plan will be akan Nawwara?....Jawad! Ahmad! Kabir! kowa fa son gaskiya yake mata and kowa kuma ɗin ya taka wani muhimmin abu a rayuwarta. wait, let make a decison! ko dai ta zama bata kowa ba acikinsu a raba sa'insar da zata iya shiga tsakani! dan idan Kabir ya iya haƙuri, do you think Ahmad zai iya haƙura?, kuma ya ɓangaren su Hajjah Nashwa(Maman Jawad) zai kasance?...abun da bamu sa ni ba shi ne, zaren wata ƙaddarar da bamu san da shi ba zai iya warwarewa a gobe, wata ƙila before the wedding Fatiha takes place or after, WATA ƘADDARAR TAMKAR ZANEN DUNTSE TAKE....an interesting Chapter coming next insha'Allah.*_
One Love Guyz❤
[7/18, 11:45] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*(48)*
"menene?". tambayar tasa ta fito daga bakinsa kai tsaye zuwa cikin kunnuwanta, kuma yanayin yanda yay maganar ɗumin iskar bakinsa na fita ta sauka a wuyanta ya ƙara haifar mata da kasala. ta buɗe lumsassun idanunta ta zubesu akan hannunta da har yanzu ke kan ƙirjinsa riƙe da gaban rigarsa, wata uwar kunya ta lulluɓeta har tana neman nutsar da ita acikin ƙasa, yayin da bugun zuciyarta ya ƙaru wanda tana da yaƙinin yana iya jin sautinta dum-dum!. a hankali ta shiga ɗauke hannun nata akansa, shi kuwa yana lure da yanda hannayenta ke rawa kamar ana girgizasu. ya fahimta a tsorace ta ke, tsoron da shi kuma ba ya so yake ganinsa a tare da ita. sai kawai shima ya saketa ya matsa baya da ita yana kallon yanda hatta ƙafafuwanta rawa suke, hakan yasa yace da ita,"zauna". yanayin muryar tasa da ta fito fayau tasa tayi saurin ɗago kai ta dube shi, a lokacin har ya zauna kan kujera yana tattara wasu takardu da ke gabansa.
ta silale ƙafafuwanta zuwa ƙasa ta durƙushe akan carpet ɗin, har yanzu hannunta bai bar rawa ba, kuma tambayar da ya jefo mata ne yasa gaba ɗayanta girgiza a lokaci ɗaya. "kinyi wanka?". sai ta shiga girgiza masa kanta da ke ƙasa ba tare data amsa masa da baki ba. kuma a wannan karon da ya ƙara jefa mata tambayar taji yanda amon muryarsa ya sauya daga na ɗazu. "me yasa to ba kiyi ba?". tayi shiru ta kasa cewa komai, sai taji ya ƙara cewa. "daga wannan lokacin har zuwa gobe kar wadda ta ƙara sa ki aiki acikin gidan nan kika yi, kinji na faɗa maki, kuma duk yaron da naga kin ƙara goyawa abunda zanwa goyon yaron kaɗai zai sa ki shiga hankalinki...". sai tayi yunƙurin katse maganarsa da cewan,"ai...". bai bari ta ƙarasa ba shima ya tari numfashinta,"ai me? ke baiwar kowa ce?, ko su suka ɗauko ki aikin?". yanda yake maganar cikin ɗagawa sai ya tsoratata, bata san san da bakinta ya buɗe da ce masa,"a'a Ya Kabir duk ba haka bane". muryartata ta fito a karkarye. kallonta kawai yake yi kamin yaja tsaki ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihun wando. sai da ya zo saitinta sannan yace,"minti goma na ba ki kiyi wanka ki shirya". ta miƙe da azama zata bar ɗakin ƙwayar idanunsu ta gauraya, ya wurga mata wani wawan kallo da ya tsaida tafiyarta yace,"ina nufin ki shiga wannan toilet ɗin kiyi wanka". ta haɗiye wani guntun yawu sannan tace,"zan ɗauko kayana ne, kuma Innah zata nemeni zamu yi yankan albasa".
kai tsaye bakinsa ya fito da furucin,"ba zaki yi ba. ko ɗazu da nace kar ki ƙara aikin komai kunnenki a toshe yake?". tace,"a'a". bai ce komai ba ya juya zai fice yaji tana binsa a baya, bai tsaya daga tafiyar ba taji yace,"kar ki ja na sauke dukan fushina akanki...ina nufin kiyi wanka anan, ga kaya can a leda ki saka su, idan kin gama ki sameni a parlo". abin da yace kenan ya fice gaba ɗaya daga ɗakin cikin taku biyu. tabi bayansa da kallo tana haɗiye wani ƙullutun abu da bata san ko menene ba, wucewar sakanni uku ta ɗaga ƙafarta da take tunanin ta maƙale a wurin ta ƙarasa ta rufe ƙofar ɗakin, sannan ta juyo ta nufi inda toilet ɗin nasa yake ta buɗe ta shiga, bata da natsuwa sam, hakan yasa ta gaggauta yin wankan ta fito, ƙamshin shower gel ɗin da tayi wankan da shi ya baɗe ɗakin, hatta ita kanta lumshe ido take tana zuƙar ƙamshin saboda daɗinsa.
a ƙasa ta tsuguna ta jira har ruwan jikinta ya gama tsanewa gaba ɗaya, ta miƙe kenan sai gani tayi ƙofar ɗakin ta buɗe a lokaci guda, kuma ƙofar ta gaya mata wane tun kafin taga ƙafafuwansa da suka shigo a yanzu, ba tare da ta shirya ba sai jinta tayi a tsaye akan ƙafafunta duk a rikice, ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi.
sam bai lura da ita ba sai da yaje ya kwashi takardunsa ya dawo zai fita tukunna ya lura da ita a tsaye sai ƙudundune jiki ta ke yi, kallo ɗaya yaywa gashin da ya kwanto saman goshinta ya san zai iya cewa jikinta yaga ruwa, amma yanayinta sam bai yi kama da na wadda tayi wanka ba. dan yanda ya fita ya barta da kayan jikinta haka ya dawo ya sameta da kayan jikinta. kallon hannayenta da ke aikin rawa yake yana jin kamar ya kamo su ya riƙe acikin nasa har sai sun tsaya, to amma hakan da zai yi dai-dai yake da ƙara rikita yanayin tsoron da yake gani tare da ita, ƙwaƙwalwarsa na gaya masa cewa bayan ihun da yake ganin bakinta zai iya yi wannan siraran ƙafafun nata har kwasa da gu