da ka ƙara haɗa special mood ɗin da nake ciki da Maryam, na rantse maka Abdurrhim sai na sassaɓa maka kamanni, sai na bar maka mummunan tabon da ba zaka iya shaida kanka ba...i told you, don't stop talking to me about someone's wife kaga yanda zan faffasa maka baki". a fusace yake maganar kamar zai kaiwa Abdurrahim ɗin duka, kuma shirunsa yay daidai da buɗe idon Abdurrahim ɗin ya kallesa sau ɗaya yana mai sauke guntuwar dariya a saman fuskarsa, kan yaja tsaki yace,"in ka fasa fasan baki Kabir". gaba ɗayansu kuma sai suka saki ƙwafa a tare, shiru ya gimla tsakaninsu na wasu ƴan daƙiƙu, sai sanyin acn da ke dukan jikinsu, kuma a wannan shirun na shuɗewar daƙiƙu biyu Kabir ya jera guntayen tsaki sunfi biyar, Abdurrahim da ya gaji ya ɗago a harzuƙe yana cewa,"dilla Malam ni ka isheni da wannan tsokin naka. ai bani na kar zomon ba dan haka sai ka bari idan ka hau jirgi ka ƙaraci yin abinka acan, amma ni ka dameni". sai kuma yaja gajeran tsaki yace,"you know i totally forgot". yay maganar yana mai zira hannunsa a aljihu ya zaro wayarsa. "what do you forget?". Kabir ya tambaye shi yana kallonsa a sa'ilin da ya buɗe baki da zummar sauke masa bala'in da ke cinsa.
"I was at the reception Yagana called me, she wanted to speek to you. tana ta kiran naka wayan a kashe".
"swithh off?" ya tambaya in surprise trying to pick up his phone from his pocket. "to ni dai haka tace min". Abdurrahim ɗin ya ce ya shiga whatsapp yana serching numbern Mu'azzam ya danna voice call daga nan ya miƙawa Kabir.
wayan bai jima yana ƙara ba Mu'azzam ya ɗaga, daga can ɓangaren Mu'azzam ya gaida shi sannan Kabir yace ya miƙawa Yagana wayar idan yana gida. abin da ya ɗaga hankalin Kabir lokacin da Yagana ta karɓa kukan da ta fashe da shi, ƙirjinsa ya buga, fargaba kuma ta dirar masa. ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya kan yace da ita,"Yagana lafiya? me ya faru?". maimakon amsar da ya zata daga bakinta sai yaji ta kuma rushewa da wani kukan, dan haka yay saurin katse kiran ya ɗauko tasa wayar ya kira Ahmad hankalinsa a tashe. "Kana gida?". daga can ɓangaren Ahmad yace masa,"ehh ina gida amma ina shirin fita yanzu. i heard your voice full of anxiety, what happened?". Kabir yay ɗan jimm bai ce komai ba, dan ko a iyaka muryar Ahmad ɗin ya tabbata ba wata matsala bace a gidan, rigima ce ta Yagana kawai, and now he can undertand the reason for her crying.
"Kabir kayi shiru, me ke faruwa dama?". tambayar Ahmad ta katse masa shirunsa, ya fitar da numfashi sannan yace da shi,"ba komai, ka kaiwa yagana wayar zanyi magana da ita. vedio call zan kira so on your data". Ahmad ɗin yace da shi "to" ba dan ya yarda da cewan ba komai ɗinsa ba, duba da yanayin yanda yake maganar very cool.
A bedroom Ahmad ya tadda Yagana zaune a gefen gado ta duƙar da kai sai kuka ta ke yi, Inna Zulai da jikokinta sun zagayeta, da kuma ƴan'uwanta waɗanda suka fara zuwa biki tun a shekaranjiya da biki ya rage saura kwanaki huɗu.
"mene ya faru?". ya tambaya yana ƙarasawa bakin gadon gefen da mahaifiyarsa ke tsaye. "uhmm wa ya san me aka ma ta, tun ɗazu dai ta ke kuka, kai tunda ta tashi ma zance maka. kuma anyi tambayar duniya taƙi cewa komai". ya daɗa maida dubansa ga Yagana yana cewa,"Hajiya Yaganata menene? ko dai ni ne ba ki son rabuwa da ni kawai na haƙura na tare acikin gidan?". sai yanzu taji maganarsa dan haka ta ɗago kai ta dube shi da cewar,"Yauwa ɗan aljannah zo zauna nan". ta faɗa tana masa nuni da kusa da ita. "kukan na menene? ko duk saboda zan miki kishiya ne?". sai kawai tayi murmushin da za'a iya kiransa da na dole kuma na yaƙe sannan tace,"yo ni meye ruwana da amaryarka, me zai ɗagan hankali akan wata kishiya bayan nasan naci gida na kuma gama siye zuciyar mai gida, mtswww ni Allah sauƙe nayi kishi da waccan abar". yay guntun murnushi shi ma yana cewa,"faɗi gaskiya dai". tace, "kaga bar batun wannan sillan karan amaryar taka, kira min Kabiru a wayanka, na kira shi da ta Mu'azzam yaja min tsaki ya kashe". tayi maganar with serious face. yana kunna data kuwa sai ga kiran Kabir ɗin, ya ɗaga miƙa ma ta, a kallo ɗaya da ta yiwa idanuwansa ta kuma rushewa da kuka tare da zabga salati kaman wadda aka yowa aiken mutuwa. Kabir ya matse idonsa yana cewa,"dan Allah dan Annabi ki bar ɗaga min hankali da wannan kukan naki". "to Allah ya jiƙan rai Ubana Manniru nayi shiru". ta faɗa tana sa gefen ɗankwali ta share hanci. ya so yin dariya amma kuma sai ya gimtse yana cewa,"kin san abin da hawayenki yake haifar min ai". tace,"ina kuwa zan sani Kabiru tun da na san ba ƙaunata kake yi ba, Kabiru idan so ka ke na mutu to ka aiko kawai a kashe ni ka huta da jin numfashina a duniyar nan, tun da ka tsaneni baka ƙaunata. wallah Kabiru a yau ko gobe ko jibi ko wani watan na mutu to kai ne ajalina, na faɗa maka wannan sabuwar halayyar taka ita zata zama ajalina saboda zuciyata ba zata ɗauketa ba, duba fa yanda idanuwanka su kayi loko, ga yanda ka rame, ka zuge ka zaftare kaman ragowar yaƙi". ganin yana motsa baki zai magan