jefa ƙasan gado, ina tsaye na haɗe rai ta shigo banko dubi inda take ba, balle na amsa mata maganganun da take, kallona take tana ƴar iskar dariyar nan tata me ƙularwa, na juyo a fusace zan kai mata duka ta kauce.
"ya isheki Adawiyya idan ba haka ba zan gurza miki rashin mutunci, sanin kanki ne hankali ba gama ratsani yay ba walla saina ɗauka wannan langar na rantama miki a tsakiyar ka ki koma sahun su Kulu kema". Ta tsagaita dariyarta tana cewa, "Ke nifa banga dalilin da zai sa ki dinga hanani dariya ba, ai bance dake nake ba". Nayi ƙwafa na girgiza kai tare da cewar,"karki fasa kici gaba".
Dariyar ta daina tana faɗin,"yasin tawa tafi taki kyau". Sai yanzu da tayi maganar ma na lura da kayan dake jikinta, doguwar rigace irin tawa amma tata ja da baƙi kuma kwalliyar tawa tafi tata, rigarma dai gaba ɗaya tafi dai-dai da jikina dan ita ta kamata, kuma tsayin yayi mata yawa, ni kuwa daga tsayin har faɗin rigar dai-dai dani, na ƙare mata kallo na kwaɓe baki nace,"arziƙina dai kika ci aka raɓa dake a siyan, kuma wallahi ƙarya kike tawa tafi taki kyau". Sallamar Ya Kabiru a ƙofar ɗakin na bar inda nake da sauri na tafi naje na rungume shi, adu'a nake jera masa tare da sanya masa albarka, ya ɗago kaina daga jikinsa yana kallona, sai dai har yanzu hannuna na kewaye da shi, na ɗan doki ƙafa a ƙasa da cewa,"Ya Kabiru wannan kallon fa kamar yaune ka fara ganina". Acikin sigar zolaya yace,"dama ni na taɓa ganinki ne banda yanzu, wace ke?". Na shagwaɓe ina narkewa jikinsa sai dukan ƙafafu nake a ƙasa nace, "Ya Kabiru ni ce fa". Da kwaikwayon maganata yace, "ke wa?". "ni Mairo". Ya buɗe baki yana riƙe da haɓa yace,"Yaushe Mairon tawa ta zama balarabiya?". Murmushi kawai nayi sannan na ɗago daga jikinsa ina riƙe da hannunsa nace,"Ya Kabiru kuma Allah daga yau karka kuma saya mana abu tare da Adawiyya, tun ɗazun tazo tasani agaba tana min dariya wai tata tafi kyau".
Sai da ya dubi Adawiyya kana yace,"yo dama ita kalar ƙauye ina tasan kyau, baki kalla kayan ko amsarta ba suyi ba ta koma kamar dodo". Na tuntsure da dariya ina mata gwalo, haushi ya cikata zata bar ɗakin ya janyota jikinsa yana cewa,"aike kika fara tsokanarta".
Bai bar Adawiyya ta fita ba sai da ya sata dariya kana, ni kuwa har da zungurinta ina ƙara yi mata gwalo, tabbacin ta shaƙa yasa na ƙara da ce mata me wargajejen baki. Duk nauyin da Gwaggo ke cewa ina da shi Ya Kabiru baiji shi ba ya ɗorani saman ƙafarsa guda, ina wasa da gashin sajensa nace,
"Ya Kabiru baka taɓa saya min kaya masu tsananin kyau da tsadar waɗan nan ba, na rasa kalar murnar da zanyi, Ya wanne irin aiki ka samu baka faɗa min ba bayan kace ni ce sirrinka".
Yana goga haɓarsa saman kaina yace,"wai ni Mairo wanne kaya ma kike nufi ne?". Na zame daga jikinsa ina cewa, "Ya Kabiru waɗan nan mana". Yay ɗan jim yana daɗa ƙare min kallo, bakinsa ya motsa kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, muryarsa a hankali ta fita da cewar, "Mairo yau kinfi ko yaushe kyau, kin ƙara kyau sosai, har kyan naki na neman kashe min idanu". Daɗi ya kamani ina wasa da yatsunsa ina cuno baki gaba nace, "Ya Kabiru amma shi abokinka Jawad haka yace min wai mummuna dani sai rashin kunya, inda za'a bashi ni ma gidan zoo zai kaini".
Yaja ƙaramin tsoki da cewa,"ƙyale wannan shashashan, komai shi baya masa kyau...kin sha ice cream ɗin dana kawo miki ɗazu?".
Na kaɗa masa kai alamar a'a, "ai ban gani ba, wa ka bawa ya aje min?". "a kusa dake na aje miki, ƙila Gwaggo ta ɓoye miki". "ko kuma wannan kwaɗayyar ƴar tata ta shanye min ba dan nasan dai Gwaggo ba zata adana min ba ko zata ga ƙwari na shiga ciki". Nayi kamar zanyi kuka na ƙwace hannuna daga nasa na fita a ɗakin ina cewa,"Allah Gwaggo in dai ƴarki tasha min abuna yau saina ɓallata acikin gidan nan". Tace dani,"me zai hana ki ɓallata tunda kin samu kara".
Ya Amadu kuwa ko da ya dawo sai cewa yayi ai Adawiyya ta fini kyau, kayanta ma sunfi nawa kyau, nawa ma kamar ba sabbi ba, yau ɗinma dana saka kayan larabawa maimakon nayi kyau sai nayi muni, Adawiyya kuma ta zama kamar balarabiya, Naji haushi sosai danni a komai so nake naji ance nafi ƴan gidanmu musamman Adawiyya da take sakuwata. Abincinsa ma da aka bani na kai masa ɗaki ina sane na faɗi da gangan na zubar, na kuma ji daɗi da Inna Zulai tace babu wani sai dai idan ya duba masu awara.
Da daddare na shiga ɗakin Gwaggo zan cire kaya, na ɗauki zanen Gwaggo da ke rataye jikin ƙofa na rufawa Kulu da ke kwance, saboda yanda naji garin da ɗan sanyi sanyi. Na gama sauya kaya zan fita maganar Gwaggo ta dakatar dani.
"dawo anan zaki kwana". Nace mata,"bari na ɗauko kayan shimfiɗa". "zo ki kwanta nan kusa dani". a kan gadon ƙarfen nata da ta saba kwanciya ita ɗaya na kwanta kusa da ita, na takure zuciyata cike da taraddadi, can naji tayi nisa ta fara ce min.
"ayau kin shiga wata sabuwar rayuwa ta ƴa mace wadda tasha banban data ƙuruciyarki. Zina da dangoginta, Mairo na horeki da ki kiyayesu, idan ba haka ba zaki ƙare rayuwarki ne acikin