NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 190 of 223

ta samu damar yin wanka?, ciwon da ke damunta ya warke?, gajiyar jikinta ta barta?, sannan kuma ya tambayeta me take so?. kwanaki da kwanaki kenan yana jin wani abu na wucewa har zuciyarsa akan yarinyar, ya rasa menene shi, abun da kawai ya sani yana so ya zamana yana kasancewa tare da ita, yana so ta sake da shi ta dinƙa faɗa masa wannan ɓoyayyun sirrikan damuwar da ya lura tana tare da ita tun farkon zuwanta gidan, ya sani ba zai magance mata komai ba, amma zai yi duk mai wuyar da zai yi dan ganin ya rabata da damuwar da mutum zai ke iya tsinta a tare da itan. sai kawai ya kulle idonsa ya buɗe tare da fuzgar da iska daga bakinsa, shi kansa ya san ya sauya 100%, ba ya da walwala a yanzu, ba ya da sukuni, ba ya iya sakewa da mutane, yanayin fara'arsa ta sauya, kullum zuciyarsa matsewa take, forsure yasan ya canja daga Kabir ɗin shekarun baya da yawa, kuma kullum ƙaryata zuciyarsa da Abdulrrahim ya ke akan cewar Soyayya ce ta maida shi hakan, shi ai ba ragon namiji bane, dan haka mace da soyayyarta basu isa su lugwigwita shi ba, basu isa su sauya shi daga Kabir ɗinsa ba, abu ɗaya ne yanzu dunƙule a zuciyarsa, kuma ya kusa kora shi ya wuce da abinda yake ganin shi ne mafitarsa, nan kusa ba sai an kai ga nisa ba, a gobe ba jibi ba. ya sani aure ya ƙunshi abubuwa guda uku; abota, aminci da yarda, sannan so da ƙauna. tabbas waɗannan su ne ginshiƙin aure, in har da su aure zai yi inganci da ƙarko, to sai dai anya ba zai yi kuskure ba akan abinda ya gama yanke tabbatuwar faruwarsa a gobe?, idan shi akwai waɗannan abubuwa ukun to ita fa?. ya sa ni baya tsoron komai goben kawai yake jira, babban fatansa shi ne Allah ya kai kowa lokacin. ya kai hannu ya ciro wayarsa da ke ringing a aljihunsa, bai ɗaga ba sai da ta kusa tsinkewa kana ya kai kunnensa yana yin sallama. Akila ta amsa masa yanayinta babu yabo babu fallasa. "are you coming to Abuja?". "no Ummi". "but why?". "just like that". "but you will attend the dinner party ok?". bata jira cewarsa ba ta ƙara cewa,"Kabir i want to you to go to the dinner party please, don't say you will not go". to dama me ta ke tunanin zai hana shi zuwa?, zai je forsure, wata ƙila ma Dinner ɗin ta tashi ata mutane biyu, mutane ɗayan da aka shirya da mutane ɗayan da ba'a shiryawa ba. Ya rufe murfin idonsa sannan yace da ita,"zamu zo insha'Allah Ummi". "kai da wa?". "mu biyu". Akila na miƙawa maid wasu kaya tace,"are you sure Kabir?". kaman yana gabanta ya gyaɗa ma ta kai,"ehh Ummi indai ba zai wuce nan kano ba zamu zo". Akila ta sauke numfashi daga inda ta ke kafin tace masa,"ananne mana za ai, komai ai a masarautar bichi zamu yi tarukan bikinmu". bai ce da ita komai ba yay shiru yana sauraron bugun zuciyarsa da ke harbawa da sauri-sauri. ta katse shirun nasa da faɗin,"Kabir jikina sai yake bani kaman zaren wata ƙaddarar zai gifta kafin ɗaurin auren nan". nan ma bai ce komai ba yay shiru. ta ƙara cewa,"na kasa yardarwa kaina ba zaka mallaki Maryam ba. Kabir mai yasa ba zaka fito ka faɗawa su Baba abin da ke ranka ba?". yay wani gajeren murmushi a saman leɓensa sannan yace,"zan iya faɗa musu hakanne kaɗai idan Ahmad yace ya fasa kuma baya son Maryam. amma muddin Ahmad na sonta ba zan taɓa iya buɗewa kowa zuciyata ba yaga abin da ke dangane da Maryam ba. Ummi hatta raina zan iya sadaukar da shi akan ƙannena balle kuma wata aba soyayyar mace. dan Allah ina so ki manta da na so ƴarki, haka kuma ki daina kawo faruwar wani abu a ranki da zai hana auren nan domin ina son farin cikin ɗan'uwana, ni na cire soyayyar Maryam a raina tuni, zan kuma tabbatar miki da hakan wata ƙila a gobe". Tayi murmushi mai sauti sannan tace,"kai ma kasan ba zan taɓa yarda da batunka na cewan ka daina son Maryam ba, duk wannan fiffizgewar da kake ƙarfin hali kawai kake, dakiya ce irin taka ta jaruman maza, amma yanayin maganarka kaɗai ya isa ya ƙaryata kalamanka, kuma kaman yanda na faɗa maka sam sam bana farin ciki da auren nan kamar yanda kai ma baka farin ciki da shi". "Ummi ya za'ai ki faɗi hakan. taya zanƙi farin ciki da auren ɗan'uwana, gaba ɗayanmu fa alkhairin auren nan muka nema, kullum cewa kike Allah ya bani ita idan har ita ce alkhairina, to tun da kika ga hakan ta kasance Allah ne zai mana sauyi mafi alkhairi tsakanin ni da ita". yana gama maganar ɗiff yaji ta katse wayar. sai kawai ya girgiza kai, sannan ya fara tafiya sannu a hankali har ya kai ga parlon Yagana, yana shiga hayaniyar mutanen da ke zazzaune a parlon ana ta hira ta shiga kansa, ta ke yaji wani ɗan ƙaramin ciwon kai na neman kama shi, saboda haka ko tsayawa cire takalmansa bai yi ba ya gaidasu a tsaitsaye, da yake duk ƴan'uwana sai suke ta masa tsiyar ƙaninsa zai yi aure ya barshi, shi dai murmushi kawai yay bai ce musu ƙala ba, har wata Yayar Malam ƴar wan Babansu tace da shi,"Allah Kabiru kaji mun faɗa maka tazarar aurenku ba zata wuce wuta guda ba, wannan ai sai ya zama hauka, so kake ka zama tuzuru...ni shi yasa sam ban so wannan karatun nasaran ba, ga shi nan kun ɗauki
🏠