NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 196 of 223

ka sauya kowa sai ƙorafi yake akanka, jiya a gidan nan tambayanka ake alhalin kana cikin gidan, keɓewa daga mutanen na mene Kabir?, wannan sabuwar ɗabi'ar taka ban yarda da ita ba". muryarsa a ƙasa cike da girmamawa yace da Baban nasa,"kayi haƙuri Baba, ni kaina bana jin daɗin kaina a yanzu, kuma ba komai bane ya jawo hakan sai yanayin karatuna, accounting akwai zafi sosai, ga yanayin yanda business ɗin nan ke neman wargajewa, company ɗin da muka haɗa hannun jari dasu naje nasa hannu a kuɗaɗen da basu kenan ba, hakan kuma na neman yaja min asarar da ba zan iya maida ita ba, shi ne duk al'amura suke neman dagule min". Malam ya numfasa yace,"to ya kuwa ba za kai wannan ta'asar ba ka koma wani kalar mutum na daban...mtswww". tsakin da mahaifin nasa yaja ne yasa shi saurin ɗagowa ya dube shi, "dan Allah Baba kayi haƙuri, adu'arka kawai nake nema". "Allah ya gyara lamarin...kuma jiya munyi magana da Gwaggo Azumi tace min kai kaɗai ne baka bada gudunmawar Amadu ba, me yasa? bayan kasan kaf ɗinku babu wanda aka ɗaukewa hakan". Kabir ya ƙara yin ƙasa da kansa yana fitar da wata zazzafar iska daga bakinsa. "wallahi Baba gaba ɗaya na manta ne, ni da kaina ma na kira shi nace ya tura min account number. to ban san me ya sha'afar dani ba. shi kuma bai tuna min ba". Malam ya kuma jan tsaki," ya za'ai ya tuna maka salon kai tunanin maula yake wurinka tunda ka fishi, kuma ai ba shi yace ku haɗa masa ba ni naga hakan ya kamata shi yasa nace ku haɗa masa, da kake wani batun bai tuna maka ba. banda shirmen banza har akwai abinda zai ɗauke hankalinka akan lamarin da ya shafi ɗan'uwanka...to bari kaji na faɗa maka Kabir wallah dukiyarka a banza zata tafi muddin kace ba zaka taimaki ƴan'uwanka ba dan kwata-kwata ba za tayi albarka ba. dan ubanka idan baka kyautata musu ba wa zaka kyatatawa, shirmen banza kawai, ashe a matsayinka na magajina ba zaka iya kula da su ba lokacin da na bar muku duniyar...". yay saurin tarar nunfashin mahaifin nasa da faɗin,"a'a Baba ba haka bane wallahi ka daina wannan tunanin. na rantse ko kusa ko alama bani da zummar morar abinda yake mallakina ni ɗaya, duk wani faɗi tashi da nake dalilin ƴan uwana na kan gaba gaba". "shikenan ai. tashi kaje, ni dama wannan sabuwar halayyar taka ce bana so, dan Shatu ma ɗazu ta faɗa min kwata-kwata ma bata ganinka acikin sha'anin da ya shafi bikin, shi Amadu da abokansa ne kawai suke komai". a wannan karan bai ce komai ba, yay sallama ga Baban sannan ya miƙe ya fita, takaici duk ya cika shi, shi komai yana yi ne domin Allah, abin da Baban bai sani ba shi ne shi kansa gidan da Ahmad ɗin zai zauna shi ya bashi a matsayin gudunmawa tun ranar da aka kira shi akace an tsaida maganar aure, tunda yasan Ahmad ɗin ba ya da ƙarfin da zai iya mallakar gidan kansa a irin ƙurarran lokacin da akasa, yasan da cewar yafi ɗan'uwan nasa ƙarfi shi yasa yaga babu babban taimakon da zai yi masa sama da wannan, kuma yace da shi hakan ya zama sirri a tsakaninsu ko da Baba bai yarda ya faɗawa ba, dan zasu ga kaman ba ya wani samu da wurin aikinsa, amma yanzu anzo an saka masa ido ana ta ƙanan munafurci ana neman haɗa shi da mahaifinsa. zai nufi part ɗin Ahmad ɗin ya hango Nawwara, tana riƙe da wata ƙatuwar kular abinci da ta rinjayi hannunta, ga goyon wannan ƙaton yaron da ta yiwa wanka ɗazu, a kallo ɗaya yaywa goyon ya fahimci nauyin yaron yafi ƙarfin ƙirjinta. sai ya kulle idonsa ya buɗe, so yake ya kirata tazo gabansa yasa hannu ya kunce ɗaurin zanin, in yaso ma yaron ya faɗi ƙasa ko fasa kai ne yayi shi babu ruwansa, ko da yake bautar daga yau ne, matsayin da zata samu a gobe ba ya ƙara bawa kowacce ƴar banza damar sakata rainon yaronta ba. yay tattaki ya ƙarasa wurin cuncurundon iyayensa mata da suke tsaye ana lissafin yanda za'a ɗora tukunyar sanwar abincin yau...ta gefenta ya ratsa, amma bata san da ya zo wurin ba, haka kuma bata san ya wuce ba, sai bayan wucewarsa ne ta tsinci maganarsa a iska da ke shiga cikin kunnenta a yanzu. "kar ki sake kizo min da wannan goyon ɗakina". abin da yace da ita kenan, kuma ta gane mai maganar tasa take nufi, taje ta same shi, ta same shi a ɗakinsa, kuma bada wannan goyon ba, hakan yake son ce mata amma sai ya dunƙule maganar. ta waiga tana kallonsa, kallon tafiyar nan tasa take mai ɗaukar hankali, tafiyar da ba zata iya kwatantata ba, taji wucewar wani dunƙulallan abu ta wuyanta sannan ta ɗauke kanta daga inda yake. haka kawai ta tsinci hannunta na rawa, ta ɗan duƙa ta zurkuɗa goyan yaron ta gyara shi, sannan ta ɗauki kular abinci ta wuce babban store ɗin gidan da ke bayan ɗakin da ake ajiye generator. **** "za ka fita da motarka ne?". Kabir ya kalli Ahmad da yay tambayar yace,"i dont think so, amma kai yanzu zaka fita da ita?". Ahmad ɗin ya ƙara cewa,"zuwa 11 dai. wancan ɗan rainin hankalin Abba telan bai ɗinka min babbar rigar da zan saka ba gobe...to zuwa zanyi na sa shi a gaba". Kabir ya shafo wuyansa sannan yace,"kai ma kasan halin wannan mashirirancin ina kai in
🏠