NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 188 of 223

eyeee?". muryarsa a ɗage yake maganan kuma cikin faɗa, tuni idonta ya ciko da ruwan hawaye ta shiga girgiza masa kai, ta kuma kasa cewa da shi komai. yaci gaba da faɗan yana cewa,"kar ki sake wannan hawayen su zubo". ya ƙara faɗa very loadly, hakan yasa tayi saurin sa hannu ta maida hawayen. yace,"idan na dawo zan miki exams, idan kika kasa zan sami amsar tambayoyina anan, kuma za ki kalla mai zan maki". a raunane tace da shi,"dan Allah Ya Kabir kayi haƙuri, wallah yau ne kawai banje ba". ya doka mata tsawa,"comon shut your mouth up". sai tayi shiru kaman yanda shi ma yay shirun, can kuma yay nisa yace,"ke me yasa ba'a maki ƙunshin ba?". tace,"mutane sun yiwa mai ƙunshin yawa, tace na bari zuwa gobe idan ta gama yiwa kowa sai ta yi min". sai ya saki guntun tsaki na haush yace,"ita ɗaya ce me yin lalle a duniya?". tana girgiza kai tace,"a'a, Yagana ce dai tace ita zata yi mana". tayi maganar duk a tsorace saboda yanda taga duk ya rikiɗe nata zuwa wani Ya Kabir ɗin na daban, wancan mai sanyi ne amma wannan a zafafe yake. tana cin jinsa ya ƙara cewa,"kuma ita mai ƙunshin da aka ɗaukota sai akace idan ta gama yiwa kowa na gidan ta tsallakeki ta gama yiwa baƙin da suka zo kafin ke ɗin ko?". bata ba shi amsa da baki ba ta girgiza masa kai kawai. ta ɓangarensa yay shiru yana janyo leɓensa na ƙasa cikin bakinsa, ya tsotsa for 1minutes sannan a hankali muryarsa ta fito da cewa,"kar ki wanke gashin, ƙunshinma ko da an ce kije ayi miki karki je. ki jirani na dawo, am on my way, in the next 5hours zan iso insha'Allah, be ready da na dawo zamu fita". murya na rawa tace,"to Allah ya dawo da kai lafiya". sai taji yace,"tsorona kike ji ne?". tayi saurin kaɗa masa kai alaman a'a. "to ɗago ido ki kalleni kiyi adu'an". ta ɗago tana kallonsa tace,"Allah ya tsare hanya, ya dawo mana da kai lafiya, ya kareka da kariyarsa". "ameen ya Rahman...thanks to you. ki nemi abinci kici kinji ko, idan hidiman bikin yasa baku tanadarwa cikinku komai ba ki jira a parlo zan taking maki order yanzu". "ai zuwa anjima za'ai girkin". bai bi ta kan maganar tata ba yace, "me kike son ci?". ya tambayeta with full of concern. tace,"Yaya ba sai ka kashe kuɗi wurin saya ba. aiki ne ma ya min yawa shi yasa ban samu naci ba, yanzu da na gama yankan farcen zan ci". a lokacin da take maganar ji yay kaman ya zura hannu ta cikin wayar ya fizgota zuwa gabansa, yay mata kashedin muhimmancin cikinta a wurinsa da kakkausar murya ko ta samu ta shiga hankalinta tayi masa shiru da wannan surutun wofin. kuma a yanda ita ma take kallon idonsa tana iya hangowa da a kusa da ita yake zai iya ma ke bakinta. ta cikin shirunsa da yay yana jifanta da wani hargitsatstsan kallo maganarta ta kutsa ciki da faɗin. "Yaya zan ci abincin". fuska a haɗe kamar hadari yace,"me za ki ci?". "komai aka samu Yaya". sai ya gyaɗa kawai, ba tare da yace komai ya kashe wayan, kuma kashewan nasa yay dai-dai da shigowan Basma ɗakin. "ba sai ki faɗi mani Ya Kabir ne a waya ba kuma kawai sai ki bani ki wuce". Basman ta cuno baki tana miƙa mata hannu da cewar,"oho ni nayi zaton kin gane nufina". Nawwara ta ɗau wayan ta miƙa mata jikinta a sanyaye. Basma ta kuma cewa,"Yarinya kuma yanzu Yaya ta zo". wannan fargabar da Nawwara keji tun a ɗazu ta gushe jin ambaton Maryam tazo , ta miƙe cikin jin daɗi tana faɗin,"tana ina?". "see you kika wani miƙe, to ai har ta tafi". Basma ta faɗa tana dariya. "are you serious?" "wallah, ita da Ummi ne fa, kin san sai yau ta dawo daga Qatar ɗin, kamin su wuce Abujan Ummi tace bari tazo ta gaida Baba". Nawwara na murmushi tace,"Allah sarki Yaya naso na ganta wallah. anyway sai gobe ma haɗe a wurin dinner, Allah yasa dai aje da ni". "karma ki saka ran zuwa, saboda gidan duka za'a daɗe Yagana ma tace sai taje". sai kawai Nawwaran ta gyaɗa kai da rashin jin daɗi a ranta, ta fita domin ci gaba da aiki. tun da ƴan biki suka fara zuwa bata zauna ba, duk da cewar akwai iya yanzu da suke aiki tare wadda Kabir yasa aka kawo ta ke tayata aikin, ba damar ta zauna waccan zata bijiro ma ta aikinta, tun ma masu ƴaƴan nan, ita ce wankin kashi, wankin kayan yara, ga ƙawayen Adawiyya ma motsi kaɗan sa ƙwala mata kira. hakanne yasa duk jikinta ke ciwo babu abinda ta ke so a wannan lokacin irin tayi wanka ta ɗan miƙe ko yane ta huta, to amma ita da hutawa sai in kowa bacci yay a fidan. **** Habib da ke daga kishingiɗe akan 3seater ɗin ɗakin Ahmad, ya ɗan waiwayo kaɗan ya kalli Ahmad ɗin da ke shafa oil akan askin da yay a ɗazu. Yace,"Ahmad tela ya kawo sauran kayan nan kuwa?". "kai bama dolensa ba. kayan fa da zan saka ne gobe a wajen dinner". Mubarak da ke gefe ya fashe da dariya sannan ya ce,"Daren farko mai sanya zumuɗin angwaye. Ahmad na lura gaba ɗaya a ƙagauce kake da zuwan jibi, gaba ɗaya tun da akace an wayi garin yau ka kasa sukuni". Habib ma na dariya yace,"kai baka jishi bane da muka dawo daga masallaci, ya dokawa Maryam ɗin kira da sanyin asuba wai Mai Kyau 2days remaning fa ki zama mallakina". Ahmad
🏠