a, kamin ƙiftwar idona sai tsintar Jawad nayi agabana, ya damƙo hannuna yana matsawa yace,"dan Allah Maryam ƙara faɗa". na cuno baki nace da shi,"me?". ya rumtse ido ya juyar da kai sannan ya dawo da kallonsa kaina yace,"sunan da kika faɗawa Me Martaba kamin ya fita". na karyar da kai na ɗan harare shi sannan nace,"au wai My Jawad?". sai kawai naga ya ɗaga kansa sama ya cije leɓensa na ƙasa yana wani irin smiling, sannan ya sauke kan nasa yana cewa,"ashe duk pretending kike dama kina sona?". na kanne ido nace da shi,"kawai dan nace My Jawad sai ka fassara shi da abinda yake zuciyarka. to dama ai dole na so ka tunda kai ɗan'uwana ne, kuma dan nace My Jawad har wani abune dama?". "Jawad ɗinki fa kika ce". na sake cewa,"to a matsayinka na Yayana kai ba nawa bane...kaga tsaya! na fahimci dai jingina kalmar My ga sunan mutum ta ƙunshi tarin ma'anonin da yawa, dan haka zan kiyaye gaba". kuma irin kallon da yake min acikin ƙwayar idanuwansa yasa sauran maganata ta maƙale a maƙogwarona, cikin wani irin mood mai wuyar a fassara shi. sai kawai nayi ƙasa da kaina na taka zan wuce ta kusa da shi sai naji ya riƙo hannuna ya dawo dani gabansa, cikin wata iriyar murya da ban taɓa jinsa da ita ba yace,"ina sonki Maryam, wallahi ina sonki, kuma burina ki zama abokiyar rayuwata na har abada, Maryam Jawad mai ƙaunarki ne, ya fara sonki tun a ranar da ya fara ɗora idanunsa akanki cikin wannan tsiwar rashin kunyar ta ki, kawai nayi shiru ne a lokacin saboda kinyi yarinta da yawa, kin min ƙanƙanta, idan nace zanyi soyayya da ke za ki dinƙa cin karo da abubuwan da suka fi ƙarfin kanki, please Baby doll kice ni za ki aura ba wancan Ahmad ɗin ba da bai ko iya soyayyar ba, kizo gareni na nuna maki soyayya da...". ban bari ya ƙarasa ba kawai na ture shi daga matsoni jikinsa da yay na fice daga turakar mai martaban, ina jiyo shi yana fitar da wani makirin murmushi mai ƙarfin sauti. kuma ban ƙara ganinsa ba sai yau da safe a dining, wai saukarsa kenan daga ƙasar moroco ya biyo ta nan saboda yasan idan ya wuce ethiopia ba lallai ya sami damar zuwa bikin ba, shi ne ya shigo a yunwace yana zuwa ya afkawa abincina da muke ci a plate ɗaya ni da Bro Almustapha. na kama ƙunƙuni ya fizgoni gabansa ya damƙe gashina wai bari ya yanke gashin da wani gaja can ya gani ya liƙewa, ai yasan komai, Ahmad ba sona yake ba haskena da gashina yake so, Bro Almustapha ya ƙwaceni na bishi da harara ina murguɗa masa baki nace,"oho dai ba zan dai ce ina sonka ba".
nasa hannu na share hawayen da ke sauko min cikin azama, tunawa da maganar Mami da nayi a ranar da ta tsuguna min tana roƙona da girman Allah kar na kuma zubar da hawaye akan asalina, in har da gaske ne na yafe mata to karna ƙara kuka akan yanda aka haifeni, kuma na ɗaukar mata wannan alƙawarin. don haka na bar tunanin koma na zuro ƙafafuna ƙasa daga kan gadon, dai-dai shigowar Shamsiyya da suka fita tun a ɗazu, tayi turus daga inda take tana cewa,"kambu wai sai yanzu ku ka gama wayar?". ban amsata ba, nayi ma ta harar wasa ina ɗaura towel ajikina. ta taɓe baki tana cewa,"in yayi haƙuri dai gobe za'a kai masa...kuma ke Allah kiyi sauri ki shirya dan ga Daddy can ya dawo, naga ma har driver ya fita kai kaya airpot". na nufi hanyar toilet ina cewa da ita,"dan Allah ki ɗauko min underwear a ɗakin Mami". "to". sai kuma ta ƙara cewa,"dama ba ki taho da allon saukarki da certificate ba?". (da yake cikin wata ukun da nayi a qatar bayan larabcin da na koya har da alqur'ani muka sauke). "Mantawa nayi Shamsiyya, kaina duk ya cunkushe amma zan kira Alhassan in zasu taho ya ɗauko min". "to wannan gift ɗin da Madam Deborah ta ba ki na haɗa da shi acikin wannan ƙaramar trolly ɗin ko da za ki nema. tunda nasan kai tsaye gidanki za'a kai kayan, kuma zan iya mantawa ban maki bayanin inda na saka maki wasu abubuwan ba". "to Shamsiyya sannu da ƙoƙari. kiyi sauri kema ki shirya kar Anty Samiha ta haɗa faɗan har da ke...ina Aisha Tayo?". tana saka wasu kaya cikin trolly ɗinta tace,"to ai kayan fa su Anty Iftihal ne suka tafi dasu, Aisha ta bisu. dagani sai ke sai Mami da Ummi muka rage. dan Daddy ma naga kaman tafiyarmu ba tare ba". na buɗe ƙofar toilet ɗin ina cewa,"ƙila ko sai ya jira su Uncle Lucas sun zo, wannan bataliyar christian ɗin ba son zuwansu nake ba...ke nifa gaba ɗaya mantawa na ke daga zuri'ar arna na fito". na faɗa da sigar mita da jin haushi, na bar Shamsiyya da dariya tana faɗin,"kuma kin san Ummi tace rigar da Granny Chioma ta ba ki za ki saka a dinner ba". nako ce,"tabɗijam Allah tsaren dasa kayan arna wallah, ko mai zasu ce sai dai su faɗa". daga haka na faɗa toilet na barta da ƙyalƙyala ƴar iskar dariyarta mai cin rai.
*Bichi.*
Alhaji Adamu ne zaune a ƙaton parlonsa, tunda Malam yaje Umra ya dawo shikenan mutanen ƙauyen suka koma kiransa da Alhaji duk da cewar inkiyar mai faskare bata bar sunansa ba. ya ɗago da kansa ya dubi Kabir da ke zaune a ƙasan carpet yana fuskantarsa yace,"Kabir wai meke damunka ne?, gaba ɗaya