a ƙare". kuma maganartata sai ta zama kamar ta fito da allura ne ta ɗinke bakunan kowa, dan babu wanda ya sake wata maganar. ni kuwa a wannan lokacin banda hawaye babu abinda nake, dakacen inama ba'a haifeni ba nake, fata nake dama ace mutuwa tazo ta ɗaukeni a yanzu ba sai anjima ba, tun da maganar auren nan ta kama babu abin da nake facing sai ƙalubalen da ya shafi maganar asalina, hatta a dangin su Ya Ahmad ɗin ma akwai wadda tace min,"Maryam ki bar ganin zuri'arku kuna da dukiya da sarauta, kuma kema naji ance mahaifiyarki da mahaifinki sun mallaka maki kadarori da dukiyar da za'a iya saka ki a sahun farko na masu kuɗin ƙasarku, to ki sani da waɗannan kaɗai ba ki isa kifi Amadu ba, dan na lura kun siye mana shi ne da kuɗi ko kuma barazanar Yayanki zai iya korarshi daga aiki, banda haka babu ta inda kika dace da shi domin shi yafi ki da abu ɗayan da zai shafe duk wani abu da kuke gadara da shi, Maryam Ahmad ya fiki tsarkakken asali ki tuna da wannan, da tsarkakken asalinsa kaɗai duniya ma zata fi ganin nasa girma da komai ɗin da kuke tutiya da shi".
a lokacin da Umma Sahura take faɗa min waɗannan maganganun ji nayi kaman naje na sami Ummi nace mata na fasa wannan auren, to amma kuma sai na tuna farin cikin Ummina, ko ba komai ina so na sakawa Ummina da irin sadaukar da farin cikinta da tayi akan ganin na rayu. na kai hannu na toshe kunnena da ke min amsa kuwar wasu ƙananun maganganu da naji a san da nasa ƙafata zan shiga ɗakin su Jamila naji ƴan'uwan Inna Zulai nayi, hawaye ne kawai ke sauko min, kuma a lokacin kawai sai zuciyata da ni kaina muka tsinci kanmu a matuƙar son ganin Ya Kabir, a wannan yanayin da nake ciki wanda kaina ke daf da tarwatsewa babu hannun wanda nake so na jini, babu kusa da wanda nake so na jini sai Ya Kabir. to me yasa shima nake nemansa a wannan lokacin?, idan na gansa me zai yi min da zai wanke baƙin cikin da nake ciki?. ko kuma dan na sami labarin cewar wata a dangin su Baba ta shegantani yasa ƙafarsa yay fatali da ita ya tattaketa?, na tambayi kaina yafi sau cikin masaki dalilin da yasa Kabir zai yiwa wadda ta ke ƙanwace wurin mahaifinsa haka? ya manta girman mace ne?, ban ankare ba kawai naji ƙafafuna na ɗauka na su na tafiyar dani zuwa sashensa, sai da na ɗora ƙafata akan steps na entrance shiga parlonsa sannan tunanina ya ankar da ni inda nake neman kai kaina, wurin Kabir, wannan Kabir ɗin da a duniyarsa ta yanzu babu wadda yaƙi jini sama da ni, kar fa na manta ya tsaneni, shi da kansa ya furta min na rabu da shi, kenan da nazo nan ƙara na kawo masa ko me?, after all nasan da cewan a yanzu shi yafi kowa ƙyamatata, illegitimate ta ɓata kyakykyawar alaƙar da ke tsakaninmu, shin na manta ne da cewar na yiwa kaina alƙawarin ko a lahira ni da Kabir?, to ayanzu da nazo wurinsa dan huce takaici ai babu abin da zan samu face wani baƙin cikin da ya fi wanda kowa ke sani aciki, dan na tabbata Kabir zai iya wankeni da muggan kalamai akan ciwon shegantani da su Mami su kai. "Yaya kin manta Ya Kabir ɗin ba ya nan". maganar da Basma tayi kenan a bayana, ba tare da na bari ta fuskanci halin da nake ciki ba na bar wurin da sassarfa, na fita daga gidan na hau motar haya na nufi airpot, wanda sai bayan naje can ɗin tukunna na kira Ummi nake faɗa mata.
tabbas zuciyata ta karanta min yafi sau adadin lissafi cewar Maryam ba za ki taɓa auren soyayya ba, balle har ki zama cikin farin ciki, saboda wannan ciwon har abada ba zai bar zuciyarki ba, dan haka asirinki alaikum ki auri Jawad kawai, shi ne wanda ko da ya goranta maki kansa ya gorantawa. bana son Jawad dan haka me yasa zan aure shi?, ai har gwara ma wannan mutumin da Ummi ta ban labari, shi naji ɗarsuwar sonsa a raina, kuma shi ko da ya walaƙantani rantsuwar Allah ce zata ci shi, tun da ya rantsewa Ummi da Allah zai tsaya min, zai gusar da dattin baƙin cikin shegiya daga zuciyata, haka zai goge tabon ciwon shegiya da ke tare da ni, duk da nasan cewar wannan soki burutsin soyayya ne kawai, amma shima ba zai so samawa Ƴaƴansa uwa marar asali ba.
"zuwa yaushe za ku taho?". maganar Ya Ahmad ta katse dukkan tunanina, cikin sanyin muryata nace da shi,"Daddy ake jira ya dawo, mu mun gama shiryawa". "a jirgi ɗaya za ku taho?". na ɗaga kai da faɗin,"ehh". "to ki kula min da kanki kinji". na amsa da,"insha'Allah, kaima ka kula min da kanka". daga haka wayar tamu ta ƙare. wayar da ban iya saukewa ba daga kunnena ba kenan, haka kawai hoton Jawad ke haskawa acikin kaina da idanuwana. san da Mai Martaba(kakansu Mami) yace na ba shi zoben azurfar hannuna, na maƙe kafaɗa nace da shi,"a'a wannan ba naka ba ne". da ya tambayeni na wane sai na kalla Jawad da ke hakimce akan kujerar Mai martaban, fuskarsa da tsananin damuwa, kallonmu kawai yake ba tare da ya saki fuskarsa ba, ina murmushi nace da Me Martaba,"wannan zoben daga hannuna sai hannun My Jawad". nayi maganar da sigar zolaya, furucin nawa ya haifar da tasirin tsoro a gareni, dan cikin sauri ya waro ƙwayar idonsa da suka ƙanƙance ya saukesu akain