NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 2 of 223

nan kusa bada jimawa ba". Dariya na ƙyalƙyale da ita, na ɗago kai ina kallonta nace,"Inna idan ya shigo me zai yi miki?". Ba tare data dubeni ba ta ƙarasa tasbihin da take sannan tace, "ya shigo nace masa sauran ƴaƴa duk sun wuce makaranta ke kina nan a zaune". "idan yazo hukuntani kuma ki hana ba". Na faɗa ina ƙara ƙanƙameta ina murmushi, inata jiyo takun sauran yaran gidan na wucewa makaranta. Buɗar bakinta zatayi magana aka ɗaga labule, Gwaggona ce bakinta ɗauke da sallama, aciki na amsar sallamar sai Inna Amarya wadda ta amsa a fili suna gaisawa. "ai zanbi bayanta sai Zulai take ce min ta shigo nan bata tafi ba". "umm". Shine abinda Inna Amarya ta iya cewa kawai, dan ta tabbata Inna Zulai ta faɗi hakanne domin Malam yaji ko kuma ita Gwaggo ta zazzageni da faɗa. "gashi kuɗin laraba ne dama, sai da naji yara kowa na faɗar abashi nasa sannan na tuna da nata, tunda ita bata da hankalin tuna abubuwa masu muhimmanci, tafi gane sai taje a dawo da ita". Murmushi kawai Inna Amarya tayi ta miƙa hannu ta amsa tsohuwar ashirin ɗin dake hannun Gwaggo, ita kuma tasa kai tana ƙoƙarin ficewa, Kafin ta fita ta juyo ta kuma cewa da Inna Amarya, "nace yau mu sayo awara ko kuma ayi ƙosai kawai?". Muka haɗa ido ni da Inna Amarya yanda Gwaggo ba zata gane ba, sannan Inna Amarya tace mata, "a siyo awarar kawai, tunda kinga shekaranjiya da jiyan duk ƙosai akaci". "to shikenan". Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin gaba ɗaya acikin sanyin jiki. Ɗabi'u da kyawun hali, da sanyin jiki irin na Gwaggona su mutane suke min Kwaɗayin samu, ni kuwa a halinta babu ɗaya dana ɗauko musamman ta ɓangaren haƙuri, ban sanshi ba ni kam. Gyaran muryar dana jiyo ne daga tsakar gida yasa na bankaɗa ƙasan gadon ƙarfen Inna Amarya na faɗa ciki a gigice, jikina banda ɓari da kyarma babu abinda yake yi, tsorona Allah tsorona Ya Amadu ya shigo ɗakin Inna Amarya, ko kuma uwar gulma Inna Zulai tace masa ban tafi makaranta ba. Banda sauke numfashi da sauri da sauri babu abinda nake yi. "kya iya fitowa ai, naji kamar ɗakin Malam ya shiga". Inna Amarya na faɗar haka nasa kai zan fito daga ƙasan gadon, aiko sai jin sallamarsa kake ya shigo ɗakin, babu shiri na kuma maida kaina Allah ya taimakeni bai ganni ba, da yau saina gane bani da wayo, Ya shigo ya zauna ya gaida Inna Amarya sannan ya tashi ya fice, yana ficewa kuwa na fito, dan nasan ɗakin Gwaggo ya faɗa kuma idan ya shiga yana jimawa bai fito ba, takalmana da allona a hammata na fito saɗaf-saɗaf na fice daga gidan, ina isa bakin zaure na arta ana kare, ban tsaya kuma a ko'ina ba sai makaranta, kuma ko dana isa Malam ya tambayeni dalilin makarar dana yi sai nace masa Ya Amadu yace dan Allah yayi haƙuri zai zo yayi masa bayani. Malam Nasiru ya kaɗa kai kawai ya bani hanya na wuce, darajar Malam kaɗai ita ta ke saka shi ɗagawa ƴan'gidanmu ƙafa a duk wani lamari da ya shafemu a makarantar. Da an idar da sallar asuba muke shiga makarantar asuba, ba kuma a tashinmu sai ƙarfe takwas, sannan ƙarfe goma mu ƙara komawa. Muna kan hanyarmu ta dawowa ne mukaci karo da Ya Kabiru, tun daga nesa ya buɗe haƙora yana sakar min ƙawataccen murmushinsa wanda ke daɗa fitar da ainihin kyawunsa, gani nake kaf duniya babu wani namiji me kyau kamar Ya Kabiruna, haka kuma babu ƙanwar data yi dace a rayuwarta kamarni, samun Yaya mai nagarta hali, dattako, ilimi, haƙuri da sanin ya kamata kamar Ya Kabiruna sai an shirya. Shekaruna goma sha huɗu a duniya, a idon jama'a da dama na girma amma banda idon Ya Kabiru, domin kuwa shi kullum a wajensa jaririya nake, ɗanya shagaf ma kuwa, baya min wannan kallon girman da mutane ke yi min, saboda haka ne ma sau tari idan nayi abin faɗa sai yace a ƙyaleni ai ban san me nake ba, da saurana har yanzu, a bari lokacin dana girma sai a dinga yi min faɗan, shine lokacin nasan me ake cewa me kuma ake nufi, amma yanzu idan sunyi a banza dan ba fahimta nake ba, a banza kuwa, domin ni dai Mairo da wuya ayi min faɗa na gane me ake nufi, indai ba wai nice nayiwa kaina faɗan ba. Daga inda yake ya buɗe min hannu, na tafi da ɗan guduna zan faɗa jikinsa na rungume shi sai kuma ya sarƙafe hannayensa yaƙi bani damar hakan, na cuno baki gaba cikin shagwaɓa ina bo-ne fuska, fuskarsa na bayyanar da ƴar siririyar dariya ya dafa kafaɗa yana cewa, "muje ki rakani shago na siyowa Gwaggo sikari". Hannuna acikin nasa muka ƙarasa har shagon Bala, ya auna sikari ya bamu, mun juyo zamu tafi yake cewa Ya Kabiru a faɗawa Malam dan Allah idan kuɗaɗen nan da yake binsa zasu samu yana da buƙatarsu,  yana so zai ƙaro kayan shago, Ya Kabiru ya jinjina masa tare da cewa, "to Bala insha'Allahu zan sanar masa. Nawane kuɗin dama?". "dubu huɗu ne da dari uku, ɗazu ma Adawiyya tazo ta karɓi ɗari to amma ita wannan a barta". "to Bala an gode Allah ya saka. Kuɗin kuma in Allah ya yarda za'a kawo maka". Har muka iso gida idona a rufe yake, zuciyata na wani irin zafi, bana so ba kuma na ƙaunar naji ana bin Babana bashi, duk da cewa saita kai m
🏠