duk da bata san da wanne su na zata kira kayan ba, ta san ba les bane kuma ba material bane, doguwar riga ce ita ma kuma kamar ba ɗinkata akayi ba, ta san dai tana ganinta a jikin turawa a tv.
kawai sai ta tsayar da tunanin da ke neman shiga kanta ta natsu akan maganar da yay mata da ya shigo, maganar da sai da ta gama shawagi a iska sannan ta shigo kunnenta da girgiza ƙafafuwanta kaman zata faɗi sai kuma maganar amsar da zata bayar ta riƙe ƙafafun nata.
"Nawwara idan naje gidanku nemawa wani aurenki a yanzu Babanki zai bayar? zai iya damƙa min aurenki Nawwara? ko kuma dole sai mun tura wanda yake uba agaremu tukunna?". kaman matsar bakinta yay a lokacin ta bashi amsarsa kai tsaye hawaye na biyo kuncinta. "Ya Kabir ai tuntuni Baba ya bada ni, ba wannan Baban da yake riƙona ba. Babana kafin ya mutu, kuma ita ma Mama kafin ta rasu ta ƙara shaidawa wannan Umman da ke riƙona sun bada ni". zata iya rantsewa taga ƙyallin wata wuta a cikin ƙwayar idonsa a lokacin da ya kalleta, kafin ya jefa mata tambayar,"banbance min Baban yanzu da wancan Baban, da kuma Umma da Mama". a lokacin hannu tasa ta goge hawayen fuskarta da gudunsa ya ƙara yawa, sannan tace da shi,"iyayena sun rasu, inda nake zaune Ƙanwar Mamana ce ke riƙona". a lokacin da yake kallonta taga tsananin tausayinta acikin ƙwayar idonsa ya haska, kuma shirunta yay daidai da saka hannunsa ya goge ma ta hawayen, sannan ya buɗi baki yay maganar da zata ce da ƙyar ta iya jinta. "waye su ka ba ki?". "wani ne Kabiru". "ai na yake?". "nima ban sa ni ba, ban ma san shi ba. Baba dai yace min sai na shekara 18 tukunna za su neme shi, hakan Babana ya bada wasiyya".
zata iya cewa wannan furucin nata shi ne silar wannan muguwar damƙar da yay mata, dan shirunta ya haɗe ne da matse hannunta cikin nasa sosai, sannan ya janyota suka ƙarasa bakin kujera, shi ya zauna akan kujerar ita kuma ta duƙa a gabansa. kuma ayanzu in zata iya lissafi sama da wucewar minti ashirin kenan idonsa a rufe yake, haka wayarsa da ke kan ƙafarsa tayi ringingin yafi sau goma bai ɗauka ba.
har tsawon wucewar yawan wasu daƙiƙu tukunna ta fara jin hannunsa ya saki daga riƙon nata, ta leƙa fuskarsa kamar yayi bacci ne, saboda haka ta zame hannun a hankali sannan ta fice daga ɗakin da sauri, burinta kawai ta isa ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, har ta wanke wannan kwalliyar ta cire kayan ta maida nata ta dawo asalin Nawwaranta ƴar ƙauye.
sannan ta samu wuri ta zauna ta hana ƙafafunta da hannunta rawa, tukunna ta sai ta kanta ga natsuwarta, bayan nan sai ta tashi ta hau aikin gida kafin a dawo daga wurin partyn.
*washe gari, ƙarfe tara da rabi na safe, cikin masarautar bichi, turakar Sarauniya Hauwa'u.*
Net ɗin da ke jikina wani farin net ne da ya ji adon flowers pich clour ajiki, doguwar riga ce irin tamu ta larabawa da suke sawa ranar biki, an yafa min wani farin mayafi irin namu daga saman kaina, shi ma kamar rigar adon jikinsa da pich colour. bangles da zoben da ke hannuna suma farare ne hakama yari da sarƙar. kwalliyar yau ta ɗauki fuskata fiye da ta jiya, sai dai yau ɗin fuskata fayau ta ke.
tun da na farka yau sam bana son yin magana, dan idan nayi maganar muryar na fita ne kaman nayi kuka, tunda na wayi garin yau na tuna cewa yau ɗinne za'a ɗaura aurena shikenan wani kuka ya shimfiɗe a zuciyata, jikina duk yay sanyi na zama kamar mara lapia. ina zaune ne akan ƙasaitaccen gadon Ammi gefen haguna da damana an saka tum-tum kamar wata basarakiya, du ka Ammi ce tayi min wannan shirin, sai bayan ta gama shiryani ne Hajjah Nashwa ta shigo tayi min feshi da wani turare da ban taɓa jin ƙamshinsa ba, zan iya cewa dai naji irin yanayin ƙamshinsa a jikin mutum guda, wannan ƙwayan mutum ɗin da na cire shi a lissafin rayuwata.
na rasa faɗuwar gaban na menene duk da Shamsiyya Sani ta faɗa min haka amare ke tsintar kansu a wannan rana da ta ke me albarka da muhimmanci a wurinsu...amma ni nawa sai nake ganin kaman mummunan abu ne zai faru, ina zaune ne kawai dan babu yanda na iya, domin Hajjah Nashwa tace kar na motsa a wurin har sai an ɗaura aure tukunna, idan ango ya shigo shi ne za'a zo a fito da ni. a yanzu da nake zaune muryar Yaya kawai nake sonji, so nake na kira shi ko sunana ne ya ambata wannan taraddadin da ke liƙe da ni ya samu ya barni.
na kulle idona sakamakon wani abu da naji ya daki allon ƙirjina ya girgiza a lokaci ɗaya, nayi saurin saka hannu na dafe ƙirjina ina jin wani irin baƙon yanayi a tare dani, irin yanayin da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba. daga waje na jiyo tashin algaitu da busar sarewa na tashi, sai na ƙurawa ƙofar shigowa ido kaman ina jiran shigowar wani, ɗora idon nawa akai yay daidai da shigowar Jakadiyar Ammi tana cewa,"Alhamdulillahi, Allah kasa albarka". sai naga ta zube a gabana tana ci gaba da faɗin,"gaisheki ranki ya daɗe, a yau kuma daidai wannan lokaci kin shiga cikin sahun matan nan masu girma da darajara, martabarki ta ɗaga sama, Allah ya sanya alkhairi, ina tayaki murna". kawai sai naji harb