u". ta faɗa ba tare d ta nuna halin in kula a gareni ba, wanda hakan ke damuna sosai, kuma da dukkan alamu bata gane ina cutuwa da wannan shariyar tata ba, haka ko time ɗin da na zauna a abuja zaman da mu kai da ita tamkar wani zaman kishiyoyin da basa jituwa ko kuma zaman sirikan da, ƙwaƙwƙwarar magana bama yi da ita, sai dai na bita da ido, nayi tunani kala daban daban ko wani laifin na mata amma na gagara gano komai, kuma taƙi bani damar da zan zauna da ita naji laifina na bata haƙuri.
nasa hannu na mayar da hawayen da ke neman sakko min, kamin muryarta ta ƙara fito min da faɗin,"Daddynku na gaidaki, wai bai sameki a waya ba". tayi maganar idonta na kan wayar da ta ke shafawa. "mun yi lectures da yawa ne yau shi ne nasata a silent". bata ƙara cewa komai ba sai Ammi da ke cewa,"ina ga ki kira doctor ya duba Maryam, ban yarda da yanayinta na yau ba, kanta ma naji da zafi". nayi saurin ce da Ammi,"Ammi lafiya fa nake wallah, kawai stress ɗin yau ne". "eh duk da haka dai yazo ya ba ki wani maganin kisha...tashi kije kiyi wanka ki ɗan huta kamin ya ƙaraso".
Alhassan da ya ƙaraso wajen yana zama kusa da Mami ya ɗora hannunsa a bayan wuyana ya dafa ni ya kalleni yana cewa,"zama ki rabu da wannan son jikinne, kwana nawa ya rage". na turo baki gaba ina hararsa. sai yasa hannu ya ɗago fuskar Mami yana ce mata,"kalla yanda ƴarki ke hararata, to ki faɗa mata na rigata shaƙar iskar duniya, ta kiyayeni kafin taji ajikinta". Mami ta murmusa kuncinta ba tare da ta ce masa komai ba ta maida kanta kan wayar. Ammi tace da shi,"shegen son girma kaman gyaute...kai yanzuma aka ce ka daketa sai ka taɓata?". ina siririyar dariya nace,"rabu da shi Ammi, ai yanzu ko Bro Almustapha ba zai ɗaga hannu akaina ba, kasan kenan kuwa na girmi gaban dukanka". sai ya jijjiga kai bai ce komai ba, sannan ya sumbaci Mami a kumatunta ya miƙe tsaye yasa hannu a cikin aljihun wandon suite ɗin da ke jikinsa, ya dubi Ammi yana ce mata,"mijinki ne fa yace na kira masa ke, kiyi sauri sauri kije fita zamu yi". Ammi ta kai masa hannu ya kauce yana dariya. "kai ni wai yaushe ma zaka koma inda kafi wayo ne, na gaji da ganinka ina faɗa maka". yana nufar hanyar fita ya nuna ni da baki yace,"sai anyi bikin wannan ƴar zan koma, nima na gaji da ganinta saboda tana shigar min cikin al'amura".
ko da na shiga wanka na jima acikin bathtub cikin ruwan zafi kafin na fito, dan sai da na tabbatar ruwan zafin ya ratsa ilahirin jikina ta yanda gajiyar zata yi saurin sakata, ina tunawa da karatun test ɗin da nake da ita gobe.
na shirya cikin wata riga armless na zauna a dining ɗin da yake acikin ɗakin nawa na shiga zuba abinci. kuma fara cina kenan wayar Sweety ta shigo cikin tawa, na daɗa kallon sunan Ya Ahmad ɗin da ke yawo akan wayar fuskana ɗauke da tarin murmushi na jin daɗi, ban ɗaga ba sai da kiran yazo gab da yankewa tukunna.
ajiyar zuciyarsa na fara juyowa a kunnena kafin kiran sunana ya fito daga bakinsa. "me kyauna". laɓɓana suka tale da kyakykyawan murmushi na amsa da cewar,"na'am Yaya nah". murnushinsa mai sauti ya fito yana cewa,"me kyauna yau nayi kewanki da yawa, duk kinsa na shiga damuwa da rashin jinki". cikin sigar lallashi da ban haƙuri nace da shi,"sorry Yaya Nah, wallah yau munyi busy ne da yawa a school, baka kalla ba ma duk na gaji, jikina sai ciwo yake min". na faɗa ina shagwaɓe murya da fuska kaman ina gabansa ne. muryarsa ta fito cikin tausaya min da faɗin,"ayyah sannu Me Kyau nah, sannu kinji, ina ma ace munyi aure da na kawar maki da dukkan gajiyan da ke tare da ke...kinci abinci?". na kaɗa kai kaman yana ganina ba tare da na amsa da baki ba, kuma shi ma kaman yaga hakan sai yace,"to please ki samu kici abinci sai ki kwanta ki huta, kiyi bacci mai yawa please". nace da shi,"tom Swty". "albishirinki". nayi saurin amsawa da,"goro". "tomorrow by now insha'Allah ina tare da ke, zanzo na ganki me kyau nah, na gaji da rashinki a kusa da ni, wannan 2weeks ɗin da ya rage ji nake kamar shekara biyu ce nan gaba". na doka wani tsallen murna da jin daɗi ina faɗin,"Allah ya kaimu goben, Allah ya kawo min kai lafiya...Allah nima Yaya kewanka na ke sosai, wataran har sai naji kaman nayi kuka". duk da ba kallonsa nake ba a lokacin amma nasan ya kaɗa kai kafin yace,"a'a kar ki kuka plss, kinga hawayenki masu tsada ne, bana so ake zubar min da su anyhow, duk da cewan akaina ne za'ayi". na gyaɗa kai kawai, da haka muka ci gaba da hiranmu ta masoya, haka mu kai ta hiran ina cin abinci har naci da yawa ba tare da na sani ba, gaba ɗaya shauƙin sonsa daɗa tsarga min yake yi, Ya Ahmad ɗina bai yarda da na ƙoshi ba sai da muka yi vedio call ya kalleni sosai sannan yace na haska masa cikina tukunna ya gyaɗa kai yace na yarda, tun da ga cikin nan ya zama ƙato kaman nasa, saura bacci kuma, shi ma kar a tashi sai na tashi me kyau da kaina.
a cikin baccin da na kwashi mintuna ashirin ina yi na jiyo daddaɗan ƙamshin turaren Mamina ya karaɗe min cikin hanci da cikin kaina, na buɗe murfin idona a hankali ina du