NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 205 of 223

ni acikinku ya sake yi min wata tambayar ba, abinda Babanku yace da ni kawai shi ne kai Ahmad na sanar maka yanzu aure ba naka bane, kai kuma Kabir kayo shirin angwaye ku taho". Kabir ya ɗauke idonsa daga kan Baba Mujibu ya maida kan screen ɗin wayarsa da ke ringing yana kallon sunan Ummi da ke yawo akai. ya kai hannu ya ɗaga, ya ɗaga ne ba don komai ba sai don ta cire shi daga wannan ruɗanin da Baba Mujibu yasa su. furucin da ya fito daga bakinta zuwa kunnensa kai tsaye shi ne,"Congratulations Dear, You are now the groom of Maryam, i mean you are now Maryam's Husband". bai sani ba ko ta kashe wayar, shi dai sauke wayar yay daga kunnensa kawai ya nufi bakin ƙofa, a wuri ɗaya kawai ƙafafunsa suke so su gansu, gaban Maryam, riƙe da ita a jikinsa, ya hana wannan ruwan hawayen da yasan dole za su zuba daga idonta fitowa. _________________________________ tabbas idan banji comment ba sai na warware auren nan😎 [7/18, 14:11] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *(50)* "me ake nufi kenan?, gaba ɗaya babu abun da na gane ku fahimtar da ni". Cewar Kaka Tabawa. kuma har yanzu kan Ahmad na ƙasa bai ɗago ba, haka kuma Zulai da ke tsaye tun shigowarta bata iya samun wuri ta zauna ba. Yayarta wadda su ke uwa ɗaya mai suna Lubabatu ta rangaɗa guɗa tace,"aini Alhamdulillah, wannan abu yayi dai-dai...dama ina Amadu ina auren ƴar zina, Allah ai ba azzalumin bawansa bane, shi yasa ya sauya komai tun ba'a cuci kamilin yaro ba, idan auren ya zama dole a yau ga Hannatu nan ƴar'uwarka Allah sa muku albarka". tana yin shiru mahaifiyar Zulai Kaka Tabawa ta amshe,"to ni dai nama rasa abun cewa, amma ni ban gamsu da wancan dalilin nasu ba, meye wani ƙwayar halitta bata zo yanda akeso ba? dama can basu yi niyyar baka ƴarsu bane shiyasa, abun da suka so shi ne su ɓata maka suna su goga maka baƙin fenti, a cusa zargin wani abu a zuciyoyin mutane akanka, ga shi kuma sunyi nasara...amma banda haka sun san da zasu yi wannan binciken tun can farko me yasa ba'ai ba sai a ranar yau...ko kai acikinsu kwai wanda yace maka kaje kayi gwajin ƙwayalar halittar taka?". nan ma Ahmad ɗin shiru yay bai ce komai ba, sai da ta ɗaga masa murya tukunna,"Amadu bafa da kujerar nan nake magana ba, ka bani amsar tambayata". ya ɗago da jajayen idanuwansa ya dubeta yace,"ko kusa babu wanda ya tunkareni da wannan batun, abu guda ɗaya ne yake nan, kawai dai na gamsu da hujjarsu. sai dai mene yasa za su bawa Kabir ita? hakan shi ne adalci? mafita ce za'a samar ta hakan? me yasa basu bawa Jawad ita ba? wannan ai cin fuska ne, nayi soyayya da ita sannan shima yazo ya aure ta?". a zafafe yake maganar kuma cikin ɗacin rai da zafin kishi. Zulai ta numfasa sannan ta dubi ɗanta cike da tausayawa, murya a matuƙar sanyaye tace,"Amadu da ilminka, dan haka ka tsayar da tunaninka da iliminka a wuri guda ka auna, idan da Allah ya rubuta Maryama matarka ce Amadu ba ƙwayar cutar halitta ba, ko menene babu abunda zai hana fasuwar aurenka da ita...Matar mutum ƙabarinsa, ka ɗauki hakan a matsayin ƙaddararka, sai ka roƙe shi ya sauya maka da mafi alkhairinta, baka san wane tanadi Allah yay maka a gaba ba...ni mahaifiyarka ce, a kullum adu'ata akanku Allah ya haɗaku da abunda yake alkhairi agareku, ya kuma nisanta tsakaninku da abun da yake ba alkhairi bane agareku...damuwa ko ɗaga hankali ba su zasu baka Maryam ba, basu zasu dawo maka da Maryam ba ta ƙarfi da yaji, ka zama mai haƙuri da tawakkali sune suturarka". ji yake kamar yay kuka a wannan lokacin,"to amma Inna saboda rashin dacewa sai a ɗauki yarinyar da ansan nayi soyayya da ita kuma a aurawa Yayana, mene hikimar yin hakan? ba'a tunanin yanda zan dinga feeling a zuciyata idan ina ganinsu tare, me yasa ma Baba zai yarda da hakan, ba sai ya ƙyalesu su maye gurbina da wani can daban ba". "ni dai na faɗa maka Amadu, idan baka ɗauki maganata ba zugar zuciya zata kaika ta baro ka...Umarni ɗaya zan baka shi ne kar naji kar na gani, ka miƙe ka tashi ka tafi wurin ɗaurin auren Yayanka kamar yanda mahaifinka ya umarceka, kar ka taɓa bari huɗubar shaiɗan tayi tasiri a zuciyarka ta ɓata kyakykyawar alaƙar da ke tsakaninka da ɗan'uwanka, jini yafi ruwa kauri dan haka mace karta zama silar rusa tsakaninku, ka gane me nake nufi, idan har ka ƙetare gaskiya da shawarar da na ke faɗa maka kuma, danasani ce zata zo bayan aikata ba dai-dai ba, kuma wata ƙila anan ubangiji ya nuna min ishara ne". sai kawai ta fashe da kuka, kuka irin me ban tausayin nan, tasa hannu ta rufe fuskarta, inda hankalin Ahmad ya ƙara tashi, ya baro kujerarsa yazo ya kamata ya zaunar da ita, cikin muryar kuka taci gaba da cewa,"a baya na yiwa Maryam asirin kan ba zata taɓa aure ba, yarinyar nan baiwar Allah bata tare min komai ba amma ni da ƴaƴana muka sa mata ƙahon zuƙar hassadarmu...a ƙarshe saboda tasirin adu'oin tsarin da takewa kanta da wanda Suwaiba da Akila suka dage kan yi mata shi ya karya asirin, boka ya tabbatar min da karyewar asirin dole sai ya taɓa ƴaƴana uku, kuma bayan na tuba na ne
🏠