NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 180 of 223

banta, tana tsaye bakin dressing mirrow ɗina tana maƙala sarƙata a wuyanta, sai nayi murmushi kamin na tashi zaune na dubeta ta cikin madubin da ƙwayar idonta ke kallona ta cikinsa. nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsuna nace,"Ummi ce ta saya min". murmushinta me ƙarfin sauti ya fito kafin tace,"na sa ni ƴar gidan Mami, aro za'a bani please". sai na ɗago kaina ina dubanta ta cikin madubin kamar yanda ta ke dubana nace,"duk yawan sarƙoƙinki sai kin ɓige ata aro Mamin Alhassan, wannan fa me ƙaramin kuɗi ce ba dai-dai da sawarki ba ce". ƙwayar idonta ƙyam akaina, talewar da leɓenta yay da murmushi tun ɗazu har yanzu tace,"na sa ni ƴar gidan Ummi, yau ɗin banjin saka nawan ne, na aro na keso, na aron ma wannan, ko ba za'a bani bane?". na ɗauke idona daga ƙwayar idonta na kaishi ƙasa sannan nace,"kar ki taɓa min abina, ki aje min ban ba ki izini ba". ba kallonta nake ba, amma ina jin san da ta zare sarƙan daga wuyan nata ta buɗe akwatunta ta saka, sannan tace,"kiyi haƙuri na taɓa maki kaya ba tare da neman izininki ba, ba zan ƙara ba insha'Allahu". na ɗago fuskata da tayi shaɓe-shaɓe da hawaye cikin ƙanƙanin lokaci, na kalla har ta kai bakin ƙofa zata buɗe ta fice daga ɗakin, sai na maida kaina ƙasa nasa tafukan hannuna na rufe fuskata, kuka ya kuma ƙwace min. sai naji tausassun hannunta akan nawan su na ƙoƙarin buɗe fuskar da na rufe, daga nan kuma ta janyoni jikinta gaba ɗaya ta rungumeni tsam wanda har ina iya jiyo bugun zuciyar da ke harbawa a ƙirjinta, a hankali ta ke shafa gyararriyar sumar kaina da ta sha gyara, bata hanani kukan da nake ba har sai da na gaji dan kaina na tsaya, na tsayar da kukan a sa'ilin da na shiga mata magana cikin shashsheƙar kuka. "Mamina...". ban iya cewa komai ba wani sabon kukan ya kuma zuwar min. sai naji ta sauke ajiyar zuciya a hankali kamin ta fara magana. "na sani Maryam, Na san dalilin hawayenki. ba ki min laifin komai ba, Maryam kunyarki nake ji shi ne dalilin da ya sa nake kasa sakewa da ke". na ɗago kaina daga jikinta ina dubanta nace,"Mami wacce iriyar macuciyar kunya ce wannan da za ki bari ta kassarar da ƴarki? Mami ba zan yarda da wannan furucin naki ba, saboda haka kar ki yaudareni da batun cewar wai kunyata kike ji shi yasa kike yakice kanki daga gareni, ba don mu biyun da kika haifa duk ta dattin hanya kika samar damu ba, da sai na ce ba kya ƙaunata ne saboda kin haifeni a shegiya, amma tsakani da Allah meye banbancina da Alhassan da ni ba za ki iya bani soyayyarki da kulawarki ba?, ko kuma dan shi ya taso a cikin gata da daula ne, ni kuma na rayu cikin karkara, na rayu a ƙazantaccen wurin da kike ganin ba za ki iya tarayya dani ba, to bari kiji, wallahi summa tallahi ƙauyen bichi ya fiye min wannan daular masarautar taku sau dubu miliyan, ina ƙaunar bichi fiye da wannan ƙasar taku, nafi ganin kyanta akan wannan wajen da rashin rayuwata acikinsa ya hanani samun soyayyar uwata...ba komai Mami, na gode da iya amsawar ma da ki kai na cewar kin haifeni, Allah sarki Gwaggona, Allah ya jiƙanki da rahma ya haskaka ƙabarinki, na tabbata ko babu soyayyar wata uwa a gareni a duniyar nan, tunawa da iyaka tata da na samu ma kaɗai ta isheni nayi farin ciki muddin rayuwata, ballantana ina da Ummi, wacce ta sadaukar da jin daɗin rayuwarta dan ganin na rayu, ta hana kanta jin daɗi da walwalar duniya duk saboda kada na shiga damuwa ko da na sakan ɗaya". sai kawai ita ma naga ta shiga zubar da hawaye daga idonta, kuma ta ke hankalina ya kai ƙololuwar tashi, hakan yasa na tsayar da maganganuna, na shiga kaɗa mata kaina da sauri ina kama fuskarta ina goge hawayen, sai ta kuma rungumeni muka shiga kukan tare, kukan da bana komai bane sai na huce takaicin da zuciyoyinmu ke ciki. "ki yafe min Maryam". muryan Mamin ta fito a hankali, a hankalin da ya haifar da tsargawar jin wani tsananin tausayi da jinƙai na mahaifiyata. "ni ba ki min komai ba Mami, dan haka ki daina neman yafiyata, ni ce dai zan nemi yafiyarki, na kuma roƙeki da Allah nima ki sammin soyayyarki da kulawarki, ko da ace bai kai kwatankwacin yanda kike nunawa Alhassan ba". "Maryam kenan, ba ki san cewar nafi ƙaunarki akansa ba. ba za ki gane bane, you are still a baby, shi yasa gaba ɗaya kika kasa fahimtata, Maryam ina kunyarki ne idan na tuna ta irin hanyar da na samar da ke, amma kiyi haƙuri ki yafe min, nima bana jin daɗin yanda na ke mu'amalantarki, kuma daga yau na daina, insha'Allahu, zan nuna miki dukkan so da ƙauna da kulawa muddin rayuwata, ƙila ma har kice Mami wannan soyayyar ta fara isata, domin za ki dinga ganinki ne kamar jaririyar da ke shan nono...kin yafe min ɗin?". ban san lokacin da wani murmushi ya suɓuce min ba, na kaɗa mata kai, sai ta ɗago da fuskata sama ta sumbace ni a goshina da kumatuna, kamin ta furta,"ina sonki Maryam, ina tsananin sonki". nima nace da ita,"nima ina sonki Mamina". ta kamo hannuna ta riƙe acikin nata, sannan murya a hankali tace,"idan kina cikin fushi ki daina magana kinji, ki dinga bari sai kin sauko,
🏠