NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 19 of 223

nu ta kaudani gefe, duk da bata kallona amma haka na murguɗa mata baki sannan nace,"wai ke Kulu baki san kin girma bane, sai kita wani shishshige min ala dole sai nayi ƙawance da ke, akan mene na aje kaya zaki zo ki ɗauka ki wanke sai kace na saki, wannan ma ai shishshigi da ƙwala kai a faranti ne, to ni dai bana so karki kuma min irin haka ba ruwanki dani da al'amurana dan bana kula mahaukata irinki...". Ɗiff bakina ya ɗauke ganin ta Ɗaga hannu a zafafe zata tsinkeni da mari, ban san me ya hanata ba naji ta sauke hannu, ta ƙarasa shanya zane sannan ta juya ta bar wurin, in da ni kuma a lokacinne na ɗago ina binta da kallon mamaki, abunda idanuna suka ci karo da shi a wuyanta shi ya ɗauki hankalina, abu ne kamar tambari na tauraro baƙi, kasancewarta fara ƙal gashi nan raɗau kana kallonsa, sai da ta ɓacewa ganina sannan na sami damar haɗe murfayen idona ina son tuna in da na taɓa ganin wannan tambarin, na fi daƙiƙa biyar a tsaye acikin wannan tunani sannan na buɗe idona, tabbas idan ba a wuyan Gwaggona ba to a wuyan Jawad ko shi ko Suhail ko kuma Ya Kabiru na taɓa gani. na ɗan ciji yatsana, to amma kuma ai kamar wannan tambarin an taɓa nuna shi a tv a masarautar larabawa, kenan ananne na taɓa gani irinsa?, kai bayan nan ma kamar na taɓa gani a tsakanin mutum huɗu nan da na ke zargi, ɗan ƙaramin tsaki nayi dan sai yanzu na tuna ma ashe a wuyan Basma ne, har nake tambayar Gwaggo ko ƙonewa Basma tayi tace a'a baiwace, nima kuma a lokacin har na ɗau madubi na duba nawa wuyan, da yake hasashe ne nake sai naga kamar nima ina da shi, da na bawa Gwaggo ta duba min sai tace kar na isheta da shirmen banza. Sai da na ɗauki kayana na kuma wankesu sannan na wuce ɗaki, dan acewata wankin Kulu ƙazanta ne, tunda ban taɓa ganin tayi ba sai yau ɗin. Ko da naje ɗakin Inna Amarya sai tace naje wurin Gwaggo, a ɗarɗarce dai na shiga ɗakin Gwaggo sai rakuɓewa nake, ƙasan zuciyata ina ta biya_"dinkimma dinkim Allah ya kafe bakinki"._ dan ni saukar bugu kawai nake jira daga wurinta domin nasan tana sane da komai, jira kawai take Allah ya kawoni kusa gareta ta zartar min da ɗanyan hukunci. "idan kin gama raɓe-raɓen ga kaya can a leda ki ɗauka ki saka, karki sa wando sai kin manna waccan abar". Gwaggo tace dani tana ficewa daga ɗakin. Na ƙarasa na buɗe ƙatuwar baƙar ledar da ta min nuni da baki, na zazzage kayan ciki a ƙasa, na shiga ɗaga kayayyakin ɗaya bayan ɗaya ina dubawa, dogayen riguna ne da nake ganinsu ajikin labarawa idan munje kallo gidan Liman da azumi, a ciki kuwa harda shigen wadda likitar da tayi min allura ɗazu a asibiti ta saka, kalar shuɗi da fari da wasu azababbun duwatsu ajiki masu shegen kyau da ɗaukar ido, murmushi kawai nake wani sanyin daɗi da farin ciki na baibayeni, babu tantama wannan siyayyar Ya Kabiruna ce, gaba ɗaya rigunan guda uku ne, duk da ban san farashin kaya ba amma da gani kasan kuɗi ne ba ƙarami ba a wannan siyayyar, to amma aina Ya Kabiru yake samun kuɗi kwana biyu? aikin me ya samu?. Tunanina ya katse a sanda naji an kamo hannuna an miƙar dani tsaye, Kulu ce riƙe da hannuna da tattausan hannunta me matuƙar kashe min jiki a duk lokacin da ta taɓani da shi, kallona take da dara-daran idanuwanta wanda na kasa ɗauke ganina acikinsu, ban taɓa kallonta ido cikin ido ba, amma yau saboda tsananin kyawun da nagani acikin ƙwayar idanunta sam na kasa daina kallonsu duk da kwarjin da suka yi min, Magana take min da ido wadda tsab na karance me take nufi, saboda hakane na natsu ina dubanta da abunda tace na maida hankalina akai, wani madaidaicin kwali ta ɗauko a wata leda ta daban dake gefen wadda na buɗe, ta buɗe shi ta ɗauko wando ɗan ciki(pant), ban taɓa ganin irinsa ba dan irinmu Ƴaƴan Malam Audu na ƙauye ba irinsu muke sawa ba, gajere muke sawa irin na tsaffi wanda ake cewa bantai. Kallon yanda take min bayanai da hannu nake yi, ta ɗauko irin abar da naga an rabawa su Adawiyya kwanaki a makaranta, ta ɓare ledarta ta zaro ɗaya ta manna ajikin wandon, sannan ta miƙo min. "me zan yi da shi?". Na tambayeta cikin muryata da tayi sanyi. A yanzunma dai da ido ta bani amsa, ganin zanyi gardama a maganartata yasa ta zare min ido har saida na firgita na rungumeta ita kuma ta tureni daga jikinta, ina ɓata rai na saka wandon ajikina wanda ya kamani tsam, naji wani banbanci na daban. Tana ganin na saka ta bar wurin, na bita da kallo ina maimaitawa kaina anya Kulu mahaukaciya ce?, ko kuma anya asalin Kulun dana sani a gidan nan ce ba masayen wata akayi ba?, ta ɗaga labule zata fita nace, "kiyi haƙuri da kalmar dana faɗa miki ɗazu". Shuɗiyar doguwar rigar na ɗauka na saka, na ɗaura ɗan yalolon mayafin dake tare da ita, kamar an gwadani kamin a siyo, inata duban kaina acikinta ina zullumin shigowar madubina gidan yazo ya gane min kyan da nayi, ni tun ina ƙarama ban san nayi kwalliya na duba madubi ba, Ya Kabiru shi ne madubina. Daga tsakar gida na jiyo Adawiyya na ƙwala min kira, na ɓata fuska nai saurin tattara kayana na
🏠