NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 174 of 223

Maryam yana kallon Kabir yace,"mantawa da Yagana kayi ko shi yasa ka kasa nemana a ɓangarenta?". Kabir yace,"kar ta jika kaja min magana fa". Kabir ya faɗa yana shafa wayarsa, shi kuma Ahmad ya ɗan dara yace. "to ya akai?, ai na shiga wajenka baka nan time ɗin...nace kura tayi lafiya kenan". "ka bari kawai, exams enn ce tasa na wartsake ba shiri". bai san me yasa ba, amma a duk wani furuci na Ahmad wani haushinsa ne yake tsarga masa, abin da bai taɓa ji ba dangane da ɗan'uwansa, kai wani ma daban ba shi ba. ga shi yaƙi yardarwa kansa da hakan a matsayin kishi ne, gani yake tun da har yaywa kansa alƙawarin cire yarinyar daga ransa to babu wani abu da zai dame shi game da ita, zai ci gaba da kallonta ne matsayi ɗaya da su Adawiyya, kuma matar ƙanensa. "idan ka tafi motarka fa?". ba tare da Kabir ya dube shi ba yace,"kai zan barwa ai, kaga ka rage yawan huzzeling da ita". "amma kuma da ka barta ba'a kawo ba, sai ka dawo nan ɗin kawai". "idan baka manta wane ni ba, ba zaka mance da rashin sauya ra'ayina da na tsara ba tun farko". "to godiya na ke, Allah ya ƙara buɗi...kaga sai na ƙara tarin kuɗina yanda nima zan mallaki babbar kai irin taka". da kai kawai Kabir ya ba shi amsa, domin ya kai gejin da ba zai iya ƙara tanka masa ba. lokacin Ya Ahmad ya maido da hankalinsa kaina, kaina a sunkuye yake ina zane da yatsana guda ɗaya akan dining table. nayi tagumi da ɗayan hannuna, fuskata na haskawa da damuwar da ke ƙasan raina, ayau kaɗai wani mugun haushin Ya Kabir na ke ji, haushin da inda ace na kai matsayin da zan saka masa duka babu abin da zai hana ni. tun a daren jiya da na dawo hayyacina naga kowa akaina yana min sannu shi ban gansa ba, shikennan na fara jin haushinsa matuƙa, amma kuma a yau da na farka da sanyin safiya naji wai ya tafi kai Nawwara school sai haushinsa ya ninku a raina, wai mutumin da bai da cikakkiyar lafiyar ƙafa shi ne har da su driving, driving ɗinma ba nan kusa ba can da uban nisa. in ace Nawwara ɗiyar wani ƙusan ce sai na kira kulawar da naga yana ta rawar ƙafar bata a matsayin neman gindin zama, to ita ba kowan kowa bace, duk da na san shi ɗin me tausayi ne da son kyautatawa wanda ba shi da shi, ba a yanzu da yay kuɗi ba, tun lokacin ma da ba ya samu a ko da yaushe. ni ban damu da sannunsa ba, tun da ko yayi min ko bai ba zan warke abuna in sami lafiya, to amma na damu da janye min da yay, wannan kulawar tasa gare ni, wannan soyayyar da yake min, wannan fara'ar tasa akaina duk ya ɗauke min kai da su, tsakani da Allah sai da ya saba min da hakan kuma sannan zai janye min a lokacin da nake jin kamar nafi buƙatarsa fiye da lokacin baya. ta shiga ƙifta idanu kamar zata fashe da kuka, sanyin hannun Ya Ahmad da naji a saman goshina yasa na ɗago na dube shi da raunannun idanuna. "kin daina jin zafin ƙirjin?". nayi masa knodding kaina kawai ba tare da nayi magana ba. "to asha maganin?". na ɗaga masa kai still ina kallon ƙwayar idonsa da ke nuna tsantsar damuwa da ciwon nawa da kuma nuna kulawa. sai na kwaɓe fuska ina tura baki gaba na girgiza masa kai alaman bana so. murmushi yay cikin murya mai taushi yace,"kiyi haƙuri kisha magani kinji, kinga ba ki da lafiya, kuma rashin lafiyanki ba ya barin kowa ya sami natsuwar zuciya da ta ruhi...ko ba ki son hankalin Mami ya kwanta ne?". tambayar ƙarshe tasa na kaɗa masa alaman a'a, sai ya ɗora tafin hannunsa ƙasan haɓata da faɗin,"to kiyi haƙuri kisha kinji ƴar lelen Mami da Ummi". a karon farko tun tashina daga barci nayi murmushi, na ci gaba da kallon gefen fuskarsa da a yanzu ya karkata yanawa Basma magana. lallai sanadin cuta kana cin wani arziƙin, banda ciwon nan ya ɗaga hankalin kowa ina zan sami wannan tarairayar a wurin boss ɗin gidanmu, Ya Ahmad ɗin da ko kasha magani ko karbka sha ko a kwalar rigarsa, bana mantawa da idan naƙi shan magani bulala yake sawa ya zaule min jiki, shi yasa idan ina gardama kan magani da Gwaggo tace ku kira min Amadu babu shiri nake sha. kuma kawai sai naji wani abu mai sanyi ya tsarga ta jikina da ban san menene shi ba, naci gaba da kallon laɓɓansa dabke motsawa suvna magana da Basma, duk da cewan laɓɓansa ba su kai na Ya Kabir kyau da burgewa ba amma shivma kyan nasa nada iya gwargwadonsa, ko da yake kyan Innah yayi, Inna Zulai tana da kyau sosai kawai dai dan batayi kyan hali bane, dan yanzu kam Alhamdulillah Innah ta sauya hali ƙwarai dalilin isharar da ta gani, kuma ba komai ya firgitata ba irin yanda rayuwar Inna Amarya ta koma, haka zalika da yanda taga ubangiji ya maida ni, abunda ta faɗa da bakinta cewar bata taɓa zaton zan iya taka wani matsayi ba, asheɓma ni ɗin na wuce gaban tunanin kowa. "Ya Ahmad gashi". Basma tace da shi san da ta miƙo masa ledar magungunan da ya sa ta ɗauko a ɗaki. "bamu ruwa mara sanyi". yace da ita yana aje ledan ya fito da tarukan magungunan ciki har da inhaler, gabana ya faɗi, wato a rayuwa kowa da kalar jarabawarsa, kamar ni daga wannan sai wannan, wai yau ni ce da cutar asthma, cutar da ta ɗaure kaina da ko
🏠