mi yafiyarsu ban faɗa da wannan ba balle suce sun yafe min, na ɓoye saboda ina ganin kamar saboda shi ɗaya za su iya cewa basu yafe ba...ban yarda da maganar boka ba sai da akazo ana saka ranar auren Adawiyya sama da sau uku tana rushewa, Jamila ma ya zama a ranar aurenta yaron yace ya fasa, ananne na fara shiga tashin hankali saboda asirin da nayi akan Maryam kenan, asirin tozarci ba wai ya zama sam sam babu mai zuwa yace zai sota ba, a'a zata samu masu sonta kuma har ta kai ga ranar aure amma a ranar ace an fasa, wanda silar wannan baƙin cikin ya iya zama ajalinta da mahaifiyarta...shi yasa da naga hakan akan Adawiyya da Jamila nayi hanzarin komawa wurin boka amma na tarar ya mutu...ashe Amadu kai ne zaka zama na ukunsu". muryarta ta sarƙe inda ta ƙara fashewa da wani kukan. "nayi danasani, nayi nadama, Allah na tuba...tabbas Allah ba ya yafe hakkin bawa akan bawansa, Amadu a wannan gaɓar ba zan iya tozali da bayin Allah nan ba, ka nema min gafarar Maryam dan Allah, ko lamura sa samu su daidaita".
sai kawai idanunsa suka bi bayan mahaifiyarsa da kallo a sanda ta miƙe har san da ta bar ɗakin, wani ɓari na zuciyarsa na ƙara faɗa masa ba lallai sai bawa ya aikata wani laifi ba sannan ubangiji ke jarabtarsa, sau da yawa ana shirya faruwar abubuwa amma ubangiji kan juya lamarin, wanda kai bawa baka isa ka tuhumi ubangiji akan hakan ba.
yaja numfashi ya sauke, Allah ya sani yana son Maryam, amma a yanzu dole yay haƙuri da rashinta, dole ya koyi wannan haƙurin da ya gani a tare da Kabir, wanda ya jima da fahimtar cewar yana son Maryam, sai dai bai san dalilin da ya hana shi furtawa ba...kuma dalilin ganin wannan kwantaccen son a tare da Kabir ɗin, da ita kanta Maryam ɗin da bata tantance irin son da take yiwa Kabir ɗin ba, dole tasa shi hanzarin furta mata nasa son tun kafin Yayan nasa yay masa shigar sauri, saboda a lokacin ya naji kamar ba zai iya zuba ido wani ya mallaketa ba, shi yasa tun a asibiti a amsar da ta bawa mahaifiyarta lokacin data tambayeta me yasa take son Kabir ɗin yay saurin sauya ma ta tunani, dan karma wannan nazarin da yaga tanayi yay tasiri akanta, kuma shi yasa bai yi sanya ba a lokacin da ta amince masa wajen koyar da ita zazzafar soyayyarsa, ta yanda za tayi saurin mantawa da Kabir da tunaninsa, ta kuma yi mugun sabon da ba zata iya rabuwa da shi ba, duk da yasan ta amince ne ba dan tana so ba a lokacin, sai dan babu yanda za tayi, abunda kawai zuciyarsa ta faɗa masa shi ne, zai aureta ko da bata son nasa, idan yaso bayan anyi auren zaiji da wannan, shi yasan yanda zai yi ya koyar da ita sonsa, dalilin da ya sa ma kenan tana furta ta amince bai yi wata-wata ba ya zube gwiwoyinsa a ƙasa ya nemi alfarmar Baba akan asa masu ranar aure nan kusa, yasan a hakanne kaɗai zai gama da ita da dukkan wani lissafinta, shi dai ya san yana son Kabir, amma ba zai iya sadaukarwa da Kabir ke yi ba akansa.
ya miƙe jiki babu ƙwari, ya miƙa hannu ya ɗauki babbar rigarsa ya saka, sannan ya dubi su Habib muryarsa a sanyaye yace da su,"ku tashi mu tafi". ya faɗi hakan yana mai tafiya zuwa hanyar fita, tafiyar yake kamar mara laka ajikinsa, Allah kaɗai yasan me yake ji a ƙasan zuciyarsa, abubuwan da suka wakana ajiya ne kawai ke haska masa a idanuwansa, dinner ɗin jiya, da kuma yanda suka gama tsara yanda rayuwar aurensu zata kasance.
a lokacin da suka ƙarasa bakin mota yasa handky ya goge tarin ƙwallar da ya kasa riƙeta, sannan ya shiga motar Mubaraq yaja su.
yana jiyo muryar Yagana a lokacin da ta taho zuwa sashensa tana faɗin,"to Allah na tuba mene na ɗaga hankali tun da ga dalili an bayar, ai da basu bada wani dalilin nasu me ƙarfi ba ni kaina Amadu sai nace an maka rashin adalci, kuma sai inda ƙarfina ya ƙare dan wallah ko ba Kabir suka bawa ba sai na ƙwato maka matarka balle kuma sun wullata hannun wanda nasan na isa da shi...haƙuri kawai za kai Allah baka wadda ta fita, ubangiji ai da zuciya yake amfani zai kalla kyawun zuciyarka ba zai barka kai kuka ba".
*Masarautar Bichi.*
Ɗumbin jama'ar da ke yin tururuwa su na ƙara cika kowanne ɓangare na cikin masallacin fadar su suka shaida auren Kabir Adam Hashim da Maryam Mukhtar Afafa, akan sadaki naira dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba. motoci kawai kake gani daga ko'ina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa su na ƙara yawan adadinsu. Jama'a kuwa babu masaka tsinke, babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin da ya tara su agurin, manyan mutane masu faɗa aji a ƙasashenmu gasu nan wuri-wuri. Alhaji Adamu yana tsakiyar mutane yana gaisawa da ƴan'uwansa na ƙauye waɗanda aka jima ba'a haɗu ba fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, annurinsa ya kasa ɗaukewa, sam ba zai haɗa farin cikin da yake ji a wannan karan ba da na lokacin bikin Sadiya, wanda shi ne biki na farko a ƴaƴansa.
jama'arsa bata kai wani yawan adadi ba amma amsa gaisuwa yake tayi daga hannuwa kala-kala, dan kusan duk wanda yay hannu da Major to sai yay masa nuni da inda Baban yake yace su gaisa da shi, ya gabatar masu da shine u