oji da ƴan jarida zagaye da wurin, da yawa nada ga cikin hall ɗin zaune yayinda wasu kuma yanzu ne motocinsu ke parking wanda yawancinsu dangin amarya ne, alagaitar da ake busawa na shaida bikin na masu sarauta ne.
a wannan lokacinne jiniya ta ƙaraɗe ko'ina, a cikin wurin har daga can waje kan titi sakamakon motar Mahaifin amarya da ke shigowa. a yayin da motar amarya ke shigowa daga baya, Major ya fito daga cikin motar cikin dakakkiyar shaddar magic milk colour me cijawa, sannan matarsa Aaliya ma ta fito cikin wani haɗaɗɗan less ɗinta ita ma milk colour, ta zagayo inda mijinta yake suka jera suka nufa cikin hall ɗin sojoji uku na take masu baya. sai bayan shigarsu sannan Almustapha, Imam, Joseph da Alhassan wato yayyan amarya su ma suka fito cikin shaddarsu irinta mahaifinsu da su kai anko gaba ɗayansu, suma sannu a hankali suka rankaya zuwa cikin hall ɗin.
[7/18, 12:30] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*_Happy Marriage Life Maryam Mukhtar Afafa._*
*(49)*
a motar amarya da ango kuwa a kallo ɗaya za kaiwa jigwayen taron zaka san lallai ranar aure ta musamman ce ga kowa. shigar shadda ɗabi'ar Ahmad ce tun kan su zama wasu, kuma ƙoƙarinsa ne ɗinka babbar riga a duk lokacin da wani biki na abokinsa ya kama, amma a yau yanda kayan suka amshe shi yafi na kullum. daga kallo ɗaya zaka gane cewa kuɗaɗe masu nauyi aka zuba wajen ɗinkin da ke jikinsa, duba da ɗinkin ma bai yi kama da namu na ƙasar nigeria ba. askin kansa sai walƙiya da sheƙi yake ta ƙasan hular da ke kafe a kansa, fuskarsa sai washewa take da murmushi, Hakan ya saka kyawunsa ƙara fito da ɓoyayyan kyansa.
Amarya Maryam tayi bala'in kyau da haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. net less ɗin da ke jikinta kalar shaddar angon nata ash, an ƙawata ɗinkinsa da wasu flowers da suka ƙara fito da kyan ɗinkin, sarƙa da ɗan ƙunnenta silver colour masu shegen tsada, haka pos da takalmin dake ƙafarta duk silver, lamarin dai ba'a cewa komai, dan tun lokacin da aka shirya Maryam ita da kanta tasan ta haɗu, sai dai bata san me yasa a wannan lokacin ba zuciyarta ke a raunane, zuciyarta da ruhinta na faɗa mata kamar wani abu zai gifta wanda ba lallai ta iya ɗaukarsa ba, sai Shamsiyya ce me ƙarfafa ma ta gwiwarta da ada ta mutu tun dirarsu a bichi da su kai ido huɗu da Jawad yay mata wannan murmushin nasa da ƙarya ne tace bai da kyau.
suka haɗa ido ita da angon nata suka sakarma junansu ƙayataccen murmushi sannan Ahmad ya fito ya zagayo zuwa tata ƙofar, ya miƙa ma ta hannu ta riƙe shi ta fito daga motar, A haka suka shiga cikin hall ɗin da ya gaji da haɗuwa, anyi decoration ɗin wajen da silver colour, komai na wurin silver ne da kwalliyar ash ajiki, kuma komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, haske ta ko'ina tamkar rana, fitilu sai walwali suke su na ƙara ɗaukan ido da hankali, Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. dan ɓangaren dangin mahaifinta daban kasancewar su christians, kanta na ƙasa tana kallon wasu wuraren ta wutsiyar ido, zuciyarta da fuskarta na washewa da tarin farin cikin da ba zata iya musaltawa ba. wannan waƙar da ke tashi a hankali na bin jijiyoyin jikinta su na motsata, har ta ƙara tsamke yatsunsu da ke cikin na juna. abokan ango da ƙawayen amarya ne suka masu rakiya har mazauninsu inda ya dace kuma aka tanada domin su. bayan daidaituwar zamansu MC ya bada umarnin ai welcoming nasu nan wuri ya ɗauka da tafi rau-rau, daga nan kuma Bella ta fito cikin takun ƙasaita zuwa waje na musamman da aka aje royal chair saboda ita ta zauna ta shiga kwaroro adu'a, daga bisani kuma Granny Chioma wadda ta ke ƙanwar Granny ta fito tazo ita ma tayi kalar tasu adu'ar ta kiristan sannan ta koma ta zauna.
Shamsiyya Sani ita ta fito ta bada biography na amarya, tun da ta fara gaban Maryam ɗin ke faɗuwa dan sai take ganin kamar zata fito fili ta daɗa faɗawa duniya ita shegiya ce, sai dai har Shamsiyya ta gama wannan bayanin bata ji makamncin maganar hakan ba, da zamanta kuma Habib da yake aminin ango shi ma yazo yay biograph na ango. Ummi(Akila) ita ma tazo ta bayyanawa irin jin daɗi da farin cikin da take ciki da kuma muhimmancin wannan rana a gareta. sai bayan ta koma ta zauna ne sannan MC ya umarci amarya da ango su yanka cake ɗin da aka aje akan wani table, dan rashin kunya ko da Ahmad ya yanko cake ɗin a bakinsa yasa shi sannan ya nufi bakin Maryam ɗin da shi, kunya ta hanata karɓa ayayin da ihu ya karaɗe wurin aka ɗauki tafi, sai da ƙyar ta iya buɗe baki ta amsa sannan ita ma ta ciro nata ta miƙa masa, sai dai maimakon tasa masa a baki kamar yanda ya buɗe sai ta shafe masa icing ɗin a kumatukansa gefe da gefe da kuma kan hancinsa, nan ma ihu ya kuma karaɗe wurin, ta miƙa hannu ta ranƙwafo da fuskarsa ta haɗe goshinsu da hancinsu, kamar MC Rahineena ta san me zata yi ta ƙaraso ta sai ta speaker nan muryar Maryam ɗin ta fito a hankali cikin wani amon sauti me motsa zuciyar ɗa namiji tace,"i love you".
aiko nan ta ke aka ƙara sakin ihu ana tafi, MC ma tayi ihu tayi ihu sann