aƙidarsu kuna amfani da ita, tsakani da Allah a tsarinmu mutanen ƙauye Ƴaƴanka nawa yanzu? kai ko kunya baka ji, Aminu yayi, ga Amadu zai yi amma kai wai Yagana ma ce min take ta karatunka kake bata aure ba, to naci uban bokon". kansa a ƙasa yace da ita,"za'a yi Umma, ai lokaci ne". daga faɗin haka ya wuce kai tsaye zuwa ɗakin Nawwaran, yana zuwa kuma ya tarar bata nan sai ƴan ƙunshin kayanta da jakar kayan a tsakiyar ɗakin, da alama tayi wanki ne tana haɗa kan kayan ko kuma ta fito da su dan zaɓan wanda zata saka. jin bai ji motsinta ba a ɗakin ya fito ya koma bedroom ɗin Yagana. tana ganinsa kuwa ta taso tana faɗin,"ɗan albarka ya akai?". yana kanne idanu yace,"ranki ya daɗe babu komai, ganinki kawai nazo yi". sai ta kaɗa kai kawai tana cewa,"ni kuwa kaga jiya gaba ɗaya banyi bacci me daɗi ba. ramar nan taka na bani tsoro Kabiru, duk yanda akai akwai abin da kasa a ranka yake damunka, dan Allah ka taimaka ka faɗa min, na san ban isa na rabaka da ita ba amma zan maka adu'a Allah ya yaye maka koma menene". ya wadata fuskarsa da murmushi a san da idanuwansa suka hango masa Nawwara ta fito daga toilet ɗin Yagana riƙe da wani yaro, alama kuma ta nuna masa wanka ta yiwa yaron tun da gashi nan naɗe cikin zane, ita kuma hannunta da ƙafarta duka da ruwa, ya shafa fuskar Yagana yana faɗin,"Yagana ki kwantar da hankalinki babu abinda ke damuna, idan ma akwai to komai yazo ƙarshe insha'Allah". ba hakan taso ba sai dai bata da yanda ta iya da shi, bata so ta takura masa sam. "to kaci abinci?". yasa hannu yana shafo bayan wuyansa yayinda idanuwansa ke kan ƙafar Nawwara yana bin yatsun ƙafarta da kallo, yace da Yagana. "ban ci komai ba tukunna. na ɗan fita ne sai yanzu na dawo". cikin dabara kuma sai yace da ita,"waccan yarinyar sam bata son tsafta, ana biki kowa na gyara jikinsa amma ita kalleta wani curkuɗe-curkuɗe". ya ƙarasa maganar yana haɗawa da ƙaramin tsoki.
Yagana ta waiga ta dubi Nawwaran da yake magana akai sannan ta dawo gare shi da cewan,"wallah ba laifinta bane...aiki ne ya mata yawa bata zama, kaga ɗazu ma har ta zauna za'a mata ƙunshin kuma wannan yaron sai yasa kuka, shi kuma uwar tazo ba lafiya shi yasa dole ta tashi". a lokacin ji yay kaman ya haɗa uwar yaron da yaron ya yarfa masu zagi, sannan yaywa Uwar yaron kashedin kar ta ƙara saka masa Mata rainon ɗanta tun da ba ita ta haife shi ba, kuma a cikin kuɗin aikinta babu na raino, ba kuma raino aka ɗaukota yi ba.
lokaci guda ɓacin ransa ya ƙaru yana me cewa da Yagana. "jiya ma bata je makaranta ba yauma haka. ɗazu Principal ɗin nasu ya kirani ai...tazo ta sameni a ɗaki su yi magana da shi". Yagana tace,"to Allah yasa su karɓi uzurinta, ni ban san hakan zai zama da matsala ba da ban hanata zuwa ba". shi dai juyawa kawai yay yana daɗa faɗawa Yagana,"ta taho min da kayan abincina".
Kwata-kwata Nawwara bata lura da shigowarsa ɗakin ba, sai lokacin da furucinsa na,"bata je makaranta ba". ya shiga kunnenta. A lokacin ne ta ɗago kai ta gansa, idonta ya shiga cikin nasa, kuma haka kawai ƙwayar idonta ta haska da wani irin tsoro da fargabar da bata taɓa ji ba, bata san ya dawo ba sai cikin dare da ta farka taga kwalaben madarar waken suya acikin leda har guda uku, da kuma tufa guda shida, da bunch na ayaba, kuma a wannan lokacin yunwa ce ta tasheta, dan haka ta tashi Iya dan neman izininta akan taci, tun da babu damar ta fita yanzu neman abinci, ta san ba zata samu ba dan yanzu abinci baya saura a gidan.
ko da Iyan ta tashi ta faɗa mata ai tsarabar Kabir ce da ya dawo, ta tsorata sosai da irin baccin da tayi dan tun sha biyu na rana ita ce sai 11 da rabi na dare ta farka, baccin da zata ce bata taɓa yinsa ba tun girmanta, sai dai taji daɗin yanayin jikinta sosai, wannan ciwon kan ya ɗauke gaba ɗaya, haka duk inda ke mata ciwo ajikinta ya saki, amma tayi mamakin baccin sosai. kuma murɗawar da cikinta keyi yasa ta aje mamakin a gefe ta shiga cin tufar tana korawa da madarar waken suyan, tana sha tana lumshe ido daɗinsa na ratswa har cikin kanta.
fatanta ɗaya ne a yanzu Allah yasa bai ganta ba, dan a yanda ta tsara sai lokacin dawowa daga makaranta yayi zata je ta gaishe shi, kuma jin yace ta kai masa abinci taji wani abu me kama da tsoro shi kaɗai ya dira a ƙirjinta. kallonsa take har ya ɓace daga bakin ƙofar ɗakin sannan ta ɗauke kanta da sauri ta shiga shafawa Abbas mai ajiki, jikinta sai rawa yake kamar wacce ta yiwa sarki laifi, yanayin fuskarsa take tunawa da yanayin furucinsa, da kuma kalmarsa na cewar zai yi mata exams idan ya dawo, me zai faru idan ransa ya kai ga ɓaci yace ya zare hannunsa daga ɗawainiyar makarantarta?, zata iya ɗaukan wannan ɗanyen hukuncin?, tana ganin kamar ƙwallafa ran da tayi akan karatun bokon zai iya mata illa a duk san da akace yau karatun ya datse mata?, ya zama dole ma taje ta ba shi haƙuri tun kafin zuciyarsa ta gama yanke hukunci.
dan haka da sauri ta ƙarasa shirya Abbas ta saɓe shi ta goya shi, daga yanda take nishi zaka gane goyon yaron yayw