NOVEL SHARES -
akina ina tsotsa da tarin murmushin da ya ƙi barin fuskata, ji nake ajikina tamkar Yaya nah na rungume ba wayar da ke ɗauke da saƙonsa ba. kuma ta ke hoton wannan ranar ya shiga haska min acikin idona, wannan daren ranar da Ya Ahmad ya buɗe min zuciyarsa, ya tona min sirrin da ke shimfiɗe a cikinta a game dani da soyayyata.
wannan daren da ya sameni da Al'ameen a parlo muna hira, saurayina da ya min proving soyayyansa a computer school ɗin da na shiga kafin na baro bichi, kuma a wannan daren ne zuwansa na farko gida da izinin Baba da Yagana, amma zuwan Ya Ahmad ya wurin ya tarwatsa zaman fahimtar junan da muke shirin yi ni da Al'ameen.
a gaban Yagana, gaban Ya Kabir, gaban Basma da Inna Zulai, gaban Ya Aminu da Baba, gaban Ummina, gaban kusan kowa na gidan. ya jawoni daga kan kujerar da na ke zaune gefen Al'ameen, ya tsayar da duga-dugaina a gabansa, dab da shi sosai, ya kama dukkan hannayena biyu ya ɗora saman ƙirjinsa, saitin zuciyarsa, wani abu da ya haifar da tasirin da na ji kamar zanyi fiffike na tashi sama.
wannan lokacin da nake a dab da gabansa, hannayena saman ƙirjinsa, sai nake jin zuciyata a lokacin kamar fayau ta ke babu komai acikinta, na kasa haɗa ido da kowa na kuma kasa kallon gefen da kowa yake, sai haɗiyar wani yawu nake a maƙogarona da ke wucewa da ƙyar, kafin daga bisani naji ƙafafuna na neman gaza ci gaba da ɗaukata, dalilin wannan harufa biyar da Ya Ahmad ya furta min.
_"Maryam za ki Aure ni?."_
*Plss Comment,Share&Vote.*
[7/17, 08:47] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*(44)*
"Maryam za ki aure ni?". tambayar ta ƙara fitowa kamin rufewar idanuwana da buɗesu.
bai nisa ba ya ƙara cewa,"Dan Allah kice min eh, kice musu kin amince, ki faɗawa kowa kin yarda dan Allah. na gama shirya rayuwata da ke Maryam, duk wani plans nawa na gaba na gama tsarasu da ke, wallah ina sonki, kuma so nake na aureki. i cant imagine this life without you Maryam, tun daga ranar da komai ya bayyana kika samu muhalli a zuciyata, i love you, i love you so much". harufan ƙarshen suka fito tare da ɗauke hannuna da yake daga saman ƙirjinsa ya sarƙe yatsunmu wuri guda ya damƙe hannuwanmu sose, ya kafe ni da idanuwansa da haskawar wani abu da ban taɓa gani ba a ƙwayar idon wani mahaluƙi.
ina iya jiyo yanda ƙafafuwana suka shiga rawa a wannan lokacin, da yanda jikina ya ɗauki kyarma gaba ɗaya, naji wucewar wani dunƙulallan abu ta maƙogwarona da ban san mene shi ba, a lokaci guda murfayen idona suka haɗe, wani duhu kuma ya shiga haskawa cikinsu, sannan a hankali kuma kalaman Ya Ahmad su shiga maimaituwa cikin kaina. _"Maryam za ki Aure ni? aurenki nake so nayi, i love, i love you so much."_ maimaituwa kalaman suke kaman a lokacin ne yake faɗa min su, ƙara shiga suke ta cikin kaina da tunanina da wani irin tasirin da ke ratsa ko'ina a jikina. iyaka abinda na sani a lokacin shi ne Al'ameen kawai nake so, kuma ko a halin da nake ciki kalaman Al'ameen ɗin da na Ya Ahmad ke kamanceceniya suka gauraye su na amsakuwa a kunnena.
sannu a hankali sai naji duka kalaman Ya Ahmad ɗin sun gushe daga tunanina, zuciyata kuma ta shiga harbawan da zan iya rantsewa na kusa da ni su na iya jiyo sautin ƙararta. na buɗe rufaffun idanuwana na ɗorasu akan fuskar Ya Ahmad da har yanzu bai ɗauke idonsa akaina ba, fuskarsa cike da fargaba, kallona yake da irin tasirin shigar wani abu ta babban yatsan ƙafata zuwa tsakiyar ƙoƙon kaina.
_"na rasa da me zamu biya waɗannan bayin Allah'n da suka mana halacci a rayuwa, Maryam na rasa da me zan saka masu."_ maganar Ummi ta haska a cikin kaina, a washe garin ranar da ta dawo daga india. idan ban manta ba abin da laɓɓana suka furta mata a lokacin shi ne,"Ummi ai mun biya su, ko su bana tunanin su na ƙara saka ran wani abu daga garemu, mun saka masu da abin da basu taɓa haskowa kansu ba". kuma tun daga lokacin da na buɗe baki na fara maganar kallona ta ke da murmushi a fuskarta, har san da nayi shiru ta ɗora da cewan,"Maryam gidan nan da muka basu gani na ke kaman bamu basu komai ba har yanzu, gani nake dama can sunfi ƙarfinsa, Maryam so nake ace yau sun bijiro min da wata buƙata tasu a wurina da zan iya basu kai tsaye, su nemi abin da nasan ina da shi, abin da nasan bai fi ƙarfina ba...". kuma a lokacin bata ƙarasa faɗin abin da zata ce ba Alhassan ya tari numfashinta da faɗin,"Ummi ko Maryam suka nema za ki iya ba su?". kuma ina iya tunawa da amsar da na ba shi a lokacin na cewan,"ai dama ni tasu ce, har abada tasu ce ni". yace,"ina nufin fa Baba ya nemawa ɗaya daga cikin yaransa aurenki, za ki amince Maryam?". abin da Alhassan ya furta kenan,