NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 178 of 223

n sama, daga bakin Shamsiyya Sani, sanin cewar kiran nata bana arziƙi bane yasa ban tsaya sauraronta ba, naci gaba da tafiya abina, tafiyar da ka kalla yanda nake yinta zaka san nayi matuƙar gajiya. a hankali na ke saukowa daga steps ɗin bakin hall ɗin namu, hannuna na dama riƙe da matsakaiciyar jaka kasancewar yau ban lodo handouts ba. kamin na kai ga ƙarasa sauka daga step na ƙarshe na zare space glass ɗin da ke kewaye da rabin fuskata, sannan na zura hannun haguna cikin aljihun pink abayar da ke jikina wadda su Shamsiyya su kai ta santinta su na faɗin rigar ta dace da ƙirar jikina. a bakin hall na tsaya ina jiran fitowar Shamsiyya da Nusaiba amma shiru shiru ba su fito ba, naja ƙaramin tsoki na takaici sannan naci gaba da takuna cikin natsuwa har san da na taka kan titin cikin makaranta, yanda nake ta faman ɓata fuska zaka ce ko banda lafiya ne, haka ina ji wayata na ringing amma naƙi ɗagawa duk da na san mutumin da kiran nasa ke shigowa cikin wayar me muhimmanci ne a gare ni, kamar yanda na banbanta ringing ɗinsa da na saura. "Ya Ahmad". angona wanda za'a ɗaura min aure da shi nan da sati biyu masu zuwa. tafiyar da nayi akan titin gaba ɗayar bai fi taku 8 ba naja na tsaya, tsayawar tawa tai daidai da tsayawar motar da ta zo ɗaukana a gabana. a cikin yaren larabcin da a yanzu ya maye harshena nace da driver,"me yasa kayi late yau?". "kiyi haƙuri ranki ya daɗe, na kai Alhassan library ne, bai kammala da wuri ba ne shi yasa, kuma na yita kiran wayanki ba ki ɗaga ba". "yana ina?". na tambaye shi a sa'ilin da nake duban cikin motar ban ganshi ba. "yanzu zai ƙaraso ya tsaya da abokansa ne su na gaisawa, hangoki da yay ne yace na ƙaraso na ɗauke ki...ga ma shinan naga ya taho". ya ƙarashe zancen yana min nuni da direction ɗin da Alhassan ke tahowa wanda ke gab da iskomu. "menene? ba ki da lafiya? wani abun aka maki?". tambayoyin da Alhassan ke jera min kenan ya ƙaraso yana ɗora hannunsa saman goshina, yana mai tambayar cike da nuna damuwa da kulawa. na kwaɓe fuska ina karayar da kai nace,"na gaji ne". "to sannu". ya faɗa yana amsar jakar hannuna, sannan driver ya buɗe mana motar muka shiga, ko da shigarmu ban iya zama ba sai kwantawa da nayi na ɗora kaina saman cinyarsa. "Mami ta tafi?". na tambayeshi a amon muryata na fitowa a hankali. "har ta shirya sai kuma tace ta fasa wai ba yanzu ba". lokaci guda naji wani abu ya tsarga min a zuciyata, wani abu da ya haddasa jin daɗi a ƙasan ruhina. ko kaɗan bana son nesanta da ita, shi yasa ko da na taho karatu wata huɗun nan da nayi babu ita kusa da ni sai nake jina tamkar ina rayuwa ne a cikin kurkuku, irin kurkukun nan da ke da duhun ɗaki da kuma ganiyar azabtar da me laifi. driver ya tsayar da motar a rumfar wajen da aka tanada dan ajiye motoci, motocin da ake fita da Ammi kaɗai a cikinsu, sai ni da na zama ƴar gidan yanzu, ya fito yazo ya buɗe mana ƙofa, kamin na zuro siraran ƙafafuwana da suke ɗauke da gajiya waje, Alhassan ya kama hannun mu kai cikin gida. sanin cewar a irin wannan lokacin Ammi na tare da Abbi ne, yasa bamu biya ta parlon da ta ke zama ba. muka wuce kai tsaye zuwa ciki inda sauran ɗakunan ɓangarenta su ke wanda acikinsu ne aka fitar min da babban ɗaki guda aka bani tun zuwana karatu ƙasar, dan lokacin da Ummi tayi aure acan saudiya wurinta na koma da zama, sai ma lokacin da za'a saka ranar biki ne naje can abuja inda Mami take na zauna na tsawon sati biyu daga abuja kuma na wuto Qatar, ko su Yagana banjewa sallama ba a lokacin. "Subhanallah, me ya faru da ita?". muka jiyo muryar Ammi da bamu tsammaci gani ba tana tambayar, na kalleta da gajiyayyun idanuwana ina ƙara kwaɓe fuska nace,"Ammi yau na gaji ne". sai ta miƙa jakar da ke hannunta wa Kuyangar da ke bayanta, sannan tayi saurin tahowa gareni ta riƙoni zuwa jikinta. Alhassan kuma ya wuce ɗakina kai min jakata, akan cushion ɗin parlon muka zauna Ammi ta shiga warware min vail ɗin da ke kewaye da fuskata tana yi min sannu. ta kwantar da kaina bisa kafaɗarta tana jera min wata sannun, sannun da bata da adadi tun daga lokacin da ta riƙoni. cushion ɗin da muke zaune na fuskantar steps ɗin da su ke cikin parlon, ta nan na jiyo takun tafiyar takalmi ƙwaf-ƙwaf na sakkowa daga upstairs ɗin, kamin wucewar sakanni biyu kuma naga ɓulluwar Mamina, tana sanye ne da butter milk ɗin abaya wadda tasha stones a jikinta, ta kuma matuƙar amsar kyawun nata, ta ƙarasa saukowa tana sauya hannu na riƙe wayar da ke kare a kunnenta zuwa ɗayan hannun da ke riƙe da ƴar ƙaramar jakarta haka ta ƙaraso wajen cushion, ta cikin wayar da ke kare a kunnen nata ta ke faɗin. "a'a i just want to stay more for a while". tayi shiru kamin ta ƙara magana,"oak hakan ma Yayi Your Excellency. muyi waya letter". daga haka ta katse wayan a yayinda ta ke zama acikin ɗaya daga cushions din. "sannu da hutawa Ammi". "yauwa". lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawayen da basu kai ga sakkowa ba, muryana na rawa nace da ita,"Mami sannu da gida". "yauwa sann
🏠