kuma a lokacin ido kawai nasan na iya binsa da shi, ba tare da laɓɓana sun motsa ba har na furta masa wata kalma. Aure! Aure! a wancan lokacin ban bawa Alhassan amsa bane saboda nasan maganar da yayi ba magana bace mai yiwuwa, sai kuma gashi a yau ɗin kuma a yanzu ba Baba bane da kansa, ɗansa ne da kansa a gabana, yake neman yardata akan aurensa, a gaban Baba da Yagana, haka zalika a gaban Ummina da ke jiran wannan lokacin.
Ya Ahmad! Ya Ahmad dai mutumin da shi ya kaini makaranta, da kuɗinsa na fara karatun boko, to shin dama ni wacece da har zanƙi amsar wannan tayin nasa? na girgiza kaina a hankali zuciyata na faɗa min cewar Maryam ke ba butulu bace. ko da baice min ya fara sona ba tun a ranar da ya san haƙiƙanin alaƙar da ke tsakanimu, zan amincewa aurensa ko da a yanzun nanne yaji ya fara sona, ko da za'a min auren dole da Ya Ahmad bana sonsa ba ya sona tabbas zan zauna da shi, tun da har ya kasance shi ɗin jinin Baba da Yagana ne.
na taɓa cewa Alhassan da Mami duk wani abu da zai sa a binciko asalina to ina gudunsa, zan kuma kaucewa duk wata hanya da zata zama sanadin hakan, dalilin bincikar asalina yasa bana sha'awar yin aure kuma na cire ran yinsa har ƙarshen rayuwata. Abin da Umm ta faɗa min a wannan lokacin shi ne,"Maryam idan har za ki ci gaba da dasa wannan abin a ranki to kuwa kina tare da ɓacin rai har ƙarshen rayuwarki, ki manta da komai tun da komai ɗin nan ya rigada ya wuce, ki fuskanci sabuwar rayuwa da kika shiga a yanzu, kiji daɗinki da kwanciyar hankalin da kika samu...kuma abin da nake so na jadddada maki shi ne Aure ko kina so ko ba kya so Maryam sai kinyi, saboda haka ki tsayar da zuciyarki akan Jawad muddin da gaske kina tsoron duk wani abu da zai tono asalinki, dan shi ne wanda ba zai taɓa goranta maki ba, shi yafi dacewa dake a yanda kike, saboda haka ki yarda ki zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya ke da shi tun da acikin danginki yake...idan ba ki sa ni ba ma ki sa ni Jawad ba tun yanzu ne yake sonki ba, tun ranar da ya fara ɗora idonsa akanki yaji yana so ya aureki, ba tare da ya duba banbancin da ke tsakaninki da shi ba, abu ɗaya ne kawai ya jinkirtar da shi akanki Maryam, karatunki! kuma a yanzu da komai yazo a gaɓar da ya tsara, ya furta miki ya kuma sanar da Mai Martaba dan haka ki yiwa kanki karatun ta natsu ki tsaida zuciyarki da tunaninki akansa, ina ƙara faɗa maki da Jawad kaɗai za ki kasance ki tserar da kanki daga wani ƙalubale na asalinki".
ofcourse i know rayuwar aurena da Jawad ta dace dan shi ne rufuwar asirina, to amma a yanzu da nake tsaye gaban Ya Ahmad bana tunanin ko wannan mutumin da Ummi ta bani labarinsa ne zai zo wurin nan a yanzu ya furta min da bakinsa cewar zai aureni zan amince masa, wannan mutumin da Ummi tace ya so ni tun kamin na zama cikakkiyar mace, ya ɗau shekaru goma yana ƙaunata duk da yasan wace ni, ya ɓoye hakan a ransa da zuciyarsa ba tare da ya furta min ba, ba wai dan son da yake min yana da tangarɗa ba, a'a sai dan saboda tsananin soyayyar da yake min, gudun kar ya buɗe min zuciyarsa rayuwata ta faɗa cikin garari idan na gane wace ni, Ummi ta faɗa min tun kafin na san asalina na fara zubar da hawaye shi yake zubar min da nasa, hawayen da yake yinsu akan abu biyu, tausayina da kuma tsananin ƙaunata. mutumin da yace mata ko daga sama aka jefoni zai aureni, ba zai gujeni ba, ba zai taɓa ƙyamatata ba, illa ma yayi dukkan mai yiwuwar da zai yi ya gusar da duk wani dattin baƙin ciki daga zuciyata, ya tsaya min tsayin daka wajen ganin banyi kuka ba dai-dai da second 1, burinsa shi ne kawai yaga laɓɓana na talewa da murmushin farin ciki da jin daɗi a kullu yaumin, ya mantar da ni ƙalubalen da ke cikin rayuwata, ya faɗa mata ya ƙara nanata mata rashina zai iya yiwa zuciyarsa illa._
_"son Maryam zai min illa idan har na rasata Ummi"._ waɗannan kalaman kullum su yake faɗawa Ummi cikin raunin zuciya. kuma a wannan lokacin da Ummi ke ban labarin mutumin da ban san da shi ba naji ina sonsa, har na iya ce mata tace da shi yazo ga Maryam tasa ce.
sai dai a yanzu ko da shi ɗinne yazo bana jin idanuna zasu iya kallonsa ma ballanta har na miƙa masa zuciyata nace zan aure shi, naji ya so ni tsawon shekaru goma, kuma ya so ni tun ban zama mace ba, ya ƙaunace ni duk da ya san asalina, amma a wajena nafi ganin girman soyayyar da aka fara yi min ita cikin lokaci kaɗan, soyayyar da bata haura watanni biyar ba, soyayyar Ya Ahmad ta fiye min duk wata soyayya bayan ta iyayena.
"Maryam abin da nake so kawai ki faɗa masu shi ne kin amince za ki aureni, ki bar batun kina sona ko ba kya sona ko taya za ki fara sona, zanji da wannan agaba, ni zan koyar da ke soyayyata idan mun kasance a inuwa ɗaya".
maganar Ya Ahmad ɗin ta katse min duk wani tunani nawa, kuma maganar tasa da ta ƙara ɗauke komai da ke cikin kaina, wani dunƙulallan abu ya tokare min a ƙirji. _"Halacci! Halacci Maryam!"._ harafai biyun da suka dira a raina kenan, ban san taya akai ba sai kawai naji saukar hawaye a saman kumatuna, na sauke ganina