NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 199 of 223

du ma za suyi su fita su bar ɗakin. kawai sai ya kaɗa kansa yace da ita,"har yanzu ba ki yi wankan ba?". kamar jira ta ke yay maganar da sauri kuma cikin saurin murya tace,"nayi tun ɗazu ma na fito, kayan da zan saka ne ban san inda suke ba". abin da tace ɗin ya fito tare da tsayawarsa a gabanta, wannan dunƙulallan abun da ke maƙogwaronta yaƙi wucewa a san da tayi ƙoƙarin kora shi da yawu. a yanzu da take jin saukar numfashinsa a jikinta ji take kamar zai ɗaga hannu ya duketa ne. dan haka bakinta yay saurin furta,"kayi haƙuri yanzu zan shirya". "why are you afraid of me?". bata iya kallonsa ba kuma bata iya ba shi amsa ba, alhalin taji me yace ɗin. "wannan wankan da ki kai sunansa wankan ƙazanta". ya miƙa hannunsa yana haska mata agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana ci gaba da cewa,"ko da saɓi ɗaya ki kaiwa jikinki bai ci ace kin fito a minti biyu ba balle har ki ƙara da cewar tun ɗazu kika fito". sai yasa hannu ya ɗago haɓarta,"ki nutsu Nawwara babu abin da zanyi miki, ba zan cutar da ke ba, ni ba mugu bane...kawai ina so ne naga kema kin zama kamar kowa ba yanda kowa ke son ganinki kina kai komon aiki ba...ki koma ki sake wannan wankan, akwai towel aciki ki ɗaura shi kar ki mayar da kayan jikinki dan wata dauɗar ce zata kuma hawa jikinki...idan ma ba za ki iya ɗaura nawa ba to akwai sabo daga ɗayar hanger ɗin yana nan ki saka shi". sai ya saki haɓar tata yay mata nuni da bakin gadonsa,"kayan da za kisa su na cikin waccan ledar, dan Allah Nawwara kar ki ɓata lokaci, jiranki nake yi, kuma nima jirana ake". sai tayi masa knooding kanta kawai, ya juya ya fita sannan ta koma toilet ɗin ta sake yin wani wankan, sai dai bata sako sabon towel ɗin ba kaman yanda yace, nasan ta saka ba tare da tasan me yasa zuciyarta ta sauya ra'ayi ba a san da zata saka sabon. atamfa ce sky blue da kwalliyar flowers dark blue acikin ledar da ta buɗe, anyi ɗinki jiki da dark blue ɗin net less, daga atamfar har ɗinki sun bugu, tana iya tuna inda ta taɓa ganin irin atamfar da kuma kuɗinta da taji an ambata, ranar da su Ummi suka je store su kai sayayya, acikin kayan taga atamfar har Ummi tace ta bawa Sadiya ita a gudunmawar bikinta, atamfar na da tsada dan dubu ashirin taji Ummi na cewa Yagana ta siyo, har Yagana ke cewa ana almubazzaranci dai da kuɗi, ta ke ta mitar mene zai sa a sayo atamfa har ta wannan kuɗin, a sayo ta ƙasa da hakan ma sauran kuɗin kuma ai sadaƙa da su tunda an lissafa dole sai an kashe su. sai ta ke ganin kamar zata yi kuskuren saka kayanne, wata ƙila yayi mantuwar nuna ma ta su ne, amma wannan kayan sunfi ƙarfinta, sun girmi matsayinta, ba ta kai ba, bata isa ta saka sutturar da ta kai waɗannan kuɗin ba, abunda ta sani shi ne kuɗin suttirarta ba ya wuce sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, atamfa leda kenan ita ma kuma sai sallah ne Baba ke siya musu, amma yawancin kayanta kwance ne suke samu a ba su. saboda haka sai ta zaro mayafin ciki ta yafa shi akanta, duk da cewar ba wani babba bane amma yazo mata har kusan cikinta, ta ɗauki kayan ta riƙe ta nufi ƙofa ta fita, daga bakin ƙofar ta tsaya kanta a ƙasa, sannan ta buɗe baki, ta ɗan ɗaga muryarta yanda zai jiyota tace,"wanne ne kayan?". idonsa ya ɗauke daga kan tvn da ke manne a bango, ya juyo zuwa inda yaji sautin muryarta da tambayartata, idonsa ya fara sauka akan ƙafafunta da suka bayyana ta ƙasan towel ɗin, kafin ya maida ganin nasa ga kayan da take nuna masa. "ehh su ne". yana faɗin hakan ta juya ta koma, kayan kaman an auna da jikinta, dai-dai ita ciff. tunaninta bana yadda zata fita gare shi a cikin kayan ba ne, ta yanda zata fita ta dinga ratsawa ta cikin mutanen gida su na ganinta. saboda haka sai ta yafa mayafin a kafaɗa, shi kuma ɗankwalin ta ɗora shi a saman kanta ta rufe fuskarta da shi, sannan ta fita daga ɗakin. abun da ya bashi tabbacin fitowarta ƙamshin man da ta shafa, dan haka ya ɗago yana kallonta a inda ta ke tsaye daga bakin kujerar da ke kusa da shi. kamin ta silale ta duƙa ƙasa, wannan hannayen naci gaba da rawa kamar yanda suke yi tun a ɗazu, ba dukan fuskarta ya gani ba amma yasan tayi kyau, gefen leɓensa ya tale da murmushi sannan yace da ita. "ga abinci can kije ki zuba". "zan ci idan na koma ɗaki". shi ɗin kawai ta gani a gabanta san da tayi shiru da maganar, kafin tayi wani yunƙuri taji ya sunkoyo ya kamo hannunta guda ya ɗagota, sannan ya jata suka fara tafiya zuwa inda dining ɗinsa yake daga can baki-bakin ƙofar shigowa, Allah ya sani a wannan halin da take ciki babu abin da ta ke so tayi irin ta kurma ihu ta ambaci ta shiga tara, dan halin da yake sata aciki tun daga ɗazu zuwa yanzu yafi gaban ta shiga uku, ta lura ya kasa fahimtar cewar yana neman ya zautar da yanayinta musamman a yanzu da ya ƙara sa ɗaya hannunsa ya kamo ɗayan nata ta bayansa, ya damƙe a nasa hannun, kuma abin da ta fahimta so yake ya dakatar da duka hannayen nata daga rawar da suke yi. "haka na cewa telan ɗinkin na ƴar siririya ne, siririyar fa irin firit ɗin nan,
🏠