NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 184 of 223

akan tafin hannun Ya Ahmad da ke tallaɓe da haɓata, kafin naji laɓɓana sun furta,"Ya Ahmad na amince zan aureka". furucin da ya fito a hankali kuma suka shiga raɗau a kunnuwan kowa da ke wajen. sai kuma naji zuciyata ta matse, irin matsewar da ban taɓa ji ba, har ina jin kaman zata faso allon kirjina ne ta fito ta tarwatse a ƙasan gabana. babu zato naji Ya Ahmad ya ƙara janyoni jikinsa ya kwantar da kaina saman chest ɗinsa yana furta min kalman,"thank you". da alama ya manta da mutanen da ke wajen balle yaji kunyarsu, ko kuma yana ɗaya daga cikin mazan da basa shayin nuna soyayyarsu akan abin da suke so a gaban koma wane. a wannan lokacin idona na kan Ya Kabir ne da ke kan kujera kusa da Ummina, kansa yana kan wayarsa yana shafawa, farin hannunsa tar acikin hasken fitilun da suke gauraye a parlon, kallon zoben hannunsa nake da ƙyallin haskensa ke hasken ido a duk san da na kalla na yatsana da ya saka min tun kafin Mairo tasan wace ita. a wannan lokacin babu abin da nake so sama da Ya Ahmad ya sakeni na ƙarasa gaban Ya Kabir, na duƙa a gaban ƙafafunsa, na miƙa hannuna na riƙe nashi ko ya samu ya tsaya daga karkarwar da naga yana yi a yanzu, nasa ɗayan hannuna na ɗago da fuskarsa na ƙarewa wannan handsome face ɗin nasa kallo kamin nace da shi ya buɗe idanuwansa da suke a kulle ya faɗa min damuwar mece nake gani a saman fuskarsa da tayi yawa haka. idan da so samu ma na kwantar da kansa a ƙirjina na dinga shafa sumar kansa har zuwa san da zai sauke ajiyar zuciya ya buɗe laɓɓansa yace min Maryam komai ya gushe, babu damuwar, babu ɓacin ran, komai ya tafi, na daina fushi da ke, zan dawo asalin Ya Kabir ɗinki. ashe abin da ban sa ni ba shi ne, wannan kallon da nake masa har nake ayyana wasu abubuwa shi ne zan iya kira da kallo na ƙarshe, dan tun da Ummi tace,"Masha'Allah, Ahmad na baka auren Maryam". Baba kuma yace,"Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa". Yagana kuma tai guɗa, kunya kuma tasa Ya Ahmad ya sakeni. a wannan sandarewar da nayi ina kallon lokacin da Ya Kabir ya taso kaman a fusace, ya kuma zo ya wuceni kaman wucewar guguwa, na kuma ji san da zafin hucinsa ya sauka ajikina kaman garwashi, na kuma ga dawowarsa parlon bayan fitar da yay ta mintuna 2, ya miƙawa Ya Ahmad key ɗin dana ji ƙararsa ya dawo ya kuma wuceni a zafafe. daga wannan fitar, kuma wannan ranar ban ƙara ganinsa ba, har muka baro bichi muka koma abuja bayan bikinsu Mami, na taho makaranta, akasa ranar bikinmu naje ethiopia nayi kwanaki duk ban sashi a idona ba haka ma muryarsa. sai dai abin da har zuwa yanzu ban gane ba shi ne me na yiwa Ya Kabir a rayuwa?. da naga kamar banda damuwa da hakan kawai sai nayi wancakali da Ya Kabir daga duniyata, na ƙanƙamo ƙaninsa na riƙe, kuma zazzafar soyayyar da Ya Ahmad ke nuna min ta mantar da ni ma wani abu Ya Kabir da Rayuwarsa, alwashi ɗaya da na san na ɗaukarwa kaina shi ne, ko bayan aurena da ƙaninsa ba zai ga fuskata ba a matsayina na matar ɗan'uwasa, haka ma ba zai sami girmamawan nan ba ta sirikantaka balle ta ƙanwa...domin tuni na riga na gano musabbabin dalilinsa na fita a harkata, na tsanata da ya ɗorawa kansa, ai da hankalina, komai ya sauya ne tun daga ranar da ya san wace ni, ranar da kowa yasan sai da akayi zina aka samar da Maryam, illigitmecy shi ne dalilin tsanata da Kabir yay, kuma banga laifinsa ba dan irinmu abin a ƙyamata ne, sai dai abin da bai sa ni ba shi ne wannan shegiyar da yake ƙyamata a yanzu yana cin arziƙinta ne ta wani ɓangaren, don haka kaf duniyata Kabir na ɗaya daga cikin mutanen da bana ƙauna. bayanin da naji matar da ke cikin tv na kwararowa su suka yanke min tunanin da nake yi, na baro tunanin bichi da abin da ya faru a cikinta, na dawo qatar da kuma abin da ke wakana yanzu a cikinta, na tattara hankalina gaba ɗaya ina sauraron abin da balarabiyar matar ke cewa a tashar aljazeera cikin harshen larabci, kuma tun a kalamar Genotype ɗin da ta ambata allon ƙirjina ya girgiza sakamakon tunawa da saƙon Daddy. _"Dukkan ɗan Adam Allah Ya halicce shi ne tare da wasu ƙwayoyin halitta waɗanda su ke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake, ƴaƴa su na samunsu ne daga irin nau'in wanda iyaye suke da shi, idan iyayen suka zama da nau'i mai kyau, za su haifar da ƴaƴa lafiyayyu, idan aka samu akasi kuma za su haifi ƴaƴa masu rauni da matsalar Amosanin jini wadda ake cewa cutar sicler...Masana sun raba genotype zuwa kaso uku da suke cewa: homozygous dominant, homozygous recessive, da kuma hetrozygous. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, wanda daga gwajin ake samun Genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda 3 kamar haka,  AA, AS, SS...AA su ne masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa Carrier, akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukunsu ne SS masu ɗauke da amosanin jini wato Sicler saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura...Abu mai muhimmancin da ya kamata a lura kafin aure idan an duba genotype ɗin su ne kamar haka: Rukunin farko wato
🏠