a ta dakatar da shi da faɗin,"kaga kar ka jama min musiba riƙe salatinka da kake ƙoƙarin jaa tun da ni dai Rakiya ba annoba bace....wai Kabiru ko sai ansa dalma an zana sunanka a goshina sannan zaka tabbatar da cewar kafatanin jikokina kai nafi so, to ban ma sa ni ba ko sanin hakan yasa kake galabaitar da sauran numfashin da ya rage min, to matuƙar na mutu Ubanka Adamu ka yiwa ba wani ba". sai kuma tayi shiru taci gaba da kukan. ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace,"kiyi haƙuri Yagana". "yo haƙurinka ko cuta Kabiru, tsakani da Allah watanka nawa baka gidan nan? ka ɗauki ɗabi'ar banza ta miskilanci ka ɗorawa kanka kana neman katange kanka ga kowa, yanzu abin da ban gane maka ba nake so naji shi ne bikin ma ba zaka zo ba kenan? kuma sai yaushe zan kuma ganinka a zahirance ba'a wannan hoton gajimaran ba, dan na gaji da ganinka a wannan iskar nasaran, ka yiwa Allah da ma'aikinsa ka dawo naji ka a kusa dani na sami natsuwa da kwanciyar hankali".
"Yagana yanzu haka ma fa tahowa zanyi me zai hana ni zuwa biki. kiyi haƙuri dan Allah nan da mintina kaɗan jirgin namu zai taso". kawai sai fuskarta ta washe da fara'a ta shiga saka masa albarka da masa adu'ar isowa lafiya, kamin nan suka yi sallama ta bawa Ahmad wayar tana juyawa ga Inna Zulai tace ma ta ai maza a daddafa duk abin da aka san Kabiru naso kamin ya dawo.
"ka bawa Basma wayar please". abin da Kabir yace da shi kenan san da yake fitowa parlo. Ahmad ya kira Basma ya miƙa mata wayar da cewan idan ta gama ta kawo masa ɗaki. "Ya Kabir ina kwana". "lafiya lau Basma, ya kike ya shirin biki?". "mu na tayi Yaya, yaushe zaka dawo? ko ba zaka zo bikin ba?". "anjima zan sauka insha'Allahu". "tom Allah ya dawo da kai lafiya. Ya Kabir kar ka manta da kit ɗin makeup ɗina dana ce maka". "insha'Allahu Basma ba zan manta ba. ina Nawwara?". "tana kitchen tana aiki". sai kawai ya ɗan rumtse idonsa for a while kafin ya buɗe yace,"je ki kai mata wayar". tayi knooding masa kanta sannan ta nufi hanyar kitchen ɗin, ko da taje kitchen bata sameta ba dan haka ta nufa ɗakinta, zaune ta sameta kan carpet tana yanke farce, gashin kanta a barbaje wanda ta gama tsifarsa babu jimawa. Nawwara ta tsaya da yankan farcen tana kallonta har Basma ta ƙaraso ta miƙa ma ta wayar ta juya ba tare da tace ma ta komai ba, ita kuma ko da ta karɓi wayar sai ta ajiye a gefenta taci gaba da yankan farcen, har a sannan Kabir bai yi magana ba, kallonta kawai yake yana mai hango irin tarin gajiyar da ke tattare da ita.
bayan ta gama yankan farcen ta ɗago hannu tana dubawa ta gefen idonta sai ta kalla kaman mutum, hakan yasa tayi saurin juyowa ta kai idonta kan wayar gaba ɗaya. sai tayi saurin waro idanuwa waje tana dubansa da mamaki, sannan tasa tafukan hannunta ta rufe bakinta tana faɗin,"kaii". tayi maganar a irin wadda ta gama cika da mamaki.
"Ya Kabir ai ban shina ba wallah, bata faɗi mani kai ne a waya ba kawai bani tayi ta juya, ni kuma nayi zaton ajiya ta ban". bai magana ba sai ƙare mata kallo da yake for some seconds sannan yace,"me ya sami gefen bakinki?". ta kai yatsa tana taɓa wurin kafin tace,"huciyan zazzaɓi ce". "when kika yi ciwon?". "an kwana biyu". irin yanda yake mata maganar da kuma kallon da ya tsareta da shi duk sai ta ji ta kasa sakewa. ta miƙa hannu ta janyo ɗankwali zata rufe kanta taji yace,"kar ki saka". hakan yasa ta dakata tana mai ƙara saukar da kanta ƙasa cike da kunyarsa na yanayin da take na rashin ɗan kwali.
"wanne magani kika sha?". "su na da yawa har da allurai ma. Yagana ce ta kai ni asibiti". tayi maganar still idonta na ƙasa tana wasa da yatsunta, sai taji yace,"ba da gashinki nake magana ba da kika wani hasko min shi gaba ɗaya, ki ɗago min fuskarki ki min magana ko na kashe wayata". bata san mene ba amma haka kawai sai taji wani abu ya harba ta zuciyarta, ta ɗago da fuskarta gaba ɗaya ta ɗan dube shi sannan ta ɗauke idonta. "an gama alluran?". "ehh an gama". "magungunan fa?". "suma sun ƙare na gama sha". "amma me yasa ita huciyan zazzaɓin bai warke ba?". "ai zai warke gaba ɗaya sai a hankali". kaman a tsoroce take da shi a yanda ya lura, ya sauke numfashi da sake tambayarta,"tun yaushe kike aiki da kika tara gajiya haka?". sai tayi saurin ɗago manyan idonta tana dubansa da tsananin mamaki, ƙwarai da gaske ta gaji, gajiya ma iya gajiya amma taya akai yaga hakan shi?. ya katse tunaninta da faɗin,"why din't you go to school today?". taji me yace amma ba zata iya mayar masa a cikin harshen ba, dan kamar yanda ya faɗa mata ne in yay mata magana da hausa to da hausan zata mayar masa, hakana inda english ne ma. sai tayi shiru bata ce komai ba. "am asking you, you kept quite?". sai taji wucewar wani abu ta maƙoshinta kafin nan ta kalle shi da cewan,"aiki ne yay yawa a gidan shi yasa". "ke ɗaya kike aikin dama? ita iya ina ta ke? dan me aka ɗaukota? ba dan saboda ta karɓeki ba a time ɗin makarantarki. ko kuma dama can asarar kuɗina nake ba zuwa makarantar kike ba?, da kika san ba kya son makaranta why can't you tell me