NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 175 of 223

wa nawa. ina ganin ya fara ɓallo tablet ɗin na miƙe tsaye zan bar wajen ya ɗago da kansa, idonsa akaina muryarsa na shaida izinin na koma na zauna. kamar nayi masa gardama saibna tuna a gaban wanda nake, da ƙyar da siɗin goshi nasha maganin, dan sai da ya cire tausayina, ya daina lallamina ya shiga zazzaga min wannan faɗan nasa da babu wanda ke ƙaunarsa. "kin san Allah kika dawo da maganin nan sai na ɗauke fuskarki da mari". na kalle shi da idanuna da suka cika da ruwan hawaye amma ba su zubo ba, naga da gasken yake maganarsa, na sauke hannuna daga toshe bakin da nayi, ta dole na tsaida aman da ke neman taso min. cikin fishi na miƙe zan bar wajen muryasa a ɗage yace da ni,"koma ki zauna". ina zama ya haɗa ni da jan dogon tsaki fuskarsa na ƙara haɗo ɓacin rai ta bayyanar. Sadiya da Adawiyya da Jamila su ka shigo da sallama, su ka gaidasu Yaya sannan su ka gaida Yagana, kamin mu gaisa da su suyi min sannu da jiki. ina dubansu da muryata da har yanzu bata saki ba nace,"ina za ku je?". Adawiyya tace,"ɗinku nan Sadiya zamu kai". da yake an kusa bikinta saura sati huɗu gaba ɗaya. na miƙe tsaye ina faɗin,"dan Allah ku tsayani mu tafi tare". "lallaima ke ɗin nan, ke da ba ki da lafiya". nace,"naji sauƙi ai...ba ku taɓa zuwa dani ko'ina ba fa tun da aka fara shirin bikin nan, kuma ina ta son zuwa, sai dai naji Inna tace kun fita". Jamila tace,"to ba Yagana ce ke ƙunsheki a ɗaki ba ta hanaki fitowa wajenmu, kinga kam ai bama yi tunanin kina son zuwa ba". karaf maganartata a kunnen Yagana da ke fitowa daga ɗakinta. "ba dan ance ba kyau idan mutum ya tuba daga wani saɓo da yake tafkawa ba a dinga taso da abubuwan da ya aikata a baya, Jamila ai da na yaɓa miki magana akan Uwarki...kuma kije dan kanki idan sharri abinyi ne kar ki fasa". ta zauna akan kujera tana ci gaba da faɗin,"dama na jima da faɗa miki wannan zaman keɓa kan da kike sai ya jawo min magana, ace ina rabaki da su saboda naga yanzu ke ƴar gata ce...gashi nan yanzu ina zaman zamana kinja min zagi da sanyin safiyar nan". Jamila tace,"Allah ba ki haƙuri Yagana ni ban faɗa da wata manufa ba". ta taɓe baki bata ce ma ta komai ba, ta maida hankalinta gun Ya Kabir tana faɗin,"Ɗan Hajara ai na muka kwana da kai?". "Yagana na shirya na bisu ɗin?". bata dubi inda nake ba tace,"wallahi ba zaki je ba...na gama magana Maryam". tana faɗin hakan nayi ɗakina a zuciye, ina shiga kuma na shiga tattara kayana ina zubawa a trolly, ko ina za ni da su oho. da yamma ina kwance akan gadona cikin nurƙufanci Inna ta shigo ɗakin, dama tun da safen nan da na shigo na gama haɗa kayana ban kuma fita ba, abincin rana ma da Yagana tazo tai maganar duniya nai ma ta shiru naƙi kulata, har taji haushi tace in dai sunanta Rakiya ba zata ƙara min magana bare na wulaƙantata. "Maryam jikin ne?". Inna ta faɗa tana zama gefen gadon tana taɓa jikina. zafin da taji yasa ta ɗauke hannu tana faɗin,"subhanallah, kin ko sha maganinki ɗazu?". kai kawai na ɗaga ma ta. ta sake cewa,"Allah ya baki lafiya, tashi muje ga Mu'azzam can yazo zai miki alluranki". "Inna dan Allah bana son wannan allurar". ta ɗagani daga kwancen tana faɗin,"nasan baki son allura amma ya za ki, dole ce tasa...daure ki tashi kinji ƴar albarka, ina aka taɓa zama da ciwo a jiki ba tare da an magance shi ba, abin da ma Mu'azzam ba shi da zafin hannu". Yagana ta shigo ɗakin ita ma. "ke ki fito ai miki allurarki dan yau ban shirya hana idona yin bacci ba". muryata kaman zanyi kuka na ɗan doki ƙafata a ƙasa nace,"nifa Yagana yau a ɗakina zan kwana Allah ba zan hanaki bacci ba". ta ɓalla min harara sannan tace,"kin san Allah ba ki isa ba allurar nan sai anyita, jiya ni ɗaya nasan me naji a zaman jinyarki...kema Zulai kin wani zauna kin zuba ma ta ido tana abin da taga dama, ta bakin Amadu ki figo hannunta kawai". na ƙara ɓata rai ina cewa,"to ni dai Yagana ki rabu dani mana tun da ciwon a jikina yake". ina faɗin hakan tasa kai ta fita daga ɗakin tana jijjiga kai. a parlon Yagana, Baba ne da Manyan Ƴaƴansa zaune, cikinsu Ya Kabir ne kawai babu. kuma ganinsu baisa na daina kukan karɓar allurar ba. Mu'azzam ya ɓare syringe ɗin yana zuƙar ruwan alluran, na tafi wurin Baba na ƙanƙame shi ina kukan ni ba za'a min ba, shi kuma Baba nata bani haƙuri. "ashe ka shigo?". Yagana tace da Baba tana zama a kan kujera. "Ehh Yagana...ina yini". ta amsa masa,"lafiya lau, ya ka baro su Alhaji Ƙaramin?". "su na lafiya duk sunce agaisheku...ashe bikin ƴar gidan Baffayo ma sati guda ne da na Sadiya". tace,"haka Nafisatu ke faɗa min ranar da su ka zo ganin gida, to mu dai baza muje ba sai dai suzo nan a haɗe ayi tare, in ba haka ba kuma maje musu murna daga baya". Baba ya kaɗa kai da rigimar da Yagana ke neman ja sannan yace,"jikarki dai har yanzu taƙi girma". ya faɗa yana zolayata da na ƙanƙame hannayensa, kuma sai na sadda kai a gefen hannunsa ina jin kunya. Kamar jira dama ta ke yay magana akaina sai ta gyara zama ta fashe da kuka tana dafe goshi. gaba ɗaya id
🏠