a kai masa ɗinkin biki...idan bai ɗinka ba sai ka sa tawa kawai". Ahmad ɗin ya kalla ɗan'uwan nasa cike da so da ƙauna yace,"kai kuma fa?". "ai ka fini buƙatarta, kai ne jigon saka babbar riga a gobe. kuma dama ai ba kala ɗaya na ɗinka ba, akwai wadda zan saka a dinner, so sai na fasa sakawa nasa goben". Ahmad yace,"tom shikenan dan babu alamar ɗinkin nan zai gamu a yau wallahi, ya ɓatan rai sosai". Kabir ya numfasa yace da shi,"wurin dinner ɗin ƙarfe nawa ne?". Ahmad yace,"takwas". "Allah ya kaimu". yay shiru, a ɗaƙiƙa ɗayan da ta wuce Ahmad yace da shi,"kaje asibiti kuwa?". "ni ba ciwo ba me zai kaini asibiti". "baka da lafiya Kabir, kaga yanda kuwa ka rame, ai yanayinka kaɗai ma na nuna ƙarfin hali kake, shi yasa ban takura maka ma akan bikin nan". Kabir bai ce komai ba, suka ɗora da wata hirar akan ziyarar da suke so su kai can dangin su Yagana bayan bikin.
daga bisani ya miƙe ya koma ɗakinsa, yana shiga ya tarar da kalanda ɗin da Ahmad yace ya aje masa na abokansa da ya gayyata. ya kai hannu ya ɗauki kalandar, hoton Maryam ɗin kawai yake kallo, da wannan fararan idanuwan nata ƙal, ta saƙalo kanta ta gefen fuskar Ahmad ɗin tana murmushi. ya lumshe ido yay wurgi da ita gefe, sannan ya nemi kujera ya zauna ya jinginar da kansa.
_"Kabir ka daina forcing kanka akan son yarinyar nan, na faɗa maka sam ba sonta kake ba kaƙi ka yarda da ni, kawai kana so ka huce takaicin rashin Maryam ne akanta, amma ba sonta kake ba, ko ka aureta ba zata samu soyayyarka ba tunda Maryam ta riga ta gama da zuciyarka...ka yarda da ni ko kar ka yarda Nawwara tausayinta kawai ka ke yi, dan haka ka daina ƙoƙarin sauke zafinka akanta, kar ka je ka aikata wani abin da zaka zo kana regreting"._
abin da Abdurrahim yace da shi kenan a jiya kafin tahowarsa, bayan sun gama waya da Nawwara, kuma furucin da ya haddasa faɗa a tsakaninsu, saboda haka ne ma Abdurrahim ko jiran tashin jirginsa bai ba ya tafi, bai sani ba ko daga baya ya koma ya ɗauki motar oho. ya fitar da iska a bakinsa yana kulle idanuwansa, a hankali kuma hoton kwanakin baya ya shiga haskawa cikin idonsa, wannan ranar da ya je Qatar jin Akila ta sauka a ƙasar, yaje don su gaisa da ita sun jima ba su haɗu ba sai dai a waya. yana zuwa ya tarar Ammi ta aiki Maryam store zata yo mata siyayya, ita kuma Maryam ɗin sun yi faɗa ita da Alhassan yace ba zai rakata ba, zuwansa Ammi taji daɗi tace ya ɗauki Maryam ɗin dan Allah ya kaita tun da yau iskar kanta tace driver ba zai jata ba shi yasa ma ta liƙe sai dai su tafi da Alhassn ɗin. shi kansa a lokacin ganin idon Akila ne kaɗai yasa shi faɗin abin da bakinsa bai shiryawa ba,"tazo mu tafi". amma da ace babu ita a wurin duk da cewan Aiya na nan tsab zai ce da Ammi ba zai kaita ba...kuma duk da hakan darajan Akila dai Maryam ɗin taci har suka je suka dawo bai taɓa lafiyar jikinta ba, saboda irin maganganu masu ɗacin da ta dinga yaɓa masa har suka je suka dawo, amma ko abin da tayi masa a parlo yaci ace ya manta da Aaliya da Akila da ke zaune a wurin yasa ƙafa ya fyaɗeta ta zube ƙasa, sannan ya ciro belt ya tafarfasa mata jiki, ta yanda gobe waninsa ma ba zata yiwa wannan rashin kunyartata ba.
ya buɗe idanuwansa a zafefe yay tattaki zuwa bangon gabas ya tsaya, ya harɗe hannayensa ta baya, kallon bangon kawai yake ba tare da ya san me yake kalla ba ajiki, tsawon wucewar mintina goma ƙofar ɗakin tayi ƙara.
a hankali hannun Nawwara da ke riƙe da handle ɗin ke tura ƙofar, muryarta a can ƙasa tayi sallama da kai tsaye ta doka wani abu a zuciyoyin duka su biyun, ta rakuɓe tsaye daga bakin ƙofar kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta, wucewar sakan 1,2,3 taji saukar maganarsa a tsakaiyar kanta. "ni zan zo na ƙarasa shigo da ke?".
wannan siraran ƙafafuwan nata da ya ƙurawa ido suka shiga takawa a hankali su na lumewa acikin tattausan carpet ɗin da ke malale a bedroom ɗin, kuma bai san dalili ba sai yaji ba zai iya jira ta ƙaraso har zuwa inda ƙafafun nata da zuciyarta za su iya tsayar da ita ba. dan haka a cikin shirin da bai yi ba yaji ya ƙarasa inda ta ke ya kamo hannunta, ƙafafunsu suka tsaya a inda bugun zuciyarsa ya tsayar da shi.
tsawonsa da ya bayyana a yanda yake tsaye a gabanta, sai wani irin ruɗani da kasala suka yi barazanar jefar da ita ta zube, tayi saurin saka hannu ta damƙo gaban rigarsa maɓalli ɗaya na gaban rigar ya cire, a yayin da shi kuma yay saurin zagaya hannunsa zuwa weast ɗinta ya dakatar da ita daga faɗuwar. wata bahaguwar ajiyar zuciya da gaba ɗayansu ba su shirya mata ba ta sauka ajikinsu.
_*what am i going to say???😅, well, to all of you that commented on the last chapter, i say a big thank you😘...i enjoyed some of the conversation i heard from you guyz...please keep the votes and comments comming oak...*_
_*and what do you think would happen? surely za'a ɗaura auren Maryam a gobe, but da wa za'a ɗaura?, Maryam ta wa zata tabbata?, don't you think everyone acikinsu ukun deserves to marry her?, how do you think Kabir's