awar wani abu a zuciyata ya kuma wucewa, sai na karkato kaɗan na kai dubana ga wayata ina duban agogo, lokaci bai ba, lokacin da akasa na ɗaurin auren bai cika ba, ɗaurin auren ƙarfe goma da rabi ne amma me ya dawo da shi ƙarfe tara da arba'in?. a yanzu da na gama kallon lokacin ba shi lokacin nake jiran gama lissafawa ba, ƙwayar idona na kai ne da jiran shigowar kiran Yaya.
"Maryam an ɗaura". na jiyo muryar Shamsiyya na cewa da ni. na juyo na dubeta daga inda ta ke tsaye jikinta a sanyaye. ni da ita duk sai muka tsaya kallon juna, muka kasa yiwa juna magana, kowannenmu idonsa da gangar jikinsa na bayyanar da fargaba da ke ɗauke da ita, sai ita ce naga tasa hannu ta goge ƙwallar da ke shirin sakko mata, kafin ta ƙaraso ta rungumeni tana fashewa da kuka.
muryata na shaking nace,"kukan na menene?". "ina tayaki murna". "wai da gaske an ɗaura?". ta ɗaga min kai alaman ehh kafin kuma nace,"amma...". nayi saurin tureta daga jikina nace,"amma me?". "naji Ummi na cewa bada Ya...". ban bari ta ƙarasa faɗin abin da take son cewa ba na tureta daga jikina a zafafe, na diro a saman gadon ina damƙe kafaɗunta, na shiga girgizata da ƙarfi ba tare da bakina ya iya furta wata kalma ba. shigowar Mamina ɗakin na sami amsar tambayata da na gagara yiwa Shamsiyya, abu ɗaya na sani shi ne, naji san da Mami tace,"ina Jawad ɗin?". amma bayan nan ban kuma sanin komai ba da kuma inda kaina ya tafi.
*09:40.*
a parlon ɗakin Ahmad ne da abokansa ana ta shirin tafiya wurin ɗaurin aure.
ango wanda tuni ya shirya yana kar ya hularsa yake cewa da Mubaraq,"ko ka shirya ko kuma wallah muka gama muyi tafiyarmu". "kai dai angon zumuɗi ci gaba da shirinka kawai. ni ka ganni lokaci nayi miƙewa zanyi na bula Babbar rigata". Habib yace da Ahmad,"duk kabi ka ishi mutane bayan da sauran lokaci". bai tanka masu ba ya nemi wuri ya zauna tare da ɗaukan wayarsa, inda yaci karo da message ɗin Maryam wanda ya shigo tun ƙarfe shida, sam bai lura da saƙon ba sai yanzu, kuma kalaman da ke ƙunshe acikin saƙon shi ya saukar da wani annuri da murmushi mai ƙarfin sauti lokaci ɗaya a saman fuskarsa, a lokaci ɗayan da ya fito ɗin sai ya ɗauke sakamakon furucin da ya ji ta bayansa da muryar Baba Mujibu.
maganar da tasa shi hanzarin miƙewa ya juyo gare shi yana kallonsa da kyau, da irin tsananin tashin hankali da ruɗanin da ba zai musalta shi ba, haka zalika idan ya kira yanayin da yake ciki yanzu da tashin hankali kaɗai to ya yaudari kansa.
ya sani Baba Mujibu uba yake a gare shi, kuma Baba Mujiba ba sa'ansa ba ne, kuma ba sa'an wasansa bane, hasalima basa wasa da shi, dan ba haka babu ta yanda za'ai ya kira wannan furucin nasa da zancen wasa, balle ya kira yanayin fuskarsa da wasa.
"Ahmad an ɗaura auren Maryam amma ba da kai ba, sakamakon genotype ɗinka da mahaifinta yaƙi yarda da shi". maganar ta shiga kunnensa tarr kuma ya fahimci me Baba Mijibun ke cewa, amma kafin a warware masa komai abun da yake so ya sani dawa aka ɗaura auren?
"Jawad". yaji kiran sunan ya fito daga bakin Kabir da ke zaune kan kujera, amma sai dai sunan bai fito da amsar tambayar da yaywa kansa ba, shi magana yake yi a waya, kuma da alama da Jawad ɗin yake wayar.
sai ya maida kallonsa ga Baba Mujibu yace da shi,"Baba babu mahaluƙin da ya isa ya hanani auren Maryam, babu shi. tabbas ko dawa aka ɗaura sai ya warware shi yanzun nan...batun irin Ƴaƴan da zamu haifa babu ruwan kowa da wannan". sai ya zube akan kujera yana dafe kansa. "genotype". wannan kalmar da ta haɗu da furucin Baba Mujibu ita ta haska akansa, me yasa tuntuni ba'ai zancen genotype ɗin ba sai a yanzu, sai da akazo kan gaɓar da ba'a isa ai masa abinda ake ganin mafita ce aka samu ba, abinda akasan ba zai ɗauka ba. abunda ya sani kawai bai san genotype ɗinsa ba, ya san dai lokacin da suka je seminer ibadan shi da Md da Almustapha dukansu anyi musu genotype, sai dai bai san sakamakon da result ɗin ya bayar ba kasancewar a jirgi akace zaa sako a biyo su da shi, kuma yasan Almustapha yace masa result ɗinka yazo hannuna amma bai ba shi ba, to shin menene genotype ɗin nasa kenan?
"SS kai carrier ne Amadu". maganar ta fito daga bakin Baba Mujibu kamar yasan tambayar da ke ransa kenan, kafin yaji Baba Mujibun yaci gaba da cewa,"wannan dalilin yasa mahaifinta yace ba zai iya baka ƴarsa ba domin ƴaƴan da za ku haifa duka zasu zama carriers. shi kuma bai san yanda ƙaddara ta ke ba amma ba zai so a jininsa a sami wani kuskure irin hakan ba, familynsu ba a aure sai result ya zamana cikin biyun ɗaya, imma AA da AA, imma kuma AA da AS. wannan dalilin ne yasa aka maye gurbinka da ɗan'uwanka Kabir kasancewar shi da ita genotype ɗinsu ɗaya ne AA+AA". ba shi kaɗai ba, hatta Kabir ɗin da bai san meke faruwa ba kawai yaji saukar maganar ne a yanzu, duka su biyun suka miƙe a zabure.
"Kabir". Ahmad ɗin ya tambayi Baba Mujibun da tsantsar mamakin da ke haskawa a fuskarsa. "Ni kuma Baba?". shima Kabir ɗin ya sake tambaya da mamaki. "ƙwarai da kai aka ɗaura...kuma bance wa