dan ƙafafunta yawo suke acikin zani duk san da tasa kaya, kaman yanda hannunta yake yawo acikin duk hannun rigar da tasa, tsayinta kuma gaba ɗaya a ƙasan ƙirjina yake saman cikina kenan. amma kar ka yi awon daidai da yanda ƙaƙafunta da hannunta zasu yi yawo a kayan, kayi daidai da yanda kayan zasu zauna ajikinta". abin da yake ce mata kenan lokacin da suka ƙaraso bakin dining ɗin, yace taja kujera ta zauna sannan ta zuba musu abincin. ta zuba abincin amma ta kasa ci sai tunanin maganar awon ɗinkin ta ke acikin kanta. "na bada awon dai-dai ko?". taji ya tambaya lokacin da ya kai spoon bakinsa, sai ta ɗago kanta a yanzu ta kalle shi sau ɗaya sannan ta maida kanta ƙasa. "ba ki ban amsa ba". "Ya Kabir amsar me?". "surutun da na gama yi miki a yanzu indai bai bi iska ba to akansa nake magana, in kuma yabi iska kici abincinki kawai". haka kawai maganar tasa yasa murmushi suɓucewa a fuskarta kafin tace da shi. "Ya Kabir to ai ban san wace siririyar ba". sai kawai taga shima yay murmushi yace,"ki ƙaddara a matsayin kece, kuma a cikin ɗinkin awon yanda aka bada". bata san lokacin da ta fara cin abinci ba tun daga lokacin nan da ya ce in maganarsa bata bi ta iska ba, dan haka a yanzu da ta haɗiye abincin da ke bakinta cikin jin kunya sai tace da shi,"ehh yayi daidai amma ni nafi waccan tsayi". so yake ta sake taci abincin dalilin da ya sa yake janta da zancen kenan. dan haka ya ƙara cewa,"kenan idan naki ne anyi kuskuren ba da awon kenan?, in aka kawo maki tsayinsu za su yi maki kaɗan?". kawai sai yaji tace,"aini Ya Kabir na taddoka a kafaɗa ita kuma kaga a cikinka kace". ya gyaɗa kansa har sau biyu san da ya kai kofin lemu bakinsa, bai sake cewa da ita komai ba sai da ya lura ta gama cin abincin tukunna ya miƙe yace ta tashi. "zan kwashe kwanukan...". wani kallo da yay mata shi ya dakatar da sauran furucinta, hakan yasa ta tura kujerar baya ta isko zuwa inda yake ta tsaya, kuma tsayuwarta kenan taji ya janyota ta tsaya ajikinsa. "banbance min wannan tsayuwar da maganarki ta ɗazu". a hankali ta buɗe idonta da ke rumtse, kafin ta kelleta gaba ɗayanta akan cikinsa. kuma maganarsa sai ta katse tunaninta jin yana cewa,"kin ƙara faɗa min kin kerewa kafaɗata ko sai na kai ki asibitin wanke ido". "na kere maka". ta faɗa a sanyaye tana murmushi, shi kuma yana sakinta a hankali ta bar jikin nasa, kafin yayi gaba ya barta a baya, san da ta ƙaraso bakin motar tasa har ta buɗe zata shiga baya cikin ɗagin murya yace da ita,"drivernki ne ni?". da sauri ta maida murfin motar ta rufe ta dawo gaba ta shiga, ta tsorata sosai da shi ɗin da yanda yay mata maganar, dan bata mantawa da kwanaki can kafin Yaya Maryam ta bar gidan ta taɓa yi masa irin hakan, kuma ƙiris ya rage ya kaiwa fuskarta mari tayi saurin kauce ma sa, shi yasa ko a yanzu da yace ma ta shi drivernta ne ta fuskanci me yake nufi.
da gudu yaja motar ya bar harabar gidan, mai gadi ya buɗe masa gate, ko gaisawa bai tsaya yi da mai gadin ba kamar yanda suka saba da shi a duk lokacin fitarsa, tun da ya hau titi magana bata shiga tsakaninsa da ita ba har suka baro bichi ya shigo kano, kuma har zuwa san da yay parking motar tasa a bakin *S. FARI BEAUTY PALACE, COURT ROAD*.
maganar da zata iya tunawa kawai ta shiga tsakaninsu awa ɗaya da suka ɗauka su na tafiya akan titi yace da ita,"kina jin yunwa?". kuma a wannan lokacin da yay tambayar girgiza masa kai kawai tayi alaman a'a, bai ɗauki a'a ɗin tata a yarda ba sai da ya tsaya a wani restaurant yay takeaway tukunna suka ci gaba da tafiya.
a yanzu da suke bakin wurin da ta lura wajen gyaran gashi da jiki da ƙunshi ne, waya taga ya ɗauko ya kira wata lamba kuma babu jimawa wata bayerabiyar budurwa ta fito, bata san maganar da su kai da ita ba tunda cikin harshen turanci ne, kafin budurwar ta juya ta koma ciki shi kuma ya juyo gareta yace da ita. "idan an gama ki kirani da wannan wayar". ya faɗa yana miƙa mata ƙaramar wayar da ke hannunsa, ta ɗago ido ta kalle shi kafin tasa hannu biyu ta amsa. sannan ya ƙara miƙo mata card ɗin da taji Ya Maryam na kiransa da ATM ya bata yace,"6915". sai da ya maimaita mata lambobin sau biyu kan ya ɗora mata da cewar,"lambobin sirrin banki ne. idan kika bari wani ya gani za ki ja a yasheni gaba ɗaya, kuma aka yasheni ke aka yashe".
"a dawo lafiya". shi ne furucin da tayi tasa ƙafa ta fita daga motar, ta rufo ƙofar taji ya kira sunanta,"Nawwara". hakan yasa ta dakata daga tafiyar ta leƙo ta glass ɗin tana amsawa,"na'am Ya Kabir". "ayi miki mai kyau, haka za ki ce da su, na faɗawa incharge ɗin wurin amma ki ƙara faɗa musu". tace,"to Ya Kabir, na gode". ta faɗa tana juyawa ta nufi inda ƙofar shagon ta ke, bai bar wurin ba sai da ya tabbatar da shigarta wurin har ya ƙara kiran matar ya tambayeta ta shigo tace masa ehh sannan ya baɗe wurin da ƙura.
*8:30pm.*
*more event center.*
daga irin yanda kake ganin zuƙa-zuƙan motocin da ke cike da harabar events ɗin har zuwa waje zaka san ehh fa lallai bikin na manya ne masu lokacinsu. soj