onmu yay kanta hankalin kowa a tashe, abin da ba'a taɓa ganin tayi ba, Baba yace,"Subhanallah Yagana me ya faru?". bata bar kukan ba tace,"Adamu gidana zan koma tunda Allah bai sa an siyar da shi ba, zanfi samun salama idan na koma can". Baba ya ƙara cewa,"Yagana akan me? ko wani abu ya faru a gidan nanne?". ta zuƙi hanci ta fyato majina tana faɗin,"to mene ma bai riga ya faru ba Adamu, kawai ni dai gwara aiwa tufkar hanci tun jinina bai hau ba, ga kayana canma na gama haɗawa tafiya kawai zanyi dama jiran isowarka nake yi, kar na bar gidan ban sanar maka ba kaga rashin kirkina". wannan karan ba Baba ne kaɗai yay magana ba, kowa sai da ya jefa ma ta tambayar,"wai Yagana me ya faru ne?". ni kaɗai da banyi tambayar ba kallon Yagana nake da bugawar ƙirji, me yasa ta kuka? kuma me yasa ta ke maganar zata bar gidan?, nayi tsilli-tsilli da idanu ina kallonta da jiran amsar da zata bayar.
kukanta ya ƙaru a san da take cewa,"ni dai ba muguwa bace, kuma ba ƴar baƙin ciki ba ce. amma ban san me yasa ake min bahagon kallo ba, wallahi ni dai ko ƴaƴan kishiya ba zan iya cutarwa ba balle jikokin da nasan daga tsatsona suke...Adamu a rayuwa me nayiwa ƴaƴanka da za su dasawa zuciyata baƙin cikin da zai kashe ni, idan wani abun nayi musu tsakani da Allah ai sai su fito fili su faɗa min na basu haƙuri tun da ni ba baƙuwar zafi ba ce. amma haka kawai sai su ɗau karan tsana su ɗora min, su ɗauki gaba da ni, ɗabi'ar da ubangiji ba ya so". tayi shiru tana murza idanu, kowa ya sauke numfashi. Baba ya shiga kallonmu kamin ya kira sunan kowa, sannan ya kalli Inna ma yace,"Zulai meke faruwa a cikin gidan nan da ban sa ni ba?, domin nasan indai fitina zata fito daga ɓangarenki ne, me Ƴaƴanki su kaiwa Mahaifiyata da baku ɗauketa a bakin komai ba". yay maganar cikin faɗa da ɓacin rai...Yagana tayi saurin cewa,"a'a kar ka ɗauki hakkinta babu ruwanta babu ruwan ƴaƴanta acikin wannan lamarin...nifa ina maka magana ne akan Kabiru da Mairo". Baba ya juyo yay min wani kallo da yasa na ƙara tsurewa dan ban san wani laifi da nayiwa Yagana ba.
kuma maganar Yaganan ta katse shi daga abin da yake son cewa, a wannan karan kuka ta ke sosai wanda yafi na ɗazu. "kaga Adamu yaron nan Kabiru tun da uwarsa ta mutu ya ɗaukeni tamkar uwa, ba ya ɓoye min komai, halinsa me kyau, nima na ɗauke shi tamkar ɗa ba jika ba, tun da Allah ya sani kaf cikin jikokina nafi ƙaunarsa ba zan ɓoye ba...amma yanzu kashi ma ya fini mutunci a idon Kabiru, gaba ɗaya ya ɗauke min wuta ba ya kula ni, wannan shegiya abar banza gaisuwa Kabiru in zamu doki ƙirji da shi ba zai min ba, kai na taƙaice maka ma ɓangarena ya daina zuwansa...to ni duk ba wannan ya dameni ba, damuwar da nake gani a fuskarsa ita ke ci min tuwo a ƙwarya, juyin duniya nayi da shi ya faɗa min matsalar yaƙi, ƙarshe ɗazu da safe da na tsare shi da tsaki ya bini kafin ya tashi ya fita fuuuu kamar guguwa, to wannan halin kyautawa ne fisabilillah, ni ya riƙe maganarsa amma ka faɗa masa bana son ganinsa a damuwa wallahi". Baba yay ƙasa da murya yace,"kiyi haƙuri Yagana, zan tuntuɓe shi naji meke faruwa". tana shashsheƙa tace,"da ka taimaka min, dan ni dai da wannan halin miskilanci da Amadu ya sauka akai shi kuma ya hau gwara kullum yazo ya dinga faffaleni da mari ko kuma yace na mutu kawai ya daina ganina, hakan zai fiye min da dai naci gaba da ganinsa da damuwa". Baba ya ƙara bata haƙuri tace babu komai, ya kalli Lukman yace ya kira masa Kabiru, sannan yace da Yagana,"ita kuma Maryam me tayi". ta goge fuska tace,"wannan abar ta kusa da kai ai fitina ce Adamu, shi yasa nace barin gidan nan zanyi tun bata ja ubanta yasa an yi min ɗaurin rai da rai ba, ko kuma tasa uwarta ta maidani baiwar masarauta". nayi kicin-kicin da fuska nace,"Yagana nifa babu abin da nasan nayi miki". tace da Baba,"kaga ni baa, duba fa a irin yanda ta ke min magana kamar zata dukeni, kasan kuwa ba ƙaramin haƙurin zama na ke da ita ba. aini tun da ƴar nan ta balaga nasan zan fuskanci babban ƙalubale, to inda Allah ya taimaka ina kai lamarinta wurin Allah amma banda haka tuni tasa an ɗaureni". Baba ya kalleni fuskarsa a ɗaure yace,"me kika ma ta?". "yo ka tambayeta salon ta ƙaryata zancena Adamu, kaima kasan ba zata faɗi gaskiya ba sai dai tayi ƙarya ta kare kanta". Baba yace,"ki barni da ita". nace,"Allah Baba ni dai nasan ban mata komai ba, kawai so ta ke taja min faɗa a wurinka". sabon kukan da ta fashe da shi ya tari numfashina. "Adamu na faɗa maka yarinyar nan fitina ce, idan kaci gaba da tambayarta zata ƙaryata ni ba tare da duban shekaruna ba. abinda ya faru ɗazu fa daga ƴar ƙaramar magana nace ba zata bi waɗancan marasa kunyar unguwa ba shikenan sai ta ɗaura gaba dani, ta shiga ɗaki ta haɗa kayanta wai barin ƙasar za tayi. na tsuguna na bata haƙuri amma duk bata ga wannan ba haka taƙi saukowa. abincin rana ma da na bita da shi ɗaki ƙinci tayi tasa ƙafa tai fatali da kwanon". ta dubi Nawwara tace,"ko ba haka akai ba ke?". Nawwara dai tayi shiru ita kuma