an ta sauya taken waƙar da ke tashi zuwa wata waƙar me taken 'Baby i Love You' ta Tiffany Alvord, waƙar da ta ƙara tashi da wurin, masoyan biyu suka ƙara shiga shauƙi, Ahmad yasa hannu a weast ɗinta ya janyota jikinsa suka shiga rawa a hankali. a wannan lokacinne Daddy da Mami suka fito su na yi musu liƙi, Dad na watsa musu Doller Mami na watsa masu Qatari Riyal, kafin nan ma Ummi ta shigo cikin mutuwar jiki ta shiga watsa nata kuɗin ita ma, nan da nan kuma hasken camera ya fara shigarsu sound ɗin ƙyas ƙyas kawai kake ji na tashi. duk abin da Akila keyi tana yinsa ne kawai a cikin rashin kuzari, tunda aka shigo wurin nan idanuwanta na kan taga ta ina Kabir zai ɓullo, kuma tana ta kiran wayarsa amma bai ɗaga ba, tasan dai yanzu aka fara dinner amma tana ganin kmar har a gama ba lallai ne yazo ba kaman yanda ya tabbatar ma ta da zai zo ɗin.
*10:00am*
*a wannan dare wannan lokaci da kowa ke wurin dinner.*
ƴan tsirarrun mutanene su kai saura a gidan, hakan yasa hayaniyar gidan ta ragu sosai ba kaman a ɗazu ba kamin su fita. ba su dawo gidan ba sai bayan magrib, zaune take a gabansa a yayinda shi kuma ke kan kujera, hannunsa riƙe yake da nata yay masa wata iriyar matsa, zafin da ke ratsata har cikin kanta, kuma duk yanda ta kai ga mutsu-mutsu dan zare hannun yaƙi bata dama.
ba sau ɗaya ba ko sau biyu ta faɗa masa,"Ya Kabir riƙon da zafi". amma sam bai ma nuna ya jita ba, sai dai a yanda ta lura so yake ya sauke zafin takaicin wani abu da yake ji a wannan riƙon, hakan yasa ta haƙura kawai tana jiran har san da zai buɗe idanuwansa ya sauke akanta sannan ya fahimci irin nata zafin da taji da yay mata wannan riƙon nasa, tukunna cikin tsawa ya umarceta da ta tashi ta bar masa ɗaki. a tsorace ta ke da shi sosai tun da suka dawo, koma tace tun da suka taho, dan lokacin da ya je ɗaukota ba haka yake ba, tana iya tunawa sun yi waya shi da Ya Ahmad lafiya, yake masa zancen ya shigo kano ne amma yanzu zai dawo sai ya ƙaraso wurin dinner ɗin, kuma bayan gama wayar tasu ya kalleta da wannan ƙwayar idon tasa da wani yanayi da ta kasa fassarawa, yace da ita,"na ga gyaran gashin". tana iyawa tunawa da yanda tasa hannunta akanta ta zame ɗankwalin duka, tana iya hango yanda ƙwayar idonsa ke kallon gashin da ya sha gyara tarr babu ko ƙifce, a lokacin abin da yace mata shi ne,"Nawwara zan iya taɓawa?". kuma kanta kawai tasan ta gyaɗa masa amma sai ya girgiza nasa yace,"ba yanzu ba". sannan ya umarceta da ta mayar da ɗan kwali kafin nan yace ta nuna masa ƙunshin, ananne bai iya hana kansa ba sai da ya kamo hannun ya shafa sannan ya faɗa mata irin kyan da yay, har yace "amma jan yafi kyau, sai ya ƙara fito da kyawun siraran yatsunki". a wannan lokacin inda zata danganta yanayin da take ciki da kalmar ruɗani, to tabbas ita kanta tasan da ta yiwa kalmar rashin adalci, shi yasa ko kusa bata alaƙanta shi da hakan ba, laɓɓan bakinta dai sun furta masa kalmar,"na gode, na gode sose da kulawanka Ya Kabir, Allah ya biyaka da mafificin alkhairi". kuma har furucin da tayi ya haɗe da wani furucin da bata san sanda ta faɗe shi ba. "Ya Kabir dan Allah nima zanje wurin partyn". tana kallon san da ya gyaɗa kansa har sau biyu a lokacin, kafin ya buɗe baki yace da ita,"Za ki je". ya sauke numfashi ya ƙara da cewa,"sun iya gyaran jiki, kin ƙara haske kin ƙara kyau, ƙamshinki duk ya cika motar". daga wannan maganar kuma har suka dawo gida wata maganar bata ƙara haɗasu ba. sai ma da suka dawo ne ya sata a gaba taci abinci, sannan ya fita ya barta a ɗakin kamar ɗazu da safe yace tayi wanka ta shirya cikin kayan da ya bata a kwali, sai bayan tasa kayanne wannan matar da ya kira tayi mata kwalliya tayi ma ta ta tafi, kwalliyar da bata san ta mecece ba, haka abubuwa da ke ta wakana ta rasa da wanne irin tunani zata masa kuma ta rasa da me zata kira shi. abu ɗaya ta sa ni tunda aka gama kwalliyar ta kalli kanta a madubi, taga ta fita daga siffar waccan Nawwaran ta zama wata Nawwaran ta daban, shikenan tayi azamar miƙewa daga kan kujerar da take zaune a gaban madubi, ta sandare a tsaye, irin sandarewa da duk wanda ya shigo ya ganta a wannan tsayuwar kawai zai hankaɗata ne ta ƙarasa faɗuwa, sannan idan gawar tata ta cancanci ai mata kuka ya kurma ihu mutane su shigo ya sanar musu ta mutu.
tunanin ya bar kanta lokacin da Kabir ya shigo ɗakin ya ƙaraso gabanta sosai ya tsaya ya kamo hannunta a nasa, ta san wani tunanin ta tafi amma bata san ko tunanin mene ba, hakan yasa hatta riƙon da yay mata da tsayuwarsa bata san da su ba. maganarsa kawai taji, wannan furucin da ya haifarwa zuciyarta yin rawa hatta da gangar jikinta, kuma lokaci ɗaya komai na cikin kanta ya ɗauke, ta ɗauke ƙwayar idonta daga kallonsa ta tsaida su akansa, ba kallo ɗaya kawai tayi masa ba, sai da ta buɗe ido ta rufe sau uku tukunna ta gama shaida kayan da ke jikinsa.
Shadda ce arniya ƴar ubanta aqua colour, taji wani azababban ɗinki da zai sa mai kallonsa kusan zaucewa, kalar shaddar kalar kayan da ke jikinta ne,