na mijin, Na biyun kuma na matar, sakamakon kuwa irin ƴaƴan da za'a samu su ne: (1). AA +AA = AA, AA, AA, AA, za'a samar da ƴaƴa masu cikakkiyar lafiya. (2). AA + AS = AA, AS, AA, AS, shi ma aure ne mai kyau kuma babu matsala a lafiyar ƴaƴan da za'a haifa amma bai kai na AA+AA ba. (3). AA + SS = AS, AS, AS, AS, shi ma wannan auren ana iya yinsa duk da akwai ƴar matsala kaɗan akan ƴaƴan da za'a haifa zasu zama AS ne duka ma'ana carriers. (4). AS + AS = AA, AS, AS, SS, akwai matsala domin za'a samu ɗa ko ƴa mai cutar sikila. (5). AS + SS = AS, SS, SS, SS, a wannan gaɓar akwai matsala sose domin kusan kaso 80 na ƴaƴa zasu zama masu cutar sicler ne. (6). SS + SS = SS, SS, SS, SS, inda matsala mai muni ta ke, domin dukkan ƴaƴan da iyayen sicler ne, zasu ƙare ne cikin tsanani da wahala na rashin lafiya...Idan aka lura da waɗannan matakan duka, ba shakka za'a kawo raguwa ko ƙarshen cutar amosanin jini wato sicler da ta ke galabaitar da waɗanda suke ɗauke da ita, kuma ta wannan hanyar kaɗai ake iya maganceta kamar yanda ta nan ta ke samuwa. Allah ƙara mana lafiya ya kuma bawa marasa lafiyanmu lafiya"._
gama bayanin matar yay daidai da shigowar kira cikin wayata, nayi saurin ɗauka hannuna na rawa bisa rashin sanin dalilin hakan ganin cewar Bro Almustapha ke kirana. na kara wayar a kunnena ina jin wani irin faɗuwar gaba matsananciya, na rumtse idanuwana na kasa yin sallamar da ta kamaceni nayi.
"Littile". ban amsa kiran sunan nasa ba sai da na haɗiye wani abu ta maƙoshina da ya wuce da ƙyar sannan nace. "na'am Bross". "kina jina ba, ki buɗe wannan box ɗin da na baki ranar dana zo, akwai wani blue envelop da sunan asibitin da muka je da ke, ki ɓare shi ki duba min menene genotype ɗinki, gaba ɗaya na manta ban duba ba a ranar, kiyi da sauri". na miƙe ƙafafuna na rakani da ƙyar har zuwa bakin dressing mirrow, na tsuguna na buɗe drower na ɗauko box ɗin da ya bani ajiya ranar da zai wuce london, na buɗe kamar yanda yace na shiga karanto masa cewar, "Bross AA ne". sai yace da ni,"oak". kamin ya katse nayi saurin cewa da shi,"Bross ka tambayi Ya Ahmad nasa, ina kiran wayansa ban samu ba kuma Dad yace na kira shi nace yana jiran result ɗinsa". da alama daga inda yake lemu ya kurɓa kamin ya ban amsa da cewan,"no ai nasan ma yana wajena tun wancan ranar da Mami tace na amso". cike da fargaba nace,"Bross shi mene nasa?". nayi tambayar da rawar murya. "result ɗinku is the same, shi ma AA ne". kan na ƙara cewa wani abu ya katse kiran. katse kiran da ya sa na jefar da wayata na faɗa kan gado ina kanƙame pillow dan murna.
zuciyata faɗa min take a yanzu ba wata fargaba, babu wani ƙalubale, babu wata damuwa, komai ya kau, aurenmu zai tabbata, Maryam da Ahmad za su tabbata ma'aurata, Maryam da Ahmad zasu kasance a matsayin abu guda, wannan tazarar da ke tsakaninmu zata haɗe a wani dare ta tabbatar damu matsayin mata da miji.
*Vote,Comment and Share plss🙏.*
[7/18, 09:32] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*(45)*
*Ethiopia.*
*Addis Ababa Bole International Airport*
*NOTHING GONNA CHANGE MY LOVE FOR YOU.*
_"if i had to live my life without you near me the days would all be empty, the nights will seem so long with you i see forever, oh, so clearly. i might have been in love before but it never felt this strong, our dreams are young and we both know they will take us where we want to go, hold me now, touch me now, i don't want to live without you...nothing gonna change my love for you, you ought to know by now how much i love you..."._
Abdurrahim da ya shigo motan ya kai hannu yay reducing volume ɗin waƙar da ke tashi a cikin motar, Kabir da ke kwance ajikin kujerar motar ya buɗe idanuwansa da ke a lumshe ya saukesu akansa, kallon Abdurrahim ɗin yake da irin kallon dalilinsa na rage masa volume tun da ba shi yake jin waƙar ba, haka kuma motar ba tasa bace balle yay masa iko da abin da ke cikinta.
Abdurrahim ya shafo sumar kansa tun da ga ƙasan ƙeyarsa zuwa sama sannan shi ma ya jinginar da kansa jikin kujerar motar, kafin kuma ya kai hannu ya kwantar da kujerar shi ma yana sauke ajiyar zuciya.
"gashi, in the next 25mints jirgin zai tashi". ya faɗa yana miƙawa Kabir wata farar takarda. Kabir ɗin ya karɓa ya aje sannan muryarsa ta fito a hankali da cewan,"ka sami damar maida min da volume yanda yake ko kuwa?". idanuwan Abdurrahim na kulle yace da shi,"kana da damu Kabir, wai mene amfanin earpord ɗin da ke kunnenka?, ka maida waƙan kaji kayarka kai ɗaya mana tun da ta zame maka waƙi'a farilla. ni wannan waƙoƙin soyayyan ciwon kai suke samin kasan da hakan amma sai kayi ta shiga da hakkina, muji a gida muji a mota haba abin ai yay yawa. ni wannan Maryam ɗin ma ai jaraba ce agareka". Kabir ya gyaɗa kai sau biyu ba tare da ya ce masa komai ba, sannan ya ɗago daga kan kujerar gaba ɗaya ya kai hannu ya kashe waƙan duka, a zafefe yay kan Abdurrahim da cewa,"duk ranar da ka ƙara min zancen Maryam, duk ranar da ka ƙara alaƙantani da Maryam, duk ranar