sai ta ci gaba da dariya ƙasa-ƙasa sannan ta sauko akan gadon tazo ta rungumeni tana bani peck a kumatu.
"easy mana my sister, mai da wuƙar kinji". na ƙara ɓata rai fiye da ɗazu dan ma tasan da gaske nake maganata, sai dai abin da ta raɗa min a kunne yasa na ƙyalƙyale da dariya na juyo ina wartar wayar hannunta nayi kan gado. muka haɗe kai muna karanta posting ɗin da ke cikin group en Matan Sirri a whatsapp, Aisha Tayo tazo zata gani muka korata da cewar ita yarinya ce da sauranta tukunna, abin na manya ne bana yara irinsu ba. hakan kuma ya ƙular da Aisha ta bar mana wurin.
wayata ce ta shiga ƙara, sanin mamallakin ringtone ɗin yasa na bar iya shegen da muke ni da Shamsiyya na mai da hankalina kan wayar, na ɗaga da zummar caccake Yaya nayi masa ruwan masifa, amma furucin farko da yay akaina yasa na sauko daga wannan saman mai nisa ta bala'in kishin da na hau, nima na shiga kwantar da murya kaman yanda tasa take, muka shiga zuba zantukan love ɗinmu ni da shi, kuma a wannan lokacin gaba ɗayanmu ji muke kaman muyi fiffike mu tashi zuwa wata sama mai nisa, mu zauna a duniyar da zamu kasance mu biyu ne kacal acikinta.
_thanks for your time and support, keep voting and commenting please, love you all😘😘._
[7/18, 11:14] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
_haba! Kabiro ba Kabir ba😝duk kun damemu da wani Kabir sai kace gwal🤨 yana fama da wani ƙaton kansa anan, mu muka ce yay dakon soyayyartata ko mu muka ce yay nauyin baki😏....#teamAhmad whre are guyz kuzo mu raƙashe a filin dinner💃💃Maryam da Ahmad za su tabbata abu guda, our dream has come true💃💃..._
*the whole page is dedicated to Ahmad's team.*
*(47)*
"me Kyauna kina irin zumuɗin da nake yi ne?". na juya ƙwayar idona sama kamin na dawo na saukesu kan hannuna ina kallon ƙunshin da yayta santinsu ajiya, muryata tayi ƙasa kafin ta fito a sirance nace da shi,"me ka gani Yaya?". daga inda yake naji saukar sautin murmushinsa, kuma na tabbatar kamin murmushin nasa sai da ya shafo kansa da ya sha haɗaɗɗan aski. "i heard that emotions in your voice, so tell me wanne irin shirin tarba kika min a daren gobe?". ban iya bawa Yaya amsa ba nayi saurin saka tafukan hannuna na rufe fuskata saboda kunya kaman ina gabansa. daga inda Ahmad yake ya saki wani ƙayataccen murmushi sannan yace,"hmm in dai wannan kunyar ce daga gobe dai ne zan cire ta". ban dai ce komai ɗin ba ya ɗora da,"ɗazun da safe before i hurt you who made you sad that you cried?". tambayar ta ɗauke nishaɗin da nake ciki na turɓune fuska, murya a kumbure nace da shi,"ba Jawad ba ne". na faɗa ina aikin harare kaman Jawad ɗin na gabana.
"me Kyauna wai Jawad sa'anki ne? please ban sanki da raina na gaba da ke ba wannan ba halin Autar Mami bane, ki bar kiransa da Jawad kai tsaye kinji...me yay maki?". "ni to ina ruwana da shi, ai shi ne yake fara takalata dan haka ba zan ce masa Yaya ba Jawad sunansa". nayi maganar har ina dukan ƙafa kaman ƙanƙanuwan yarinya. "bar ni da shi zan faɗa masa kar ya ƙara taɓa min Matata, her tears are very expensive ya daina zama silar zubarsu, if not kuma zan mance mu inlaws ne na rama maki ko Swty nah?". nayi murmushin da ya bayyanar da fararan haƙorana nace,"ai Yaya ko za kai inlaw da kowa kar ka yi da wannan, kirkinsa ragagge ne. ɗazun fa breakfast ena ya cinye kuma ya kama gashina yaja min da ƙarfi kawai dan nayi magana". kuma a inda Ahmad ɗin ke zaune sai ya ɓata rai,"ki faɗa masa ke matar aure ce, kar ya ƙara taɓa maki gashi mijinki ba ya son wannan wasan cousins ɗin kinji ni ko...ko after aurenmu ban yarda idan kinje gida kun haɗu da wani ba ki biye masa da wannan shashancin banzan, ni i don't take such kind of things as a joke, kin jini ko?". nayi saurin ɗaga masa kai,"naji Yaya and i will keep it insha'Allah". sai kuma naji voice ɗinsa yayi low a sanda yake cewa,"me kyauna ko dai Jawad bai haƙura da ke ba ne?, karfa ya zamana nayi shuka na gama ban ruwa someone else kuma yazo yaci amfanin gonar". maganar tasa ta haska min hoton abin da ya faru jiya a masarautar bichi da muka je. mahaifiyar Jawad Hajjah Nashwa, ana zazzaune a turakar Bella take cewa,"ni fa har yanzu banga ta inda Maryam ta dace da auren wani bare ba, shi yasa har da ya rage saura kwana biyu ɗaurin aurenta ni da ɗana bamu cire rai da ita ba". Anty Zaina tace,"hmm ai duk mai martaba ne da rashin yin dogon nazari har ya yanke wannan hukuncin, har ma da su Akilan ai. wai su na duba irin halaccin da mutanen su kayi masu, ina wani batun tuna halacci for God sake a inda ake son yarinya ta tsira da mutuncinta...duk wannan rawar jikin da suka ga yaron nayi akanta wallah wataran sai sunyi dakacan ina ma ba su ba shi ita ba. domin wuyarta ta ɓata masa rai zai fanshe ta hanyar tuna mata wacece ita, wallahi wataran sai ya tuna mata da wannan tabon da yake manne ajikinta, amma tsakani da Allah idan ɗan'uwanta ta aura fa, akwai wanda zai fishi ganin ƙimarta da mutuncinta ne?, aiko wani yaji ya goranta ma ta sai iyaka inda ƙarfinsa y