NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 189 of 223

yay dariya da cewa,"Kai dai Habib anyi munafuki. shi yasa ban so kazo ka tare a gindina ba, ba dama nayi waya da matata kunnenka na wajen". Habib yace,"ni wane sa'ido ne baka min ba a lokacina". Shuru ya ratsa ɗakin na tsawon wani ɗan lokaci, hakan ya bawa sautin tv'n da ke kunne damar fitowa sosai. Jim kaɗan Mubarak ya yunƙuro zaune yana cewa,"Yauwa! ya maganar zuwan Umar M. Shariff wurin dinner?". Habib ya kalle shi yana ba shi hankalinsa da cewan. "naso jiya mun sake komawa da Saifullahi office ɗin Umar M Shariff ɗin, amma yau Mai Shadda yace muje around 4 mu same shi sai muje can office ɗin nasa tare, tunda akwai fuskar sani ai ba yayi denying zuwan ba". "Yauwa hakan ma is oak, dan ina son zuwan gayen nan wajen wallah, ina matuƙar ƙaunar waƙoƙinsa over". Ahmad ya ɗan muskuta kaɗan a inda ya zauna yanzu sannan yace,"kuna ta batun M Sharif banji kuna maganan zuwan Moh-bad ba, after all kun san da cewan shi Mai Kyau tafi buƙatan zuwansa wurin". Mubarak yace,"sha kuruminka angon ƙarni, wannan ai su Jemi sun gama magana da shi, har kuɗin buking nasa duk sunyi payment tun last week". Ahmad ya ƙara cewa," ƙwamma hakan dai kam. a burge Matata da Ƙawayenta shi yafi, ba wai taku buƙatar ba". ya numfasa sannan yaci gaba da cewa,"ni ina ta jibi, ita tana ta gobe dinner, ai na faɗa mata ta shiryawa jibin nan a jarumarta". Habib ya kai hannu ya doki kafaɗar Ahmad yana cewa,"Ango sarkin zumuɗi, me kana ci na baka na zuba ne. kaman yaune fa, kuma wannan daren dai da ka ƙwallafa rai akansa kaman yanzu ne". dukansu kuma sai su kai ƴar dariya, kuma a wannan lokacinne Nawwara ta turo ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta shigo. daga bakin ƙofar ta duƙa ta gaida su sannan ta wuce kan ƙaramin table ɗin da ke daga can gefe ta aje tray ɗin flask ɗin abincin da ta shigo da shi. sannan ta ƙarasa ta bawa Ahmad wayarsa tukunna ta fita ta bar ɗakin. tana shiga parlo taji landline na ƙara, ta ƙarasa da sauri ta ɗauka domin bata manta da maganar Kabir ba. tana ɗagawa deliver Man ke sanar mata yana bakin gate, tace ya bawa mai gadi sannan ta shiga ɗaki ta ɗako hijab ɗinta ta fita taje ta amso. tabbas a duniyarta bata taɓa ganin mutum mai nutumci, karamci, tausayi, mutuntawa irin Ya Kabir ba, hakan yasa mutumin ke daɗa shiga ranta a kullum, kuma har abada ba zata manta da shi da alkhairansa gareta ba, kamar yanda a kowacce sallah ta kewa kanta adu'a haka shima ta ke masa, kuma kaman yanda ta kewa kanta adu'ar samun miji na gari haka shima take masa adu'ar samun mata ta gari. tasa fork ɗin da ke hannunta ta datsi naman gandar da ke cikin takeaway tare da yin bismilla ta kai bakinta...tana fara tauna ta lumshe ido saboda daɗin ɗanɗanon da ya ratsa harshenta da bakinta, taci green banana salad ɗin kaɗan, sai bayan ta gama tama sha ruwan swan ɗin da ke haɗe sannan ta lura da maganin da ke wata farar leda ta daban, ta ɗauko shi tana duba sunansa da akasa provigil, sai kawai tayi murmushi ta ɓalla ta sha guda ɗaya kaman yanda taga an rubuta ba tare da tasan ko maganin menene ba. sai dai tana sha ɗin bayan ta fito daga wanka sai ta ɓingle akan katifarta bacci ya ɗauketa, haka iya ta shigo ta dinga tashinta amma bata tashi ba, ƙarshe Yagana tace a ƙyaleta ta huta dama ta gaji ai da yawa. *Please Comment, Share & Vote.* [7/18, 10:10] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *(46)* *8:30am na safiya.* "ina Nawwara?". Kabir da ke tsaye a bakin entrance na parlon Inna Zulai ya jefa tambayar ga Jamila. "Yaya ba zata wuce part ɗin Yagana ba". sai ya zare hannunsa na dama da ke zube cikin aljihun wandon suite ɗin da ke jikinsa, ya sose gemunsa a san da yake kallon sashin Yagana, ya ɗauki kusan daƙiƙa uku yana kallon sashin kaman baƙonsa, nazari da tunani yake akan ta yanda zai iya shiga part ɗin Yaganan da yake ɗinke da jama'a ƴan taron biki da suka zo, ya ratsa su ya wuce zuwa inda zai sami Nawwara ya kamo hannunta ya fito da ita, yay ɗakinsa da ita ta shirya acan sannan ya ɗauki mota ya fita da ita zuwa inda ya gama tsara zai kai ta a gyarata kaman kowa, abin da ya tsara a jiya kenan da zarar ya dawo. sai dai abinda ya hana faruwar hakan tun a jiya baccin da tayi, lokacin da ya dawo tana bacci bata tashi ba, kuma ko da ya shiga ɗakinta ya taɓa jikinta sai yaji da ɗumi da alama ma akwai zazzaɓi jikin nata, wanda ya lura da hakan tun a lokacin nan da yake waya da ita. idanuwansa sun kalleta tar kuma sun fallasa masa yanayi ne na ƙarfin hali takeyi saboda babu yanda ta iya, matsayin ƴar aiki ta ke a gidan bata da batun cewar zata huta kaman yanda ta ke so, hakanne yasa ya haɗo mata da wannan maganin saboda bacci me nauyi ya ɗauketa, ta yanda duk irin tashin da za'a yi mata ba zata san ma ana yi ba, sannan ya saukar mata duk wata tarin gajiye da ke tare da ita da ma sauran ciwukan da ke jikinta. kuma abin da zai iya cewa shi ne tun a daren jiyan zuwa yanzu da yake tsaye anan hankalinsa da tunaninsa na kanta, yana kan son sanin a wanne hali ta ke ciki, taci abinci?,
🏠