin haƙurin da kayi ba". "zai yi Baba, ni na sani, haƙurin ai a jininka ne". Baban ya ƙara girgiza kansa,"inda zai yi me ya hana shi zuwa?". kafin Kabir ɗin ya buɗi baki yace wani abu suka ji Lukman na cewa,"gama Ya Ahamd ɗin nan". duka sai suka karkata hankalinsu ga motar da Ahmad ɗin ke fitowa, a saman fuskarsa kaɗai zaka tsinci abunda yake zuciyarsa. ƙwayar idonsa da ta Kabir suka sarƙe wuri guda na tsawon sakan ɗaya, sannan idanun Ahmad ɗin suka kulle ya rumtsesu da kyau yana jin wani abu na tsaya masa a ƙirji, yana jinsa ya tafi zuwa wata sama mai nisa sannan ya faɗo, yayi zaton idan ya iso zai tarar da komai da yaji a matsayin tatsuniya, dalilin ƙwarin gwiwar da ya samu kenan na zuwa, amma zuwan nasa tun a ƙofar masarautar ya samu shaidar tabbaccin da gaske an ɗaura ɗin, an ɗaura auren Maryam bada shi ba, kuma ganin Kabir ɗin yasa ya ƙara gasgata da shi ɗin aka ɗaura auren ba wani daban ba. sai ya shiga buɗe idanuwansa a hankali ya sauke su akan duwatsun da ke baje a ƙasa, sannan ya shiga miƙa hannu ga tarin mutanen da suke taya shi murnar bikin ɗan'uwansa, kowa na cewa da shi Allah ya sanya alkhairi, da ace ƙaddara bata shigo lissafin aurensa ba, da yanzu wannan adu'ar Allah sanya alkhairin tasa ce, shi gaba ɗaya ma lamarin nema yake ya zuƙe masa ruwan kai. yay ƙoƙarin nemo courage ɗinsa ya shiga bin bayansu Habib har suka ƙarasa wurin da su Baba suke, yana zuwa kuma ya miƙawa Kabir hannu yana ƙawata fuskarsa da murmushi mai sanyi, Kabir ɗinma ya miƙa masa nasa hannu su kai shaking tare da rungume junansu. Ahmad na cewa da shi,"Congratulations". shi kuma yana amsawa da,"thank you". ya rigada dama ya sani, dan haka a yanzu da yake ganin farin cikin da ke lulluɓe da Kabir ba sai ya tsaya wani mamaki ba, nan suka tsaya akai snapping pictures da su tukunna aka ɗunguma aka wuce wurin reception, ƙaton hall ɗin da Major ya kamawa ango dan shagalinsu shi da abokansa. **** *ɗakin Ammi, a dai-dai wannan lokacin.* nayi saurin kai hannuna saman ƙirjina ina dafewa, ina iya jiyo wani dunƙulallan abu, wannan dunƙulallan abun da ya tsaya min a ƙirji ya hana iska wucewa ajikina. a karo na biyu da Shamsiyya ta kuma saurin riƙoni daga faɗowar da zanyi daga saman gadon, a wannan lokacin idan ka kalleni bai zama lallai ka musa cewar jinya nake ba, saboda cikin wasu mintuna na koma sai aikin riƙoni ake, dan ko a lokacin da na suma Mami tayi zaton ta rasani ne, kukan da na buɗi ido naga tana yi a lokacin zan iya cewa nawa bai kai nata ba. amma kuma lokaci ɗaya bayan ta tabbatar da cewar a hayyacina na ke, sai naga ta koma kamar ba ita ce mai kuka da ihun zata rasa Maryam ɗinta ba, neman fitar hayyacin da nake ya dawo da ita Aaliyan da na fara tozali da ita a rayuwata a ranar farko, a wannan ranar da ta wanwankeni da marukan da zan rantse har duniya ta naɗe ba za'a kuma yin irinsu ba, dan ita kawai ta iyasu, kuma a hannunta ne kawai akwai w
🏠