NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 192 of 223

a ƙirjinta nauyi, ta fita a ɗakin cikin hanzari tana jijjiga Abbas dan yay bacci. ba ta kai ga tsakiyar parlon ba kiran sunanta da Yagana tayi ya tsayar da ƙafafunta a lokaci guda. "ga kayan abincin Kabiru can na haɗa, ki ɗauka ki kai masa ɗakinsa". "tom Yagana". sai Yagana ta bita da kallo tare da jefa mata tambayar,"lafiyarki kuwa na ganki kamar a firgice?". tayi saurin girgiza kai da cewan,"a'a babu komai Yagana". Yagana ta kaɗa kai kawai ta wuce ta barta, ita kuma ta nufi kitchen ɗin har tana tuntuɓe. **** *76 Kafe District, Asokoro, Abuja.* "i will definetly teach her a lesson, ni ba shashashar matan nan bace da zan bar ƙawa ta ƙulla alaƙar gaisawa da mijina ko saurayina. ni kika sani dan haka da ni za ki zumunci, so Aisha Tayo tell your that stupid friend kar ta ƙara kiran Yaya ko da sunan menene ma, in ba haka ba kuma wallah zata ga ɗanyen hauka". Shamsiyya Sani da ke daga kan gadona a kwance ta bushe da dariya tana yunƙurawa zaune. "wallah ke dai Maryam anyi masifaffiya, wannan wanne irin kishin jaraba ne. ance miki kiransa fa kawai tayi ta tambaye shi ke saboda tana ta kiran wayarki bata samu ba, amma kinzo kin ishi mutane da bambami". naja tsaki na miƙe daga kan kujerar da nake, na kalli Shamsiyya Sani na banka mata uwar harara kafin nasa kai na fice daga bedroom ɗin, ina jinta ta rakoni da dariyar da ta ƙara ƙular da ni, idan na dawo ciki sai munyi faɗa sosai da ita, to matsalar ina son Shamsiyya. kai tsaye ɗakin Mami na nufa sai huci na ke, su huɗu na samu a ɗakin su na arraging gift ɗin da za'a bada a wurin dinner, baka jin komai sai ƙarar acn da ke hurawa a ɗakin, da alama yanda suke magana a hankali lissafin kayan suke ba kuma sa so ya kubce masu. na nemi bakin gadon Mami na zauna ina aikin ɓata fuska kamar zan fashe. Mami ta waiwayo tana dubana tace,"Auta wa ya taɓan ke?". na ƙara kumbura fuska ina bata amsar,"ba Yaya bane". "to shi kuma Yayan da kansa yau. me ya maki hala?". tambayar tasa na fashe da kuka. Ummi tayi saurin aje kayan da ke hannunta ta iso gare ni. "ke da wa wai? sanin kanki ne bana ƙaunar kukanki". nasa hannu na goge hawayena nace,"to Ummi ki yiwa Yaya magana kar ya ƙara picking call en kowacce shegiyar ƙawata da zata kira shi. kawai yaje ya biyewa wannan banzar Mabrukan sunata waya for morethan 3mints wai da sunan kwatance yake mata. ni nace mata dole sai tazo bikin nawa ne?, ban ma san a gidan uban da ta sami lambarsa ba, dama waccan banzar Shamsiyyar ce ta jajuɓo min ita kuma Allah ita ma kiyi mata magana Ummi". "to yanzu mene abin ɗaga hankali akai. address fa kawai ta tambaye shi ba wani abu ba". sai na ƙara kumbura ina cewa,"bada address ne Ummi for more than 2minutes?, duniyar yake mata kwatance gaba ɗaya ko me?, to ni dai bana son ake jiye min muryan miji, just call him and talk to him in ba haka ba Allah ni mai iya zuwa wurin Daddy ne yanzu nace na fasa auren". Mami tayi guntun tsoki tace da Ummi,"du Allah leave this girl, go and meet Ibrahim outside naji kaman tsayawan motansa". sai na shiga shashsheƙar kuka ina faɗin,"ni nama fasa auren, dan ba zan auri me sauran maganar wata ba". Anty Samiha(cousin ɗin su Mami) ta wurgo min harara da faɗin,"kin tashi kinje kin shirya ko sai na jefo miki wannan plate ɗin...ki wuce kije ki shirya tun kafin azo tafiya kizo kina ɓatawa mutane rai, akanki Maryam ba zan ɗauki faɗan Bella ba kinji na faɗa maki". ina ƙunƙuni nace,"ita wannan Bella ta cika iko, dole ne sai anje inda ta ke sannan za ai bikin, nima ba ga gidanmu ba ta bari ayi a gidan ubana mana. mene haɗina da wani masarautar bichi, kaje ma duk wannan Jawad ɗin ya ɓata maka rai". ina rufe baki Anty Iftihal ta wawuro pillow ta jefo min, nayi saurin miƙewa ina dariya na kaucewa jifan. "ƴar ƙaniya mara kunya, Mahaifiyar tamu kike faɗawa haka saboda kin rainamu ba ki da ta ido a gabanmu". Mami tace,"to ba Kakarta bace, haka za ku yi haƙuri, ni kar a takurawa Ƴata". ina wata dariyar nace,"Allah kam wannan tsohuwan ta isheni, ko da yake kwana nawa ne ma ya rage ma ta Allah na tuba, ta tafi kowa ya huta da mulkinta". Anty Samiha tayo inda nake da plate ɗin hannunta nayi tsalle akan gadon nayi wurin Mami na ruƙunƙumeta. Mami kuma ta kareni ta hanata dukana. Anty iftihal tace,"Maryam kici gaba, rabon kisa nayi adua ne a ɗaura aurenku ku biyu gobe". na waro ido waje ina cewa,"ni da wa?". tace,"ke da kishiyarki". na taɓe baki nace,"Anty Iftihal ba ki da labarin nayi zarra a zuciyar Yaya ne ko". kuma dan ta ƙunsa min sai ta taso da maganar ɗazu, nayi saurin tashi na bar ɗakin ina faman zumɓure zumɓure na koma ɗakina. "ke kuma gorilla you know very well bana ƙawance, da ma ke kika naye min, ƙawata ɗaya ce Basma my sister, so dan haka daga yau na yanke ƙawancen dake, ki tarkata komatsanki ki koma gidanku, bikina ko babu ke za'a yi shi ai dama bani na gayyatoki ba, gayyar soɗi kika zo kuma manzon Allah ma ya hanata". abin da nace da Shamsiyya kenan a san da na shiga ɗakin, amma da yake Shamsiyya ƴar iska ce
🏠