NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 181 of 223

dan na lura ba kya iya controlling harshenki a duk san da kike cikin yanayi na ɓacin rai, kinga aure za ki yi, idan ni na ɗauka ba lallai mijin rufin asirinki ya ɗauka ba". sai na kaɗa kai nace,"zan kula insha'Allah". "yauwa Allah yay maki albarka". shiru ya gimla a tsakaninmu na wasu ƴan sakanni, kafin tayi min tambayar da na iya amsa mata da ƙyar saboda kunya. "ba muyi maganar da Umminki ba, ai na Ahmad ɗin yace za ku zauna?, lagos ɗin ko kuma a kano?". "Lagos ɗin yace, idan ya sami hutu kuma sai muke zuwa kano". "hakanma yayi, to ya batun tsarin gidan ya faɗa miki?". na ƙara yin ƙasa da kaina cike da kunya nace,"ehh hoton yana wayata". "to sai ki turawa Daddynki, ɗazu yace yanata kiran wayarki zai tambayeki. duk da Umminki tace ita zata yi sayayyar komai. kin san Mai Martaba ya baku gida ma anan?". nayi saurin ɗago da kaina ina kallonta, kafin na girgiza kai nace,"a'a Mami". "ɗazu ya bawa Yayanki Almustapha key ɗin gidan, yace ya bawa Ahmad ɗin idan sun haɗu". na shafa gefen fuskata a hankali kamin nace,"Allah sarki Abi an gode Allah saka da alkhairi, Mami ki masa godiya". ta ɗan harareni da wasa kan tace,"tun da ni ce bakinki ko". sai kuma ta ƙara cewa,"me za kiyi yanzu?". na ɗaga kaina sama na kalla agogo sannan na sauke nace mata,"mu na da test har uku gobe, zan duba littafaina". ta gyaɗa kai,"to yayi, ai karatu da yawa. bari na ƙyaleki idan kin gama sai ki sameni a ɗakina, dama saboda ke na fasa komawa gida, dan haka daga yau har zuwa ranar da Umminki zata miƙa ki ɗakinki lokacina gaba ɗaya naki ne". murmushi kawai nake yi, na sakko akan gadon na dakatar da ita taga fitar da za tayi. "Mami ba ki sa sarƙar ba". da murmushin da bai bar fuskarta ba tace,"yanzun kuma za'a ara min kenan?". nasa hannu a fuskata cike da kunya sannan na kamo hannunta ta tsaya a gaban madubin, na ɗaura mata sarƙar sannan na ɗora haɓata saman kafaɗarta muna kallon juna ta cikin madubin, muna sakarwa juna ƙayataccen murmushi, tare da haskawar tsantsar soyayyar da muke yiwa juna a cikin ƙwayar idonmu. "kin yi kyau Mamina, kin haska sarƙar". Alhassan ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya tsaya daga bakin ƙofar yana kallonmu cike da burgewa, ba mu juya gareshi ba, shi ma kuma bai yi magana ba sai da ya gama kallon namu sannan yace,"gwara dai ma kiyi auren ki tafi ki ƙyalemin Uwa". baki kawai na murguɗa masa bance komai ba, ya ƙwalo min biron da ke hannunsa na kauce ya sauka akan wuyan Mami, Mami tace da shi,"ya maka kyau Alhassan". "yi haƙuri Mami". tace,"ai ba wani abu bane, indai ƙwalowa mutum abu ne kar ka daina kaci gaba, zanyi maganinka wataran tun da kai baka san alkunya ba". yay dariya yana cewa,"yi haƙuri Hajiya Mami". "ka dai ci gaba kaji, garin jifan mutum da abu ka jefa ka sami Ubana, to nima kuwa da izinin Allah zan rama akan ubanka Major, ko da yake Allah ba azzalumin bawansa bane gashi yau da kanka ka rama min akaina, amma duk da haka ka sani sai dai idan ban sami abin jifa ba, sai na jefi goshin Major da shi yayi ƙwalele". ya rufe bakinsa yana dariya yana faɗin,"wa yaga goshin Dad yayi tsini". ta girgiza kai tana faɗin,"Allah ya gyara min kai, yanzu ya akai?". sai ya dubeni yana faɗin,"wai ke me ya sami wayarki?". nace,"me ka gani hala?". "Dad ne yace yanata kiranki tun ɗazu a kashe". sai na sa hannu na rufe baki na nufi wayar ina faɗin,"laaa wallah na manta na kashe sim ɗin, Na Yaya ne kawai a kunne". yaja tsaki kamin ya taɓe baki ya haɗa da faɗin,"to dai yace ki kira Ya Ahmad ɗin ki faɗa masa ya kawo masa result ɗin genotype ɗinsa". ban san dalili ba haka kawai naji allon ƙirjina ya girgiza, na ɗago na dube shi da sauyin yanayin da fuskata ya samu nace,"me za'ai da shi?". yace,"ki kira Dad ɗin ki tambaye shi tun da bani nake nema ba". daga haka yasa kai ya fita a ɗakin. Mami kuma tace,"dama tuntuni ba'ai wannan gwajin ba?". nayi shiru ban iya cewa komai ba, dan yanda naji jikina yay sanyi a lokaci ɗaya. sai ta fita tana faɗin,"to ki kira shi da sauri ki sanar masa kin san halin Daddynki sarai ba ya son delay". na ɗauke idona daga bayan ficewarta, na haɗiye wani abu a maƙogorona da ban san mene shi ba, kamin na iya neman wuri na zauna. nasa finger print na buɗe wayar, kuma ta ke fuskata ta washe da annuri sakamakon cin karo da saƙon Ya Ahmad da nayi, wani taraddadi dann ji yana neman mazauni acikin zuciyata ya washe, na shiga karanta text ɗin nasa da haskawar hoton fuskarsa acikin idona. _"I am in you and you in me, mutual in divine love. Saying it a thousand times won’t be enough to express my feelings towards you, but I’m going to keep saying it nevertheless- I love you! I will keep loving you till the end of my days, no matter what lays ahead of us Cutie nah, waiting and eager of the day, wannan ranar, a wannan daren da Ummi zata damƙa hannunki a nawa tace Diman Da'iman Ahmad..."._ sai na rungume wayar a saman ƙirjina na kifa kan gadon, na haɗe murfayen idona waje guda na lumshe, sannan naja leɓena na ƙasa na shigar da shi cikin b
🏠