NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 223

faɗan da ta-ke yi kamar bada ita ba, ta motsa laɓɓanta sannan ta ɗaga labule ta fita daga ɗakin. Jikina sakayau na farka, sai ƙasan cikina da nake jinsa dai a ɗaure kaɗan, muka haɗa ido da Gwaggo wadda ke zaune tana ƙarawa Basma karatun ƙur'ani, kallo ɗaya tayi min ta ɗauke kai, bata kuma waiwayoni ba sai da ta sallami Basma, ba tare da ta kalla inda nake ba tace, "ya sauƙin jikin?". Na ɗan yamutsa fuska nace, "naji sauƙi, ƙasan cikina ne dai yake murɗawa kaɗan". "sannu Allah ya sauƙe". Shi ne abunda tace dani kawai. Na sauko daga saman gadon, jinin da naga ya wanke min gefen zanena yasa a gigice na koma nayi zaman dirshen a kan gadon, na fara rarraba idanu kar Gwaggo ta ganni, gashi yana zubowa ta gefen ƙafata, ban san lokacin da kuka yazo min ba nayi saurin saka hannu na toshe bakina, jikina ya hau ɓari, yarfe hannu nake a zuciyata ina kiran mutuwa tazo ta ɗaukeni, _"na shiga ukuna."_ itace kalmar da nake ta nanatawa cikin kaina, tabbas na miƙe Gwaggo tayi ido huɗu da wannan abu sai dai ta sake haihuwar wata Mairon, domin abunda nake tunawa wata hira dana taɓa jin Inna Zulai da Inna Amarya nayi kasancewar ranar suna ƴan mutunci, ban san dai akan me suke hirar ba sai dai naji Inna Zulai na cewa, "ai tunda muka shiga naga jini na bin ƙafarta nasan wannan da wuya idan ba jini ne ya ɓalle mata ba". Innata acikin jimantawa tace,"ai ba ƙaramin wuya tasha ba awajen haihuwar nan". Na daddage na kurma wata uwar ƙara sannan na kwasa a guje na bar ɗakin Gwaggo na faɗa ɗakin Inna Amarya, ita kanta sai da ta firgita da yanda ta ganni, ta miƙe tana riƙo kafaɗuna tana jera min tambayar lafiya, cikin muryar kuka nace ma ta,"Haihuwa nayi". Adawiyya da ke zaune ta bushe da dariya tace,"ina jaririn?". "ai ina bacci na haife shi ban ganshi ba ma". Na bata amsa ina zubewa a ƙasa da ruzgar sabon kuka wiwi, hannuwana aka ina ci gaba da faɗin,"kuma wancan ranar Gwaggo tace idan na haihu banyi aure ba saita kasheni, sai ta saka min yaron a baki na cinye shi sannan zata yankani gunduwa gunduwa, na shiga ukuna wayyo Babana, wayyo Ya Kabiruna, wayyo, wayyo na shiga uku Ya Amaduna". Adawiyya na min dariyar ƙeta harda hawaye ta kuma cewa,"Shikenan Mairo zata mutu, to ke dama taya kika yi cikin?". Shashsheƙar kuka nake tamkar raina zai fice, na maida hankalina kanta ina jefa mata tambayar,"taya akeyi dama?". Maimakon ta bani amsa saita kuma fashewa da dariya harda kifawa ƙasa tana riƙe ciki. Sadiya wadda ke zaune kan dakalin ƙofa ta wurgo min tambayar,"yaushe kika shiga ɗakin mazan da ba ƴan gidanku ba?". Nayi saurin girgiza mata kai da hannu,"nifa yanzu ne kawai dana farka a bacci naga na haihu amma wallahi ban taɓa shiga ɗakin maza ba...". "ƙarya kike yi, jiya da daddare ba ina kallo kika shiga ɗakin su Ya Kabiru a salallaɓe ba bayan kuma basa nan sai abokansu". Na dire kan gwiwoyina nace,"to ai fa kawai cinnaka na ɗauka naje na sawa wannan Jawad ɗin da ya zagi Adawiyya a baki, kuma dana ga ya cije shi saina fito da gudu". Sai a yanzu Inna Amarya tasa baki, "ke dilla nutsar da hankalinki wuri ɗaya, babu wani haihuwa da kika yi". "Allah Inna haihuwa nayi, kallafa jini na zuba ajikina kuma har akan gadon Gwaggo ma dana kwanta, dan Allah kice karta kasheni, na shiga uku". Kuka nake wurjanjan kamar zan haɗiyi zuciya, dariyar Adawiyya ta fara ƙular dani na maƙuro wuyanta ina dukanta, "banza, muguwa, azzaluma, wawiya, doluwa, sokuwa, shashasha kawai, kuma saina faɗawa Gwaggo nace baki kaiwa Baaba Lami saƙon ba". Jin haka ta ƙwaci kanta da ƙyar ta shiga bani haƙuri akan na rufa mata asiri. Itama Sadiya ina jiyota tana cewa ai ni ce sokuwar ba Adawiyya ba, ban dai kulata ba saboda Ya Amadu yace na kuma yi mata rashin kunya sai ya zaneni. Inna Amarya wadda ta fita tun ɗazu ta dawo tana ce min na tashi na ɗaura zane akan kayana naje nayi wanka, bata barni na fita ba sai da ta natsar da hankalina wuri ɗaya. Na fito da kayan da na cire rungume ajikina ina kaffa kaffa kar wani ya gani, dan Inna tace duk wanda ya gani za'a yayatani a duniya ace na haihu babu aure, kuma idan Baba yaji da gatari zai faskarani tun kan Gwaggo ma ta yankani. Naja botikin ƙarfe na zuba kayan aciki, da dasu zan shiga bayin sai kuma na ajiye daga bakin ƙofa ta wajen lungun wurin ta yanda babu mai iya gani. Shaf-shaf nayi wankan na fito dan baki ɗaya hankalina yana kan wankin dana ajiye, so nake har na wankesu kar wani ya shigo gidan, sai dai da mamakina ko dana duba babu botiki babu alamunsa, na ko rikice na kama hailala da salati, to wane yazo ya ɗauka?, kar dai a mazan gidan wani ya shigo, ina ƴan dube-dube na hangi Kulu na shanya kayan ajikin garu ta bayan ɗakinsu Lukman, "kutttt". Na faɗa da ƙarfi cike da jin haushinta, da sassarfa na ƙarasa wurin da take, na kama ƙugu ina jijjige jijjige sai cika nake ina batsewa, ni nasan ban isa nayi mata komai ba amma tunanin makeken sharrin da zan ƙulla mata a wurin Gwaggo kawai na ke, ga mamakina sai gani nayi ta dubeni ta lafta min uwar harara tasa han
🏠